Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 80

Chapter 80

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai ta je, ta gaji da 'yadda ya maidata bagidajiya marar yanci, kansa ya sara yana jin ba'kin cikin ta na neman kassara shi. Haka har kwanaki uku suna zaman doya da manja, Rannan cikin dare ta ji hannunsa na lalubarta, ta zabura kuwa ta bige hannun, tare da fadin "Bana so". Bai saurare ta ba ya damko ta, ya fara kokarin gwada mata 'karfi saboda ya gaji da rarrashinta. Ganin da gaske zai cimmata alhalin ta riga ta kudiri aniyar ba za ta saurare shi ba. Dan haka ta fashe da kuka ta ce " raping dina za ka yi? na fahimci bani da mutunci a gurinka indai ba bu'katarka ce ta ciyoka ba, na daina ganin aibun 'yantattatun mata wadda suka juyawa aure baya, saboda sun san ba komai a cikinsa sai ba'kin ciki da takura da kuma 'bacin rai". Jikin Mk ya mutu yana rike da ita, da ta lura, tashin hankalin da ke zane baro baro a fuskarsa ba zai bari ya ci gaba da rarrashinta a YAU kamar yadda ya Saba ba. "Matan da suke zaman kansu, duk abin da suke so, aguje suke samu, amma matan aure sune agaba wurin samun hawan jini saboda tsabar bakin cikin da mazajensu suke 'kulla musu". 'Kololuwar tashin hankali Mk ya shiga, ji yayi jiri ya kwashe shi dan ma a zaune yake, ya tafi luu ya buge 'keyarsa da fuskar gado. Da kyar ya dauki hannunsa ya ri'ke kansa da yake tsananin sarawa, da karfi ya dinga ambaton" innalillahi wa Inna ilaihir raji'un". Ya dade yana nanata kalmar, har ya dan sami nutsuwa kadan, ya mike ya saka rigarsa da wando, ya ware murya sosai ya ce "Ni ki ka fadawa wannan maganar? Ashe kuwa har yau baki gane ni ba, zan nuna miki ba a bariki muke ba, ba kuma auren bariki na ke yi ba, ki ri'ke dukkan abin da ki ke tun'kaho da shi bana so, ki ji'ka ki shanye abin ki, amma ki sani yau da Gobe zasu biyar da ke indai kina sha'kar numfashi". A daren ya dauke dukkan abin da yake nasa ne a cikin dakin Sa'adah, sai Agogon hannunsa da yake cikin wadirof dinta ya manta bai dauka ba. har ya kwanta ya tuna bai dauko tawul dinsa ba, ya koma ya dauko, kafin ya fita ya tsaya ya kalleta tana zaune duk jikinta ya saki da alamun ba tasan girman munin maganar data furta ba, sai bayan ta fada. A kausashe ya ce "Na tsane ki, na tsani na bude ido na ganki, ba dai kin fi sha'awar rayuwar 'kazanta akan ta sunnar Ma'aiki ba? kin raina duk kokari na, kin raina ni'imar da kike ciki, Na rantse miki! ba dan kunyar Baffa ba, da a yau na mayar da ke 'yantacciyar macen da kike fata, ni kaina NADAMAR auren ki na ke yi, amma na gode Allah da nake ganin sakamakon son zuciyata a duniyar nan, ba sai naje lahiraa ba,'kiri 'kiri na nunawa mai sona da gaskiya HALIN YAU, na butulci". Ya juya ya fita ya barta cikin rashin sukuni mai yawa. Tun daga ranar ya bala'in dauke mata wuta, idan ya fita tun safe, sai dare ya fara turawa zai dawo, sannan matu'kar yana gida to kuwa kofar dakinsa a gar'kame ta ke hatta Jawad ba kasafai yake ganinsa ba, kullum cikin tambayar Sa'adah Ina Malam ya tafi?". Wannan ne karon farko da ya yi fishi ba waiwaye, hatta fuskarta baya son gani a yanzu, sabanin da da ganinta shine cikon farin cikinsa, har yau fama yake da ciwon da bakaken maganganun suka sababa masa a zuciya yake yi. Ana haka mijin Sumayyah ya yo waya akan bata da lafiya sosai, haihuwa ne ta zo mata da tangar'da anmata C's an fito da yaro amma kuma bata da lafiya. A ranar Baffa ya sanar da Mk, akan gobe za su yi asubanci zuwa Gombe shi da Inna, idan ba damuwa ko zasu tafi da Iyah ta gano jikin yar'uwarta. Bai yi nauyin baki ko kunya ba, ya ce "Zan zo na kai ku Baffah amma ita daga baya zata je". Godiya sosai Baffa ya masa tare da fadin "ko bata je bama ai kai kaje , ka wakilceta". Haka akayi tafiyar Sa'adah ko labari bata ji ba, a ranar Baffa suka juyo da Mk, da kuma Hajiyar Bichi da ke ta bisu, suka bar Inna dan ta kula da Sumayya, kafin Umma fanshekara ta je sai Innan ta dawo. Ganin da innah ta yi har washagari Iyah bata 'kira ta yi jajen mai jiki ba, sai hankalin Inna ya tashi tana tunanin ko itama ba ta da lafiya ne? Tana Shirin 'kiranta, sai ta 'kira suka gaisa, mamaki ya sake kama Inna ganin ba alamun ta samu labarin halin da 'yar'uwarta take ciki, dan haka sai tace "mijinki bai fada miki Ina Gombe ba?" "Wallahi bai fada mini ba, wani abin ne ya faru?" ta tambaya a kidime. A sanyaye Inna ta ce "yayar taki aka yiwa tiyata ga yaro nan lafiya lau, sai itace bata Jin dadi, amma dai da sauki". Cikin muryar kuka ta ce" shine ba ki fada mini ba Inna?". "Mijinki ne fa ya kawo mu, jiyan suka juyo da Baffanku, Kinga ai bana yi zaton ba ki ji ba, duk yadda akayi ba zaman lafiya kuke yi ba Iyah, tunda da bakinsa yace baza ki zo ba, sai muka dauka ko kema ba Kya jin dadi ne ya rufe mana, har da Hajiyar Bichi muka zo, duk jiyan suka juyo". Kuka kawai Sa'adah ta ke yi, irin kuka na rashin madafa, sosai kukan ya ta'ba Inna, tashin hankalin ta ya 'karu ga na Sumayya da ta ke kwance bata san wadda ke kanta ba, ga na Iyah da ba tasan ha'ki'ka in matsalar ta ba. A sukwane ta kira Baffa tace lalle akwai matsala tsakanin Iyah da Mijinta, cikin rashin daukan maganar da muhimmanci ya ce "Mijin ta bai kawo 'kararta ba, ita ba ta ce ga laifinsa ba, sai kawai naje na hau bincinkarsu, tunda sun iya 'boye sirrinsu, sai a bisu da addu'ar Allah ya daidaita su". "Ka shiga maganar nan, da alamun fa abin babba ne, hatta zuwan nan da ya yi Gombe bata sani ba, kar a zuba musu ido fa". "To" ya ce mata a gajarce ya katse wayarsa! yana cewa lamarin mata yana da ban mamaki, kawai dan kina so a tursashi ya barta taje inda baya so taje sai kice naje na shiga tsakanin su, duk tsawon lokacin da suke tare waya ya san yadda suke zaune? Haka kwanaki suka yi ta shudewa a cikin Wannan hali tsakanin Mk da Sa'adah, kullum 'kara nesanta kansa yake da ita, zuwa yanzu da suka cika sati biyu cikin wannan halin, wadda ko a mafarki bata yi zaton zai iya shareta har haka ba, domin tun ranar da ta yi wannan katobarar bai sake bin takanta ba, asalima ta lura bai son ganinta ne har zuciyar sa, tana ganin idan ya dawo a gaggauce yake shigewa dakinsa ya rufe kofa, hakanan idan zai fita a hanzarce ya ke ficewa, duk yadda bai son ya ji kukan Jawad amma a yanzu duk kukan da zai masa ba ya

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});