Chapter 138
Chapter 138
matu'kar kamata, ta tabbatar tana da matsuguni a zuciyar mijinta. duk dai abin da Sa'adah ta yi mata a asibiti, yasa ta gane har gobe tana da karfi a zuciyarsa. Yini guda bai fita ko ina ba, da aka yi azahar ya ci abinci, ya sha magani barci ya yi sosai. Dan haka bai fita ba, sai a washagari, ya fita zuwa gidan Hajiya, fa'da da Jan kunnen da ta yi masa akan ya ri'ke Sa'a da girma ba ka'dan bane. Fa'di take "ubanta mutum ne har da rabi, ka ji tsoron ubangiji ka ri'ke ta da Amana, na sha fa'da maka ba hankalin ku daya ba". Ya amsa da zai kiyaye. Daganan ya leka shagonsa, ya kuma gaida Baffah. Baffah ya ce "wannan karon ma sadaki kawai zaka bata" Da sauri ya ce "A a Baffah bar ni kawai na yi mata komai, gatan zai mini yawa, yanzu Ina da halin yin dukkan abin da ake yi, na gode sosai da karamci, Ina fatan kar Allah ya sa na sake kunyata ka Baffah". "A a ni ba ka kunyata ni, bare ka nemi tsari da sake maimaitawa, ba komai tsakanin mu sai karramawa, domin tunda kaki fa'dar abin da ya hadaku, kuma kowa ya gane itace mai laifin, sai na gane kai din jarumine, adaline, mai kuma kaunata ne, Koda ha'kurin ka ya kwace amma ai hankalinka bai kwace ba, domin baka tozarta mini Iyah ta hanyar fa'din aibunta ba, dan haka Ni baka mini komai ba, sai alheri." Ya zarce da cewa "a farko da zan baka ita, sai da na jaddada maka kar ka bari ta kangare maka, duk kuma wadda ka ga tana mu'amala da su, hankalinka bai kwanta da su ba, ka shata musu layi, Ina jin dai baka dauki wannan shawarar ba shiyasa kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki, ba fa zan rufe ka ba, kaima kana bari soyayyarta na rinjayar ka a gurare da dama, a farkon rikicin banyi magana bane saboda yadda ka boye komai ka sata itama ta rufe komai" Mk da ya san Baffah gaskiya ya fa'da sai ya sunkuyar da kansa kasa, ya kasa cewa komai. Tsawon lokaci kafin Baffa ya sake cewa "Na horeka da yin adalci a gidanka, ka yi iyakacin bakin kokarinka, ka yi adalci, sai kuma ka barwa Allah ya taya ka. Domin a yanzu ma ina sake fa'da maka duk abin da bai maka a tare da Iyah ba, tun kafin ku yi nisa ka taka burgi akansa, su mata da ka gansu idan ba a kula da tarbiyar su ba, nan da nan zasu halaka kansu su halaka mazansu". Jikin Mk ya yi sanyi, domin kuwa a kullum dabi'un Baffah na fahimtar da shi bai gama saninsa ba, har yau din nan bai ci karo da mutumin da ya fi mahaifin Sa'a karamci da fadar gaskiya ba, ko da kuwa gaskiyar akan kansa ne. Mk da ya rasa mai zai ce sai kawai ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Madallah da zuciya irin taka, dama ka sha fa'da mini ba Sa'a ce ta hada mu ba, ba kuma zata zama dalilin rabuwarmu ba, tabbas na gasgata hakan". Mk ya zarce da fa'din " Alherinka yawa ne da shi Baffah! A duk lokacin da nake gabanka sai nake jina tamkar ina cikin shekaru irin na Jawad. Saboda zuciyata tana samun nutsuwa, domin tana tare da wadda yake girmamata, yake ganin kimarta. Kai ka'dai ne baka ga laifina akan kaddarar rabuwarmu ba, Kai ka'dai ne ka yi mini shaidar fin 'karfina al'amarin ya yi, haka kai ka'dai ne a duk tsayin wannan tafiyar bai juya mini baya. Haka nan yanzu kowa jan kunne yake mini akan na rike Sa'adah komai zata mini na yi hakuri, kar na ce komai. Kai ka'dai ka ce na yiwa 'daya matar tawa adalci, kai ka'dai ne ka ce kar na yi hakuri da Sa'adah a inda zata kuskure ko ta sab'awa ka'ida. A yau na sake ganewa kai din ba uban Sa'adah bane nawa ne" Ya yi shiru saboda yadda yake jin rauni na shigar sa, ko mutane nawa ne irin Baffaha a Yau? Ya tuna kwanakin baya yadda ya zaunar da shi yana fa'da masa tsananin son da yake yiwa Iyah! Amma a yau ya ture wannan soyayyar ya fa'di gaskiya, ayiwa Farida adalci, kar kuma ya bawa Sa'a damar da zata halaka, ta halaka shi. Ya dago idansa da suka ka'da ya ce "Baffah kwanakin baya ka ce mini baka ta'ba mallakar abin da kake so kamar Iyah ba". "Eh" Baffah ya amsa a taikace . Mk ya ce "Nima yau zan fa'da maka ban ta'ba son wata mace a duniya kamarta ba. Zan yi iyakacin kokarina na dauki shawararka na kar na bari ta halaka mu, Amma fa'da mini maganin rikicinta Baffah! Ita din sarka ce mai rikicin gan-gan". Dariya ya yi ya ce "ai ba zata daina ba, Amma ina tabbatar maka zata rage da yawa daga cikin rikicin nata mussaman na dogon buri da kawaye yan karya domin ka shayar da ita mamaki. Abin da na san ba zata daina ba, shagwaba, saurin kuka, da kishi. Wannan kuma kaine zaka kiyaye motsuwar kishin, shagwaba da kuka kuwa idan ta yi ai sai ka rarrashi abarka". Kunya ta kama Mk ya kasa cewa komai Sosai ya yi godiya sannan ya mike yana cewa "Makaranta zan tafi". Da sigar tsokana Baffa ya ce "Ba zaka leka ku yi tozali ba?" Kunya ya ta sake kama Mk ya ce "Ai mun yi fa'da Baffah, ba zan nemeta ba, sai ta neme Ni". Dariya sosai ya yi tare da cewa "Anya kuwa ka yi gaskiya Mutari? Amma dai ba ruwana". Ko wayar Sa'adah bai nema ba, bare ya je gidan wurinta, ya wuce makaaranta. Sa'adah ganin kwanaki biyu da sallamo Mk amma bai nemeta ba, ya sake hauhawar fishinta, yayin da shima fishin yake yi da ita mai tsanani, kawai ya samu salama ne na tabbacin zata dawo hannunsa, amma ganinta da ya yi da Khalil ba 'karamin haushin ta ya ji ba, kullum da aikinta yake kwana, yake tashi tunda shine sanadin da yasa take mua'amala da ahalin Khalil. Kwanaki uku ya rage daurin aurensu amma babu fahimta a tsakanin su lamarin da yake ciwa Sa'a tuwo a kwarya, wani sashi na zuciyarta ya ce saboda yana da wata matar ne, wani sashen kuma ya kore wannan tunanin tare da tuno mata, tana budurwa ma haka ya dinga Wannan wula'kancin har ta yi zaton soyayyar ne bai iya ba. A daren Mk na zaune a falon sama yayin da Farida ta yi filo da cinyarsa, yana wasa da dogon gashinta tamkar mai yin kitso, sai fama yake da bugun zuciya adalilin yana son fa'da mata, juma'a mai zuwa daurin aurensa da Sa'adatu. Sau uku yana yun'kurin fa'da sai ya kasa, da 'kyar ya yi kundubalar cewa " My ferial tashi ki zauna magana zamu yi da nake bu'katar nutsuwar ki'. Ta tashi da sauri kuwa, ta zauna sosai tana fuskantar sa. Cikin karfin hali ya ce " Ranar juma'ah mai zuwa idan muna cikin rayayyu, za'a mayar da aurenmu da Sa'adah". Wani irin tashin hankali ya ziyarci Farida, irin wadda bata ta'ba hasashen zata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157