Chapter 1
Chapter 1
[5/11, 17:15] ~fatieshak🌹: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *Bismillahir Rahmanir Rahim* *Ina farawa da sunan Allah, ina neman tsari da rubuta 'Barna! Ina rokon na yi rubutun da za'a 'karu , ayi amfani da shi.Tsira da aminci ga shugaba Annabi(S.A.W.).* *GARGADI* _A kiyayi taba min labari na ta kowacce siga, Hakkin mallakar tawa ce ni ka'dai, Dole sai da izinina kafin a karanta shi a kowacce irin kafar sadarwa, wadda ya shiga hakkin mallaka kuma ubangiji ya isar mini._ *JAN KUNNE* *Gaba'daya Wannan labarin kirkirarsa aka yi(Fiction)!haka sunaye da garuruwan da ke ciki bana kowa bane, na zabe sune kawai dan 'kawata labarin, dan haka duk wadda yaci karo da abin da ya yi kamacanceceniya da rayuwar sa bada shi ake ba, arashi ne kawai* *JINJINA* _GA MARUBUCIYA_ *FADILA LAMIDO* *SUGARI BA KI YI FARIN BANZA BA*. *SADAUKARWA* _Tun daga farkon labarin har zuwa karshen sa gaba'daya sadaukawa ne ga shugaban kungiyar_ *LAFAZEE WRITERS* *SADIQ ABUBAKAR*. 1-2 Harabar makarantar kwana ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kiyawa (FGC Kiyawa), cike take mak'il da motoci da jama'a kama daga iyayen yara, da su kansu daliban rukuni-rukuni, gungu-gungu, cike da walwala sai ciye-ciye ake yi kasancewar yau ake ziyarar dalibai (visiting day). Daga can gefen lambun makarantar, wata matashiyar uwa ce da a 'kalla ba za ta wuce shekaru talatin da biyu ba. Zaune take kan lallausar darduma wacce da alamu da ita ta zo, gefenta kulolin abinci ne da kuma ledoji masu dauke da tambarin *Sahad Store.* Zaune take tana baza ido ta ga ta ina tilon dan'ta zai bullo, ba ta ankara ba ta ji an rungume ta tare da ambaton "Mamiii!" Cike da dariya ta dago kai. "Jawad wai ba ka san ka girma ba ne? ba don a zaune nake ba ai da ka kayar da ni." Ya sake komawa ya kwanta a jikinta tare da cewa, "Nayi kewarki Mami! Ina Inna?". "Ta ce, a gaishe ka, shekaranjiya ta tafi Gamawa biki" "Ki ce ba ta yi mini girebar ba kenan?" Ya fada cikin turo baki irin na sakalan yara. "Wace ita? Ai ranar Laraba yini ta yi tana hidimar girebarka, bata samu sukuni ba sai da ta kammala." Sai a lokacin ya saki fuskar yana cewa, "Allah Sarki Innata!" Ya tashi a jikinta ya ci gaba da cewa, "Ina yini?" Ta amsa tana bin sa da kallon mamakin irin girman da ya 'kara cikin lokaci 'kalilan da ba ta gan shi ba, tana mamakin inda ya sami girman jiki tun da dai daga ita har mahaifinsa ba wani girma ne da su na a zo a gani ba, hasalima in ba ka sani ba cewa za ka yi 'kaninta ne. "Kai Mami sai kin gano munina!". Ya fada yana rufe idonsa da hannuwansa. Ta yi murmushi, "Girmanka ne yake ba ni mamaki Jawad ka kerewa tsawona fa!" "To, Mami aike tsayinki kadan ne, ni kuma irin tsayin Babana na yi." "A'a, kai kam sai ka fi shi tsayi duka-duka fa watan jiya ka yi sha uku amma ka zan'kale haka!" Cikin shagwaba ya fara fadin "Haba mana Mami ki daina fada, kar ajiyo. I am 15 fa!" Ta kwashe da dariya tare da cewa "Mantawa na yi ashe ka fi ni sanin ranar haihuwarka?". Daidai lokacin ya zuge Jakarta ya dauko tsaleliyar wayarta ya mik'a mata, ''Bude mini na kira malam na ji ko ya dawo." Ba ta ce uffan ba, ta karba ta bude masa kamar yadda ya bukata. Lambobi ya shiga daddanawa har ya jera lambar da ke adane a 'kwa'kwalwarsa a cikin wayar ya danna kira ya kara a kunne, tamkar da ma jiran kiran ya shiga ake yi, ya ji an dauka ba tare da ba ta lokaci ba, sallama ya yi tare da fadin, "Malam!" Daga cikin wayar aka amsa da, "Jawad kana lafiya? Ka gan ni nan ina kan hanyar zuwa wurinka." Cike da murna yace. "Ka dawo daga Bauchin ke nan?" "A'a ban dawo ba yanzu dai nake kan hanyar dawowa na iso Babaldu zan biyo ta Dutse na iso Kiyawa." Dadi ya kama Jawad, ya shiga masa addu'ar isowa lafiya, tare da cewa, "Ina wajen da muka zauna a waccan ziyarar." Ya kashe wayar yana cewa "Oh! Allah ya so ni, jiya fa da na yi masa waya ha'kuri ya ba ni akan ba zai sami zuwa ba sai satin sama, saboda yana Bauchi, ko don bai ji na amsa masa na ha'kura ba ne, shi yasa ya bar komai ya taho?" Ita dai ba ta sa masa baki ba har ya kammala maganarsa. tana nazarin lokaci a agogon hannunta daya nuna 'karfe biyu har da mintuna talatin da biyar. "Ko ina ne Babaldu kuma? Ko har zai iya isowa kafin hukumar makaranta ta rufe shigowa?" Tabe baki ta yi tana ji a ranta to ina ma ruwanta? Amma wani sashi na zuciyarta na fada mata saboda Jawad ne, ina mama ba wadda ya zo mini? Ya katse mata tunani, "Baban Khalifa ne ba lafiya yana asibiti ka ga ai bai kamata na yi maganar mu taho tare da wani cikinsu ba." "Me ya same shi?" Ya tambaye ta cike da nuna damuwa. "Malaria yake ta yi har ta kada shi." "Muma Mami ita ake ta yi anan, Allah ya sauwa'ke ya bashi lafiya, to yanzun a tasha kika sauka?" Ta girgiza kai tana cewa, "Shatar mota muka dauko ni da iyalan gidan Ma'aji. Ka ci abincin sai mu je ku gaisa, suna can gefen mata." Bayan La'asar ba da jimawa ba, ya iso cikin makarantar sanye yake cikin tsadadden yadi fari 'kal! 'Kafar shi dauke da takalmi cover ba'ki, kansa cike da gashi, ya dora hular zanna-bukar wadda ba ta rufe gashin ba, 'kamshin turaren Versace ke tashi a jikinsa. A hankali yake tafiya cikin nutsuwa, matsakaicin jiki ne dashi, amma dogo ne yanayinsa daya da tauraron wasan kwaikwaiyon nan Yakubu Muhd, ba yadda za ka yi ka kalle shi ka ce shi ya haifi Jawad, sai dan tsananin kamar da Jawad ke yi da shi. Tun kafin ya'karaso Jawad ya hango shi, don haka ya kwasa da gudu ya nufe shi. Ga mamakin Sa'adah, sai ta ga ya 'daga Jawad cak ya yi juyi da shi tamkar yadda yake masa yana yaro. Ya dire shi, ya ru'ko shi ta gefen shi suka doso ta, wadda duk ilahirin mutanen dake wajen sai da suka bi su da ido suna sha'awar Jawad da Babansa. Kujera ya samo masa ya zauna daga gefe, amma ba wani tazara da inda Sa'ada ke zaune, ta juya musu baya. Hira suke cike da doki. "Amma anya Jawad kana karatu kuwa? Ina *C.A* Result dinka?" Ya zura hannu a aljihun wandon shi ya zaro takarda ya mika masa ya karba ya bude yana dubawa, fara'arsa na 'kara fadada, ya ninke ya kalli dan nasa ya ce, "That is my boy weldone! Ka ci gaba da dagewa." "Ni da zan zama direban jirgin sama, ai dole sai na yi karatu Malam, ko ka manta?" "Murmushi kawai Malam din ya yi yana satar kallon gefen da Sa'adah ke zaune kamar ko yaushe ta ci kwalliya ta burgewa cikin tsadadden leshi doguwar riga(bubu), hannayen ta sun ci jan lalle da zobunan Dubai Gold, 'kamshinta na dindin na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157