Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana rayawa ko sai yaushe Inna za ta dena mata bitar wannan nasihar a duk sadda zata fita? Jikin ta yayi sanyi, nasihar ta matu'kar ratsata. take ta ji ta fasa zuwa inda ta yi niyya, tunda gidan su Halima zata je su hadu da Khalil dake duk kusan unguwar su daya. Tunda akayi hutu basu hadu ba, a dalilin fushin da yake yi da ita, yana zargin soyayya suke ita da Uncle Mukhtar. Baisan gidan su ba, kullum cewa take ba a barinta yin zance, sannan indai aka ganshi yaje gun ta za ta Sami matsala babba, nan kuwa gani ta ke da kunya yazo ya ga gidansu. Nasihar Inna tasa ta canja shawara gara kawai yau ta kaiwa Zainab Ma'aji ziyara ta huta da gorin da ta ke mata na ba ta zuwa gidansu, tunda dama nan ta cewa iyayen ta za ta. Tana fita yar tafiya tayi 'kadan, tana jiran ta tsallaka, kamar ance 'daga kanki kawai sai idanuwan ta ya fada cikin na shi yana fitowa daga wani shagon aski da ke gaban gidansu kadan. Mamaki ne ya kamashi ya tsallako ya same ta, tuna nasihar da ya musu na nuna ladabi yasa ta risina tare da fadin "Barka da rana" Maimakon ya amsa da hausa sai ya juya harshe, yace "Sa'adah how are you"? how ur parents and everything?" A hankali tace"very fine" Ya sake fadin "are you living here?" Kai kawai ta 'daga tare da nuna mishi gidansu "this is our house" bata san mai yasa shi bata ji, kunyar nuna masa gidan nasu ba, kamar yadda ta ke jin kunyar su Halima da Khalil su ga gidan. duk kuwa da bashi da makusa tunda ginin bulon siminti ne, a shafe yake da filasta, 'kyauren 'kofar shiga lafiyeyye ne mai aminci, sabanin gidajen su 'kawayen nata manyan gates ne dasu, masu zubin mahadi ka ture mussaman gidan su Safina da Humaira Suraj, nasu Halima ne dai ba wani shararren gida bane amma darajar unguwar ma kadai ta kerewa tasu unguwar. Yayi murmushi tare da fadin "wonderful I know ur father since" Da mamaki ta kalle shi tace 'Realy"? "Sosai kuwa for over 5 years, is he around?" "No yaje Gogel 'dazu" "Said it in English" Ta tura baki alamun ya fara son 'kureta wadda shikuma hakan da tayi drives him crazy. Tace, "He went to our Home town" ta tsuke bakinta ta yi shiru in ma bata yi dai dai ba 'karshen dagewar ta kenan. Murmushi yayi ya sake cewa "oh rude Sa'adah!" Har cikin ranta take jin dadin yadda ya yanke sunan yake fadin Sa'adah! Bashine farkon fa'da mata hakan ba, amma shine farkon wadda ya iya fadin sunan, shinea farkon wadda yasa mata son sunan. Ba zato ta ji yace "where's is ur loverboy"? Kunyar duniya ta kamata ta yi 'kasa da kai tana jin kamar 'kasa ta tsage ta shige, Ganin yadda ya kunyata ta, yasa shi tambayar inda zata, Kai tsaye tace "Gidan su Zainab Ma'aji". Sai ya mata sallama, ya tsallaka ya hau mashin dinsa. ganin haka yasa ta wuce ta nufi gidan su Zainab. Cike da shauki ta isa gidan su Zainab din, a dakin dake mallakin tane da yayarta Asiya suka zauna, suna hira, tare da Anty Asiya gaba'daya, cike da farinciki take basu labarin haduwarsu da Uncle Mk yanzun nan. Asiya ta ri'ke baki tana kallon yadda Sa'adatu ke bada labarin shi cike da 'doki da farin ciki, kasa 'boye mamakinta ta tayi, tace "Sa'adatu da wuri haka?" Cike da rashin fahimta tace Kamar "Yaya da wuri haka, ban fahimce ki ba?" Cike da iya shege Asiya tace "Ato na ga a duniya kin washi ayi maganar bawan Allah nan, abin mamakin kuma sai gashi yau da kanki kina hirar shi cike da shauki da jin dadi, shine nace da wuri haka har 'kiyayyar ta 'kare?" Kunya ta kamata sai cewa tayi "Ni fa ba gun ki nazo ba, kuma bada ke nake zance na ba". Dariya suka sa mata daga Zainab har yayar tata, take kuwa takaicin su ya kamata sai kawai ta fashe musu da kuka. Nan da nan kuma jikin su yayi sanyi, suka gintse dariyar, suka hau bata ha'kuri, barin ma Asiya da ta ke ta fadin "daga wasa, nifa tsokanar ki nake, to yi ha'kuri ba zan sake ba" da ga haka ta mi'ke ta bar musu dakin cike da mamakin shagwaba irin ta Sa'adah. Da 'kyar Zainab ta shawo kanta ta huce, ta shiga bata labarin tunda akayi hutu basu hadu da Khalil ba, saboda yana fushi da ita akan Mk. Tabe baki Zainab ta yi tana fadin jimin yaro da 'karfin hali, to shi da nufin sa baza ki kula wani ba? bama shi da hankali. Sanin da Sa'a ta yi Zainab ba ta yin Khalil, ya sata tsuke bakin ta, har sai da ta gama caccakar shi ta 'kosa dan kanta, ta bar maganar. Wai a Ina kika ga Uncle Mk din? Zainab ta tambaya cike da son jin 'karshen maganar da Asiya ta so watsawa. Bata rai ta yi tace inace dariya ku ke min?" "Ni ba ke na yiwa dariya ba, Yaya Asiya ce ta bani dariya da ta shiga zancen da ba na ta ba". Numfasawa ta yi tace "A 'kofar gidan mu ya fito a wannan shagon na The Boss barbing shop". Amma dai kin gaishe shi, Zainab ta tambaya da sauri. "Ah sosai ma har hira mun yi" Murmushi Zainab tayi tare da fadin "In sha Allah wannan ne mafarin hirar taku, ba 'karshe ba" Da sauri Sa'adah ta dube ta, tace "saboda me kika ce haka?" Kai tsaye ta bata amsa da cewa "saboda kuna son junan ku" Sunkuyar da kai Sa'adah ta yi tana mamakin yadda ta hasko tana son Mk, sanin Zainab akwai ta da sa ido sai ba tayi mamakin gano ta da ta yi ba. Kamar zata yi shiru sai ta kasa tace "Zainab shi ba ya sona, Farida ya ke so", ta fada cikin muryar kuka. Hannunta Zainab ta ru'ko cikin lallashi tace "Wallahi yana son ki, ke duk wannan takurar daya miki a banza ce? kin ta'ba tunanin mai yasa ke kadai ya damu ki maida hankali a kan karatun ki? Ni na dade da gane yana sonki amma irin mutanan ne masu kiyaye doka da oda. kinga ai bai dace ya nuna miki soyayya alhalin aikata hakan laifi ne babba da hukumar makaranta ba za ta amince da shi ba, Sannan Farida 'daliba ce mai haza'ka irin su farin jini ne da su a gun dukkan malami ba wai Uncle Mk ba kawai. gaskiya ba sonta ya ke, so irin na soyayyar saurayi da budurwa ba, illa 'kaunar da malami yake yiwa dalibarsa mai ladabi da haza'ka". Cike da gamsuwa Sa'adah ta sake cewa "Ba kya ganin 'kaunar da ya ke mata zai iya juyewa zuwa irin son dana ke jin tsoro?" Shiru ta yi na 'dan lokaci,sannan ta nisa tace "Sa'adah gaskiya zai iya juyewa amma idan kin cigaba da bada 'kofar faruwar hakan". *Alkalamin Surayya Dee* ✍🏼✍🏼 [5/22, 12:02] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});