Chapter 121
Chapter 121
da ba garinmu daya ba,shi daga Bichi, Ni kuma daga Wudil. A lokacin da Kabiru zai auro uwarka Rabi, mahaifina ne ya zo ya karbar masa, duk da ga kannen mahaifinsa nan hakan ya faru ne bisa amincewar mahaifin nasa da yan'uwansa. Ka san dai kaine dansa namiji na farko amma baisa sunan mahaifinsa ba, sai ya saka sunan yayana da ya fa'da a ruwa ya rasu a shekarar". Ya yi shiru yana goge hawayen da ya kasa maida su, dukkan jikin Mk da 'Karfi ya yi sanyi, da kyar 'Karfi ya ce "Sannu Baba sai a ha'kuri!" Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi fiye da ta farko ya zarce da cewa "A bayan mun yi aure har mun haife ku na samu matsala da Zuwaira na yi fishin zuciya na saketa, na yi rantsuwar na gama zama da ita. Bana mantawa dawowar mahaifinka daga Bichi ya samu labarin rabuwarmu a bakin yara, da ya juya Ashe Wudil ya tafi a yammacin, wajen karfe takwas na dare sai gashi ya dawo da ita. Washagari na tashi da azumin kaffara domin bazan iya kunyata Kabiru ba, ko na nuna masa bai isa ya yi hukunci a gidana ba. Har yau din nan ban sake tada maganar ba sai yanzu da nake baku labarin, amma kai sai ka nuna mu iyayenka bamu isa ka mana alfarmar cigaba da zaama da matarka bare kuma wannan abokin naka". Ya ja hankici ya goge fuskar sa ya ce "Har Kabiru ya kwanta dama bashi da aljihun kansa, haka nima bani da nawa, koman mu daya ne, Ina da ikon zartar da hukunci a gidansa haka nima yake da cikakken iko, shiyasa na tsorata ainun hankalina yake tashi idan na kalli al'amarin da ka yi mini, na baka umarni, ka kafe ka kasa yi mini alfarma, sai nake ganin da mahaifinka yana da rai da ka ga 'kwanjina. Amma tunda ni ka'dai na saura muku sai na biku da yadda kuke so tunda ubangiji ya nuna mini wannan zamanin da ya zama iyaye sun koma agwagi." Mk ya ce "Ka yi hakuri, ka kara hakuri Baba" Ya nisa ya ce "na ha'kura amma ka sani ni ba zan iya zuwa wajen Malam Basiru ba, bani da wannan kwarin guiwar, domin har yau din nan girmama ni yake tamkar shakikin yayansa ba kuma dan kowa yake mini hakan ba, illah dan kai domin ni ban san shi ba, sai adalilinka" Hankalin Mk ya sake tashi ya ce " Duk cikin Kano bani da wadda ya fika Baba! Idan kuwa ka ha'kura to kaine mai karba mini aure a ko ina". Alhaji ya ce " ka fadi Gaskiya! sai dai na san daddako irin na Malam Basiru da irin yadda ya girmama lamarinka zai iya tirsasa yarinyar nan ko bata so ya dawo maka da ita dan soyayyar da yake yi maka. Ni kuma na ta'ba fa'da muku kai da ita daya kuke a gurina nine alkalinku, alkalanci na gaskiya zanyi a tsakanin ku. Zan je na nemar maka aurenta kadai, idan na ji a bakin yarinyar da amincewarta zan nema maka aurenta". Da sanyin muryar ya ce "fishi take yi da ni Baba! Amma da zarar anyi auren zamu dai-dai ta, tana sona wallahi" "Ashe dai ta san ciwon kanta, domin kuwa ka yi mata laifin da duk wadda ba ya jin tsoron zuciyarka zai fa'da maka cewa "komin girman laifin da ta yi maka, hukuncin da ka dauka akanta ya yi tsauri, ya wuce makadi da rawa, ko kadan babu a ragayya cikinsa". Jikin Mk ya dinga bari sosai, shi da kansa ya san kunyar Baffah ya jita irin wadda bai yi zaton anan kusa akwai wadda ya ta'ba jin irin wannan kunyar ba. Amma ya tabbatar da ya fito ya fa'di laifin da ta yi masa na cigaba da mu'amala da tsohon saurayinta, da ba wadda zai dora masa irin wannan laifin na bai yi adalci ba, domin munin abin ya baci, ba ta da hurumin yin hakan ta kowacce fuska tunda ba muharraminta bane bata da alaka da shi ta kowacce fuska, sai tsohuwar soyayya. Amma son da yake mata ba zai bari ya fadi wannan al'amarin ba, domin da yawa wasu zasu zargeta, zasu kyamaceta, tunda idan ya ce tana tare da wani ne musabbmabbin rabuwar kowa da abin da zai raya a ransa, ba a kuma isa ace sai kowa ya yarda ba barna suke aikatawa ba, shi yasa ya zabi ya boye a ransa shi ka'dai, amma kuma dole su nisanta da juna tunda ba abin da shaidan ba zai dinga raya masa ba, zai dinga zarginta ne ko da kuwa ba hakan bane a zahiri kasancewar sa dan Adam mai rauni ba a ma'asumi ba". *UZZIRI* *Duba da muna cikin kwanakin nan masu tarin falala da albarka, sai nake ganin ya kamata mu jingine Wannan labarin dan samun damar ribatar kwanakin da ubangiji ya rantse da su, ba lallai mu riski na wata shekarar ba*. *Dan haka zamu tafi hutu sai bayan sallah idan muna cikin rayayyu zamu zo mu karasa abin da ya yi saura in sha Allah. Dafatan ubangiji ya karbi ibadunmu ya sa mu yi hidimar sallah lafiya, kar mu manta da yiwa KASARMU addu'a.* *Ubangiji ya bamu damuna mai albarka*. *Na gode muku sosai da yabawar ku kan rubutuna*. *Surayya Dahiru* ✍️✍️ Surayya Dahiru. ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Barkan mu da ibada! Barkan mu da bikin farin-ciki. Ina fatan ubangiji ya karba mana kyawawan aiyukanmu, ya shafe mana kurakurai. Ina yi mana Barka da bikin Babbar sallah, ubangiji ya dawo mana da Alhazanmu lafiya, ya kuma zaunar mana da kasar mu lafiya.* *Allah ya maimata mana*. 96-97. A tunaninsa space din da ya bayar a tsakanin su, dan ya samu zuciyar sa ta nutsu ne, ta daina wasiwasi akan ta, ashe laifine tunda ba kowa ne yasan azabar da yake dandana adalilin hakan ba. A sanyaye ya ce "shikenan Baba na yarda da hukuncinka zan kuma yi biyayya akansa in sha Allah". Tari ya sarke shi sai da ya lafa masa, ya ce " duk Ranar da kuka dai-dai ta da ita ka zo ka dauke ni, ka kaini gabanta, tunda nema muke yi". Suka yi godiya sosai suka Mike bayan sun ajiye masa kudi. A mota Mk ya ce "Karfi ka ji dadi da dake Ni, duk yadda aka yi dama kana son ka samu damar da zaka dakenin shine yau da Ubangiji ya ara maka dama, ka cire tausayi ka tafka mini bulalar da sai da na ji tamkar na saki fitsari a wurin". Cikin dariya sosai 'Karfi ya ce "Ashe baka iya tsiya ba, da ka saki fitsarin ai kaga dole na yi bi'kin wurin da ka bata, dole kuma na ruga wajen Farida na karbo maka wasu kayan ai ko banza ka wahalar da ni".
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157