Chapter 40
Chapter 40
nuna mini wai zai ki zama yadda kika zama Iyah zan karyata na kuma yi gaggawar neman miki tsari da wannan karko irin na kifi. Ta ya ya za a ce kin rayu kina tafiyar da komai na aikin gida da tsaftar jikinki akan lokaci da kuma kuzari, amma sai da aurenki ya zo gaf kuma sai lalacewa ta zo miki? Wayar nan mai tsada ta zamani hatsarin dake cikinta ya fi alherin da ke tare da shi. Ki rabu da wannan shiriritar tun ba ki fada tarkon da za ki kasa fitowa ba!" Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai tana gaskata mahaifiyarta, yau kadai da wayar take kashe ta samu rarar lokaci har sallar walaha ta yi. Ta kuma samu sukunin tattaunawa da uwarta, ta yi abin da ya dace na ayyukan yau da kullum. Inna ta sake nisawa ta ce, "Ba namijin da za ki je kina masa wannan ba'kin dabi'un da kika fito da su, ku samu zaman lafiya da shi, duk son da yake miki kuwa. Ban hana ki amfani da waya ba, amma ki dinga ajiye ta sai kin kammala komai na aki, nauyi ne zai sake kama ki, shi namiji idan yana da mata komawa yake yi tamkar jariri komai sai an yi masa, ta ya ya za ki iya kula da miji da hidimar gida da wannan danne-dannen wayar da tun ana ganin na 'dokin wayar ne har kuma ya koma na kauyanci da asaranci ya zarce hankali da ka'ida." A hankali Sa'adah ta ce, "Zan gyara Inna." "Na ji za ki gyara, sai mai za ki ce mini kuma"? Inna ta fadi haka tare da zuba mata ido. Cikin kunya "Sa'adah ta ce kai Inna don Allah, to ki yi hakuri." Kai tsaye ta ce, "Tafiya za ki yi ki fara rayuwa da wani mutumin da ba ki saba da shi ba, ba shi kadai zaman zai kasance ba har da dukkan ahalinsa don haka ki koyi ba da hakuri idan kin yi laifi, ki kuma zama mai karbar gyara yayin da aka gyara miki laifinki, wannan shi ne mafi dadin zama a cikin mutane, na lura da ke ba da hakuri na miki nauyi, sai tura ta kai bango kike tuba wanda alamu ne na girman kai. idan mijinki ya gane kina da girman kai kuwa, wahalar ki zai yi don shi ma girman kan zai miki indai ya san ciwon kansa, sai dai idan solobiyo ne." *** Bangaren MK yana ta Shirinsa musamman na gyran gidan da zai zauna, saukin da ya samu gidan mallkinsa ne da ya fado a gadonsa, tun lokacin yan haya suke ciki sai yanzu aka tashe su yake gyara, a unguwar Gadon Kaya gidan yake, ba wani babba ba ne amma tsarin gidan ya yi kyau, falo ne matsakaici mai dauke da manyan dakuna biyu da bandaki a cikin daki daya. Sai tsakar gida mai matsakaicin girma, daga gefe wani dakin ne shi ma da bandakinsa, sai daya gefen kuma kicin ne da wani bandakin karami, daga harabar gate kuma akwai karamin filin da zai dauki mota guda daya, ya shuka flowers sun fara fitowa wanda nan gaba za su 'kawata gurin. Gini ne mai aminci amma ba tayals ba ne siminti ne a dakunan. Shi kuwa a kokarinsa na son dadawa amarya Sa'adah yake son sanya mata tayals a falo da bandaki duk da a lokacin an fi saka carpet irin dan yankan nan. Aka fara aikin gida sai lashe kudi yake yi sosai, wanda hakan ya sake mayar da MK ya zama very busy kullum aka tashi a makaranta yana gidan gurin masu aiki, ko wurin neman ku'dinsa ba shi da lokacin kansa wanda hakan ya sake karfafa zaton Sa'adah na bai iya soyayya ba. Shi yasa take kula Khalil har yanzu! take kuma shan soyayyar 2go, idan MK ya zo shike nan idan bai zo ba, huta roro ba ta kewarsa. Sakamakonsu ya fito wanda WAEC din Sa'adah ta kasance ba yabo ba fallasa, amma NECO ta yi kyau sosai, a lokacin suka shirya bikin kammala makaranta da murnar sakamakonsu, ba laifi a shekarar an ci NECO sosai. A *HANG OUT* suka shirya yin bikin, a lokacin gun ne yake tashe a wurin samari da 'yan-mata, da kyar Inna ta bar Sa'adah ta halarci taron. Shi ma sai da ta yi karyar yayar Zainab ce ta haihu za su je, nan kuwa iya su 4stars ne, sai samarinsu na aji Irin su Khalil da kuma saurayin Halima Sagir. Haka suka yi wannan bidirin. Sa'adah a takure saboda wannan ne karon farko da ta ta'ba zuwa wani guri da sunan party, kuma a cakude da maza sai abin ya zame mata bako, ga dai kayan kwalama cike da teburinta hatta ice ream da ta ke jarabar so bata iya 'dan'danawa a bakinta ba, Khalil sai kaffa-kaffa yake yi da ita don ta sake, ita kuma sai raya ina ma kulawa da iya soyayyar Khalil, MK ne ya iya su. Tana cikin wannan tunanin wayarta, ta shiga ruri, tana dubawa taga MK ne, ta 'ki amsawa, tana tunanin idan ya ji wannan kidan sai ya ishe ta da tuhumar inda take. Bai daina kiran ba har sai da ta yi shahadar amsawa, jin hayaniya da kade kade yasa shi tambayar inda take, ta karkace baki ta shirya karyar ta raka Zainab gidan suna, yayarta ce ta haihu, ya yi shiru ba don ya gamsu ba, saboda ki'dan music yake jiyowa ba dan ka'dan ba. Ya nisa ya ce, "Son ganin ki nake yi, ya za a yi ke nan?" A ki'dime ta ce, "Ai anjima za mu dawo na san dai zuwa magariba mun iso." Da sauri ya ce, "Har Magariba za ki kai a waje? yanzu karfe 4, ki tabbatar biyar da rabi ta miki a gida, ina jiran ki." Ya kashe wayarsa ba tare da ya jira mai za ta ce masa ba, saboda bai gamsu a gidan suna suke ba. Ta yi shiru da waya a hannunta, tana tunanin yadda MK ya mata magana a gadarance tamkar ya zama mijinta, wani sashe na zuciyarta kuma so yake ta isa gida kafin lokacin da ya ce din. Duk kokarin Sa'adah na son ta bar wurin da wuri ya ci tura, su Safina sun hana ta, kan dole ta kashe wayarta don kada MK ya sake samun ta. Sai bayan Maghrib suka kawo ta gida, ita ce a gaban motar su Halima na baya, duk yadda ta so su ajiye ta a hanya Khalil kin yarda ya yi, don so yake mugun malaminsu ya ganta a motarsa tunda a unguwar yake sana'ar sa ta wanzanci, ya san kuma saboda shi take son su ajiye ta daga nesa. Su Halima na sake zuga shi ta hanyar cewa, "Idan ka ajiye ta a hanya wallahi soyayyarka ba ta kai ba!" Dai-dai lokacin MK yana kofar shagon kusa da jikin gidansu ana masa gyaran tayar mashin dinsa da ta yi faci, daf da shi Khalil ya tsaya, tsaleliyar mota(Continue Discussion) a wancan lokacin ita ce motar da take tashe ko'ina ka shiga maganar motar ake yi wanda shi ma ta mahaifiyarsa ce ya dauko, gaban Sa'adah ya sake tsananta bugawa musamman yadda hankalin mutanen wajen ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157