Chapter 18
Chapter 18
hutu tare da 'kannen shi. ba musu ya amince, har gida suka zo suka dauke ta, sannan suka dauki hanyar jos kwata, ta yamma da Bauchi😀. Wannan hutun yana cikin abubuwan da Sa'a bata Mantawa da shi, domin kuwa ta yi matu'kar jin dadin zama da 'kannen Idris yadda suka kasance yara kamammu, marasa hayaniya amma kuma yan kwalliya ne na sosai, shiyasa abotar su ta yi da'di. Sumayya kuwa ba ta matsa musu, hatta abinci wadda suke so shi zata ce su yi, mai gidan kuma kusan kullum sai yasa direbansu ya zaga dasu, sunga gari, da wuraren sha'katawa , sannan kuma duk fita sai ya basu kudin kashewa, wadda ba abin da suke siya sai kayan kwalliya ko dai abin da ya shafi sutura. Ba abin da ya dame su illah tunanin mock exam din da suke fargaban fitowar ta, tunda dukkan su set daya suke Amma makaranta daban daban. Haka suka 'kare hutunsu cikin jin Dadi da mutunta juna, da kanshi Idris ya kawo su har gida tare da kayan tsarabar ni'ki ni'ki, barin ma dankalin turawa da dangin su cabbage da Kara's, harta atile kamar wadda za'a ci a tsawon wata. Baffa da Inna sai godiya suke,tare da sake godiya ga Allah, na yadda Sumayya ta sami mijin daya San alheri yake kuma rama alherin da kyautatawa da mutunci. Barinma idan ta zauna tana bawa Inna labarin daular da Anti Sumayya ke ciki, sai dai ta yi murmushi mai nuna yadda zuciyar ta ke cikin farin ciki. Ba zata yi magana ba sai dai ta bige da cewa kema Allah ya ba ki mijin rufin asiri, yasa ki dace kamar na yar'uwarki. Ita kuwa kai tsaye take cewa "Amma fa Inna gaskiya ni bana son irin tsarinsa, ace mutum duk inda matarka zata fita kace sai ta zumbula hijabi har 'kasa, kuma wai dole sai ansa safa? ko 'dan wanne mazahaba ne?" Cikin mamaki Innar ta zuba mata ido, tare da tafa hannu tana sallallami tace "ke kuwa Iyah wannan tsarin da yake yi na martaba shari'a ne bai Miki ba? Na mijin kwarai shi ke kishin matarsa, ya 'dora ta akan ka'idojin shari'a, wadda zasu gudu tare su kuma tsira tare! "Daular da ya sanyata a ciki ta burge ki, kina kuma fatan ki samu irinta, amma abin mamaki, hijabin da Ubangiji ne yace a saka shine bai miki ba? Anya Iyah, Baffan ku bai yi kuskuren barinki shiga wannan makarantar da ta ke sake girmama burinki ba?" Da sauri tace "Haba mana Inna! ni fa ba cewa nayi kar asa hijabi ba, gani na yi tana da tsala tsala dogayen riguna tunda ga kan yan 'kasashen Oman, Qatar, Saudi, Dubai, masu tsadar gaske masu kauri, amma wai dan 'kauyanci kuma sai akawo hijabi a maka, bayan su karan kansu hijaban ne". Ta fa'da tana fashe wa da dariya. Allah ya shirye ki kawai, Inna ta fada tare da mi'kewa ta yi tsakar gida, tana fadin wannan dogon burin na ki yana ban mamaki Iyah. Ban da 'karya da fariya, da kai kanka inda Allah bai kai ka ba, gidan uban wa kika san 'kasashen da suke sarrafa riguna masu tsada? Naga dai ke kam baki da halin samun su, ban da Allah ya miki gata ya baki yar'uwa mai halin girma tana baki kuncen su, wasu ma ko saka su bata yi, ta ke baki, amma har ki zauna ki karkace baki kina min lissafin inda ake sarrafa su?". Ta cika fam saura 'kiris ta fashe cikin turo baki tace "Amma Inna abin har da gori?" Da sauri tace "Eh dole na goranta miki, dan na ga nema kike ki manta cewa ke'din ba yar kowa bace, face malam Basiru mai 'yar tireda😀wadda ko hanyar inda jirgi ya ke sauka ba ki ta'ba zuwa ba, Amma kina bada labarin 'kasashen duniya, wallahi Iyah ki canja wadannan halayen da nake ganin kina sake arowa kina yafawa". Shiru Sa'a tayi amma takaici ke cin ta shikenan sai mutum ba zai fadi ra'ayin sa ba? Sai a hau mishi gore-gore, har a nemi cewa ya raina shari'a? Hawaye ya siraron mata, ta goge ta tashi ta yi 'dakinta, tana fatan Allah ya bata miji mai kula da iyali kamar Idris, amma ba mai a'kidunsa na asalin bahaushen arewa ba. Kayanta na makaranta ta shiga fitowa dasu tunda ga kan uniform, sandal, school bag dukkan su sabbi ne, ta shiga shirya su ta yadda gobe sai dai ta dauka a kammale. Ba tasan meyasa ta ke 'dokin komawa makarantar ba wannan karon? domin kuwa tunda Mk Bichi yaje makarantar ko hutun weekend ne fargaban zuwan Monday take yi. Wata'kila kuma dan ta sami sau'kin kunyata ta da yake yi ne. Amma Kuma duk da sau'kin da ta Sami a bangaren shi, haushin shi da tsanar shi na nan cike a zuciyar ta. kwanukan abincin su ta wanke su tas kafin ta kammala wanke wanken har gawayin ya fara kamawa, dan haka ta cika tukunya ta dora ruwan wanka, tana gama wanke kwanukan, sai kuma ta hau share tsakar gidan hadi da wanke dan matsakaicin bandankinsu, kafin wannan lokaci kuma ruwanta yayi zafi, ta juye ta shiga wanka! bayan ta maida ruwan kunu da ta jefa mishi tsamiya kan wutar. Tana fitowa a wanka innarta ma ta fito tsakar gida, tana ganin yadda Sa'a ta gyare mata gida tsab. Da'di ya kamata na yadda ko kadan Iyah bata da son jiki. Ba zato ta ji anrungumeta tare da cewa "morning Innah" Ture ta tayi tare da cewa "oh ni kam Ina kallo a gun ki". Dariya tayi tare da fadin "Inna gaisuwar kawai shine abin kallon"? Wuceta ta yi tana bude ruwan dake Kan gawayi, ganin yana shirin tafasa yasa ta fara shirin dama kunun, ita kuma sa'a tayi 'daki tana shiryawa. Cikin 'kankanin lokaci da dama kunun, ta kuma dauko fulawar data kwaba a 'karshen dare dan yin fanke, ganin ta tashi sosai yasa ta maida mai kan wutar tana shirin suya, tana kwashe kaskon farko Sa'adatu na fitowa ta shirya amma bata sanya uniform ba. Ganin yadda innarta ke kwaso fanke yayi brown ya tashi sosai, da'di ya kama Sa'adatu. Sai kawai tafara rawa tana juyi tana wa'kar "Mamana, mamana! mai sona, mai tattalin zuciyata". Kwafa Inna ta yi tana fadin "zanga sadda za ki girma Iya" "Idan Kinga na girma sai kin haifa min 'kani ko 'kanwa". Ta wuce ta dauko, kofi da plate tana fadin "Allah Inna Ina son 'kanne gashi Anti Sumayya tayi min nisa bare na dinga debo su Khalifa". Ta fa'da cikin muryar tausayi tamkar hakan zaisa innar ta haihu yanzu yanzu. Numfasawa Inna ta yi sannan tace "Ai kin kusa samun 'ya'ya ma indai kina da rabo, ba'di iyanzu ai kina dakin ki ". Daure fuska tayi, sannan tace "Nifa sai na fara karatu". Da sauri Inna tace "Inma karatun za ki zama sai dai a dakin ki, tun yanzu kina ruwan ido kowa ya zo kice ba kya sonsa, amma kuma kina son duk wani abu da zai 'kullo ya baki". Mi'kewa ta yi bayan ta debi kunu da fanken tana cewa "To Inna ai ba ro'konsu nake yi ba, Kuma Annabi yace ba kyau mai da hannun kyauta baya"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157