Chapter 110
Chapter 110
yanzu zuwa kowanne lokaci zai ji muryar ta, tana nan cikin koshin lafiya. Suna gama waya kuwa ta tura musu sabuwar lambar Sa'a. Jikin Mk har bari yake wurin kiranta, amma sama da sau goma ta ki picking. Tana kwance a dakinta tana kallon Yadda Kiran ke ta shigowa. A ranta tana fa'din har abada ban son jin ka, Jawad din ma na yafe maka shi". Mintina goma sai ga kiran Sumaayya a layin Inna, ta dinga yi mata fa'da tamkar ta shigo ta wayar ta daketa, saboda itama ta kira layin nata bata dauka ba a tunaninta Mk ne. "Iyah kalaman Jawad sun tayar mini da hankali tunaninsa mutuwa kika yi ake boye masa, idan kina haka har yanzu akwai kullin Mukhtar a ranki. Ki amsa masa waya Jawad ne zai yi magana da ke yafi sati yana cikin damuwar rashin ji daga gareki". "Ni wlh Anty har Jawad din ma bana bu'katar jinsa ina masa addu'a, ina fatan ta zame masa garkuwa a ko ina yake". Sumayya ta ce " To shi laifin me ya miki haba Iyah! Ki ji tausayi mana". Da kyar ta shawo kanta ta yarda zata 'daga wayar. Ba a jima sosai ba kuwa, 'Kiran ya sake fa'dowa wayarta. Ta dauka ta yi shiru, sanin da Mk ya yi dabiarta ce ba zata fara yin magana idan ya 'kira a waya tun fil'azal sai bai wani damu ba, ya dinga yin sallamah, ya koma cewa hello nan ma shiru, ya mayar da wayar hand free, a tunaninsa jiyota ne ba ya yi. Yaayin da Sa'adah tsananin bacin rai ne ya kamata akan me zai mata magana, ya bawa Jawad din wayar mana. Murya a sha'ke ta ce "Jawad!" Ran Mk ya baci wato tana jinsa amsawa ne ba zata yi ba. Amma a zuciyarsa ya samu nutsuwa kwarai da gaske da ya gane tana nan cikin koshin lafiya har ma tana da kwarin guiwar yin wulakanci, dan haka sai ya mi'kawa Jawad wayar a fusace. Ya tsurawa Jawad ido yadda ya ke magana yana wani irin murmushi, ya sake kallonsa sosai yana ganin ba kammanin Sa'a tare da yaron illah wushirya da farcen hannayensa, inka dauke Wannan tamkar Mk aka raba biyu aka yi shi dan tsananin Kamar da suke yi. Ya nisa ya tuno yadda Sa'adah ta tsaya a gabansa tana sheganta masa yaro, banda dai so baya shawara ai da bai kamata ya cigaba da son Sa'adah ba. Ya muskuta yana kasa kunne yana sauraron hirar su inda ya ji Jawad na maganar da ta ja hankalinsa. "Mami na tara ku'din da zai ishe ki zuwa, zan fa'dawa Malam zan zo na taho da ke". Ya juyo murmushin Sa'a da yake kashe masa zuciya ta na cewa " A ina ka samu kudi?" "Idan Malam ya bani bana kashewa, sannan munje gidan freinds dinsa na samo ku'di da yawa, kuma Anty ta je da ni gidan sister dinta nan ma anbani kudi duk na boye miki su". Dariya ta kwacewa Sa'adah ta ce "Ka siyi abin da kake so ka ji Jawad! Kudin ba zai isa na zo ba". Ya fara mata kuka yana cewa "kudin fa da yawa Mami! a school ma da muka yi tseren gudu da quiz na zo na daya an bani kudi da yawa har da chain din gold, na boye miki shima". Kukansa ya ta'ba ta sosai dan haka sai ta ce "To ka ai baka da kudin zuwa da na komawa, iya nawa ka tara ka bari sai ka sake tarawa sai ka zo ka dauke ni". Cikin kuka ya ce "Zan fadawa Malam ya biya mini". "To ka daina kuka, idan kana kuka, bazan yarda na zo ba, sannan ka bari sai anyi hutun school, dan kar a wuceka a karatu, kuma ko ba ka ji ni a waya ba, ka daina damuwa kasan Ni ma ina zuwa school, karatu ne yake boye ni, amma kullum ina yi maka addu'a". Ya goge hawayen ya ce " Na daina kukan, idan zaki mini addu'ar, ki dinga addu'ar kudin nawa ya isa na siyi jirgin kawai. Kinga sai na yi ta yawo da ke har da su Inna da Hajiyar Bichi." Suka dinga hira sosai, suna Shirin yin sallama ya ce na bawa Malam ku yi magana? shima ya damu da ba bamu same ki a waya ba". Mk ya sake kasa kunne dan ya jiyo amsar da zata bayar. "Ai mun gaisa kafin ya baka wayar, stay blessed my Boy". Daga haka ta katse wayar. Da wani irin kuzari Jawad ya mikawa Mk wayar yana fadin "thank you very much Malam". Da zai karbi wayar sai ya hada da hannunsa ya janyo shi ya dora shi akan cinyoyinsa. "Da sakakkiyar fuska ya ce " Me yasa ka damu sai Mami ta zo nan alhalin kasan bata son zuwan?" Da sauri ya ce "Lah tana son zuwa fa, tana son ka mayar da mu gidanmu mu dinga kwana tare, da zamu taho na roketa ta biyo mu na san ba zaka yi fa'dan mai yasa ta zo ba". Mk ya dinga jin wani iri, a karancin shekarun Jawad ya shaide shi ba zai wulakanta uwarsa ba, anya bai kamata ya sasanta da Sa'adah haka nan ba? Tunda ya lura a fili Jawad yafi son uwarsa akan komai. A hankali Mk ya ce "To ya baku taho taren ba?" Ta ce mini "Ba ita ka ce ta zo ba, Anty amarya ka ce ta zo, sannan bata da ku'din zuwa, na ce mata ai Baban Anti ne ya biya mana, shine ta ce ita Baffanta ba shi da kudin da zai biya mata! Sai na ce to ni zan tara kudi na biya mata itama". Jikin ya Mk ya yi wani irin sanyi, ya dinga jin kalaman yaron har cikin zuciyarsa. A shekarunsa na goma sha'daya har yasan kishin uwarsa? ya tuna duk sadda ya samu kudi yake nacin shi zai ajiye abinsa ashe uwarsa yake yiwa tanadi? Ya nisa ya sake tuno lokacin da makarantarsu ta karrama shi da bashi chain din gold, da suka dawo gida ya shige dakinsa ya masa boyo na mussaman duk rarrashin da Mk ya yi masa akan ya kawo a ajiye masa, ya ce shi ya boye da kansa, ashe duk uwarsa yake yiwa? ba abin da ya tsayawa Mk a zuciya irin da Saadah ta ce wai ita Baffanta ba mai kudi bane. Shiyasa 'danta ya kudiri aniyar ya tara mata kudi, dan ya huce mata takaici. A ranar Mk ya ji ya yafe mata kaso sittin cikin kullacin da ya mata, ya samu saukin da zuciyarsa ta yi akan lamarinta, sai dai wannan tsoron nata da ya shige shi, bai ragu ba. Ya lura idan bai bi a hankali ba, nan gaba ba karamin matsala Jawad zai bashi ba, mussaman da yana sane uwarsa tana son ya mayar da su gidansu, amma bai yi hakan ba. *** Tunda suka yi shekara da aure ba labarin samun karuwa! Farida ta fara jelen ganin gynecologist, duk wani gwaje gwaje anyi mata an tabbatar komanta lafiya kawai lokaci ne bai yi ba. Zuwa wannan lokacin Mk ya samu budi sosai adalilin tallafin da gwamnatin tarayyar Nigeria take bashi, ga albashinsa, ga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157