Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rawar murya ta ce, "Me zan dora?" Kamar ba za ta kula ta ba sai kuma ta ce, " Dambu!" Hawayen da ta ke matsewa ya balle tasa gefen dan'kwalinta ta goge, sannan ta ce, "To!" Haka ta hau aikin sarrafa dambu tana goge hawayen da ya'ki yankewa ta san dan a musguna mata yasa aka 'kir'kiri yin abincin da zata jima bai kammala ba. Ba ta sami kanta a hannun Inna ba sai wajen karfe uku, saboda yadda ta'ki sa mata hannu, ada idan za su yi dambu kusan Inna ke jagorantar yi, kawai sai dai Sa'adah ta sa ido tana lura tare da gyara gyada ko zogale. Amma na yau komai sakar mata ta yi, ta kuma kara yawansa a cewar ta za ta aika wa makwabta, ita dai Sa'a ba bakin musu saboda a tsorace take da ita don ba karamin duka ta mata ba. Faranti guda ta cika da danbun ta debi ruwa a randa mai sanyi ta sami inuwar bishiyar dake tsakar gidan, ta fara ci hannu baka hannu kwarya tamkar ba Sa'adah mai cin abincin a gayance ba.😁 Inna na kallon ta a ranta ta ce, "Ja'ira yau kin gane yunwa ba kanwar uwa ba ce." Sai da ta share abincin nan tas ta yi gyatsa gumi ya karyo mata, ta yi Hamdala. Ta jima a zaune a gun, sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan ta cika bokiti da ruwa, ta jira Inna ta fito a bandakin sannan ta shiga wanka. Sai da ta yi sallah sannan ta shirya, kana kallon ta kasan zuciyarta ba walwala, tana zaune waya a hannu tana ta kiran MK amma ya ki dauka, lamarin da ya sake dugunzuma damuwar da take ciki, a fili ta ce, "Me yasa nake son mutumin nan ne?" Ta sunkuyar da kai tana tunano adadin yadda take shiga damuwa saboda shi. Haka ta ci gaba da kira ba kakkautawa har ta gaji. Sai kuma ta koma tura text din ban hakuri da maganganun soyayya masu taushi. Amma ko sau daya ba ta ga amsa ba duk kuwa da sun nuna mata sun yi delivered, (Watau sun je). Wasa-wasa sai da aka shafe sati biyu ba ta ji daga MK ba idan kuma za ta yini tana kira ba zai dauka ba. Abin ya yi matu'kar tayar mata da hankali tun tana boyewa har abin ya fara fin karfinta, ta zama wata iri, ko abinci ba kasafai take iya ci ba. Ga Inna ba sakar mata fuska take yi ba, abin ya hade mata biyu, ta fara ramewa a tsaye. *** Bangaren Mk kuwa ba karamin zafi ya dauka da Sa'adah ba, kwana biyu ya yi a kwance yana fama da ciwon kai da wani irin zafi a cikin kirjinsa. Idan ya tuna yadda Sa'adah ta fito a gaban motar Khalil jikinta a dame sai ya ji tamkar ya shide, haushin ta yake ji ba ka'dan ba, gara ya gan ta da Alhaji Mamman akan wannan dan iskan yaron, so yake ya hakura da Sa'adah amma kunyar mahaifinta yake ji musamman yadda ya girmama lamarinsa. Sannan ya san ko giyar wake yake sha bai isa ya tunkari iyayensa maza da maganar ya fasa auren ta ba, ya rasa inda zai tsoma ransa. Yana ganin yadda kiran ta yake shigowa wayarsa ba adadi. To me za ta ce masa? Ta je su karata da wanda ta zaba. Kwanaki na ta shudewa, damuwar da Sa'adah ke ciki na sake karfafa, tsawon kwanaki ashirin ke nan MK bai dauki kiranta ba, balle kuma shi ya kira. Ranar wata Laraba da daddare suna zaune da Inna a tsakar gida amma kowa na gefensa, Yan NEPA suka kawo wuta, daidai inda Sa'adah ke zaune hasken ya fi karfi, Inna ta zuba mata ido tana kallon yadda ta lalace ta birkice. Nan da nan tausayin ta ya kama ta, sai dai ba ta nuna mata ba, amma ta kudiri aniyar yi mata sassauci. Washegari kuwa da walwala ta amsa gaisuwar Sa'adah, ta daina daure mata fuska, idan ta mata magana cikin dadin rai take amsa mata, sab'anin lokutan baya da hantara ce a tsakaninsu. Afuwar da Inna ta yi mata yasa ta samu sau'kin halin da take ciki, amma har yanzu ba ta da kuzari da walwala, Inna da kanta ta ce mata, "Idan ban manta ba na kai wata ban ji Muutar ya zo ba." Sunkuyar da kai kawai Sa'adah ta yi ta kasa cewa komai! Amma idanuwan ta sun kawo 'kwalla. Ganin yanayinta ya tabbatar mata akwai matsala a tsakaninsu ta ce, "Hala kin sallame shi saboda ba zai miki lefe ba?" Da sauri ta ce, "Haba Inna! Ni wallahi ban sake tayar da maganar ba." Cikin takaici sosai Inna ta ce, "To labarin abin da kika aikata ya same shi." Ganin hawaye ya kwace ma Sa'adah ya sa ta hadiye fa'dan da za ta fara yi mata, sai ta bige da fadin, "Kadan ke nan a cikin sakamakon da mai yin 'karya ya ke fuskanta." A ranta kuma tana raya dole su yi magana da Baffa akan rashin zuwan MK shirun ya yi yawa. Washegari Zainab ta kawo mata ziyara, suna zaune kan katifarta, "Sa'adah me yake damun ki haka?" Zainab ta fada cike da mamakin ramar da ta ga Sa'adah ta yi. Bata boye mata halin da take ciki ba, ta zayyane mata komai. Cikin takaici Zainab ta ce, "Ai indai kina biye su Safina sai sun kai ki sun baro, ka'dan ke nan." Tana kuka ta ce, "Ni yanzu ki nemo mini mafita don Allah!" "E ai yanzu da yake ta kwabe miki za ki neme ni, amma lokacin da kika bi su ai ban sani ba." Waya ta mi'ka wa Sa'adah tana fadin, "Saka lambar Uncle Mukhtar din mu kira shi da layina." Jikinta na rawa ta karba ta hau jera zababbun lambobinsa, tana fatan Allah ya sa ya dauka tunda har layinta da bai san da shi ba ta sha 'kiran ba ya 'dagawa. Cikin Sa'a kuwa ya dauka! Zainab ta gaishe shi, ya tambayi wacece? Ta amsa da gabatar da kanta, sai ta shiga ba shi ha'kuri a madadin Sa'adah, ya yi shiru har ta gama. Ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce, "Ba dan ina ganin hankalinki ba da ba zan saurare ki ba. Ki yi hakuri, ki cire kanki a cikin wannan maganar, ba zan iya da halin yarinyar nan ba, duk yadda nake zaton ta ta wuce nan". Yana fadin haka ya katse wayarsa. Bugun da zuciyarta take yi ya sake tsananta, a rikice ta ce "Zainab mai yake nufi? Ya fasa yi da ni ke nan?" Cikin son ta kwantar mata da hankali ta ce, "Ba fasawa zai yi da ke ba In Sha Allah! Kawai ya yi fishi ne sosai, ai kema kin san ba ki kyauta masa ba." Ta dade tana kwantar mata da hankali, kafin ta mata sallama ta tafi da al'kawarin za ta sake tuntunbar sa. Kwanaki biyu da zuwan Zainab, Anty Sumayya ta yi waya Sa'adah ta je ta karbo mata sa'ko a karkasara gidan kawarta. Akan dole Inna ta barta ta fita bayan ta sha jan kunne da nasiha iri-iri akan kar ta biya ko ina, har kunya ta

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});