Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 91

Chapter 91

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da Inna sai ta tambayi kanta yaushe za ta fara dariya ne ita?. Yanayin da ta ke ciki ya fi kama da na mai takabar da mutuwar managarcin miji ya zo mata kwatsam. Daidai wannan lokacin Sumayya ta iso Kano dan jajantawa yar'uwarta halin da tsinci kanta a ciki. Halin da tarar da Iyah a ciki ya bala'in girgiza ta. Cike da tausayawa tace " Na sha fada miki halin da kika jefa kanki ba inda zai kai sai nadama, gashi tun ba a je ko ina ba, kina fuskantar Halin Yau! duk wadannan kawayen na ki da kika mayar allon kwaikwayon ki YAU suna Ina?" Karon farko da Sa'adah ta fara jin sassauci domin sai a ranar ta Sami wadda ya mata fa'da, iyayen ta sun zuba mata ido, ba wadda ya buda baki ya mata fa'da, sun mata dungu suna gasa ta da idanuwan su kawai, hatta Baffah da ta tabbatar ba abin da yake so a duniya irin ta, wannan karon ta na hango ko oho da yake yi da lamuranta. Ta ri'ke hannun Sumayya ta na wani irin kuka, tana fadin "kin fada mini, ba irin gaskiyar da ba ki fada mini ba, sai dai an riga an kadddara mini yanka kazar wahala, dole kuwa sai na figeta tas, Mukhtar mutumin kirki ne, laifin duk nawa ne, sai dai nima kadddara ce da bazan iya kauce mata ba, ki taimake ni Aunti! ki bashi ha'kuri, Tunda Baffa ya barni da kaina". Ta shide tsabar kuka! Hankalin Sumayya ya ru'banya tashi, amma hakan ta daure, ta tausasa murya ta ce " ki daina irin wannan kukan, idan har kin yi amanna kaddara ce ta hau kan ki, to ki yi hakuri ki bita da istigifari, yawan kuka da 'kauracewa abinci da takurawa zuciya ba abin da zai haifar miki sai ciwon da zai kayar da ke, ina tabbatar miki duk wadda zai shiga damuwa a dalilin rashin lafiyar ki, ke ce dai mai jin jiki?" "Na gode sosai Anty dan Allah ki 'kira shi, ko zai ga girmanki". Sumayya ta nisa ta ce "Bana jin girmana zai sa ya janye kudirinsa tunda har bai janye saboda Baffah ba". Hawaye ya kwaranyowa Sa'adah ta ce " Baffa ba ya son na koma ne, a gaban mu Mukhtar ya ce ya bashi umarnin ya mayar da ni, amma 'kememe Baffa ya 'ki, ya barni na ji da dabarata". Sumayya ta yi shiru, tana jin tausayin 'kanwarta na sake kamata, ba ta gane muhimmancin mijinta ba sai da ya kubuce mata, ta tuna wani lokaci da ya shude tana mata fadan ta bi mijinta su zauna lafiya. Ta nisa ta sake tuno amsar da Sa'adah ta bata a waccan lokacin, "Anty ki ta cemin na bishi, na masa biyayya ko da yana cutar da ni, akan me zan yi irin wannan rayuwar auren alhalin ko yau Mukhtar ya barni Ina da yakinin zan samu wadda ya fi shi." Ta dago ta kalle ta, yau Mukhtar ya barta, da ya tashi barin nata ba shi kadai ya tafi ba, sai da ya yi awon gaba da dukkan nutsuwa da walwalarta, bugu da 'kari hatta kyaun da ya sa take ta'kamar zata samu wadda ya fi shi, ya tsiyaye tas, ta kai duba ga kirjinta , ta ga sun yamushe a cikin riga, mamaki ya kama Sumayya bata taba sanin nonon Iyah zai iya zubewa haka ba, domin ko da take shayarwa a tsaye kuma a cike suke, irin wadda suke ma'kale ne a kirjin mace, amma tashin hankalin da take ciki suma ya tabasu, hakanan gashin kanta sai saukewa yake yi, ga uwar rama sai ido gwara gwara tamkar idon agolan Banufe. Ta ke Sumayya ta dinga neman tsari da shiga tashin hankali kwatankwacin irin wadda Iyah ke fuskanta, ta kuma nemawa yar'uwarta samun sassauci da mafita. A hankali ta ce "zan 'kira shi, sai zuwa dare tunda yanzu yana gurin aiki, fatana dai ki kwantar da hankalin ki, ki karbi kaddarar ki da hannu biyu, yanzu a ina Jawad ya ke?" " Ni ma ban sani ba" Sa'adah ta fada a sanyaye. A daren ranar kuwa Sumayya ta 'kira layin Mk, da girmamawa ya amsa wayarta, suka gaisa, ta fara da tambayar Jawad, ya amsa da yana nan lafiya Lau, shima ya tambayi nata iyalan, da 'kyar Sumayya ta iya masa maganar Iyah, ga mamakinta sai taji ba alamun zafafawa, ya ce "Anty ku bimu da addu'a da ga ni har Sa'adatu abin ya zo mana a ba zata, muna bu'katar mu nutsu, zuwa gaba muga me ubangiji zai zartar mana, har yau ina sonta, Ina fatan mu sake zama, sai dai muna bu'katar hutu da nutsuwa, idan dukkan mu mun fahimci manufar auren, zamu dawo mu sake zama abu guda, amma for now, ya kamata mu bar komai a hannun mai juya al'amuransa ya mana zabi". Sumayya ta amsa da "Hakane" tare da yi masa godiyar amsa 'kiranta da ya yi, ta rufe maganar da ro'kon ya kawo mata Jawad yaranta suna ta tambayar shi. Ya amsa da gobe juma'ah zai kawo shi ya yi week end tare da su". Ta ajiye wayar, tana kallon Sa'adah da ta yi mata 'kuri tana son jin abin da ya ce. Kasancewar Sumayya na cikin jerin mutanan da basa yiwa 'karya kwaskwarima dan su da'dawa wani, kai tsaye ta ce "Iyah ki barwa Allah zabi kin ji, idan zaman ku bai 'kare ba, za ki koma dakin ki, idan kuwa iya adadin da aka deba muku za ku yi kenan, ina tabbatar miki ba za ki koma ba, hakan kuma ba shine 'karshen farin ciki ba". Kuka sosai Sa'adah ta yi a wannan daren, kafin ta tashi ta 'doro alwallah ta fara sallar nafila, idan ta na addua a fili take fadin " Allah ka rufa min asiri, ka mayar da ni 'dakina, Allah na tuba". Sumayya kawai kallon ta take tana sake jin tsoron ubangiji na kamata, yau Iyah ke wannan haukan akan Mk, Ashe duk wani kau'di da ginshirar da take yi shine kanta ya dawa? Ko yau Mk ya mayar da ita, ta yi amanna ya karya duk wata fuffukar da take ji da ita, za kuma ta nutsu ta daina fitinarsa, tun lokacin da ta haihu amma ya iya hana ta zuwa ta dubo ta, ta tabbatar Sa'adah ta fara kai shi bango ne, ta kuma koya masa rashin kirki. Washagari kuwa ya kawo Jawad har kofar gidan Baffa da 'yar karamar jakar kayansa da kuma ledar biskit da alawowi ga su Ayman. Da gudu ya shiga cikin gidan! Mk na tsaye yana jin rashin dadi, yana son ya shiga ya gaida Inna, amma kunya ya ke ji, hakanan ya ke ganin rashin kyauta wa idan har bai shigan ba, saboda ya saba duk sadda ya kawo shi zai shiga su gaisa sannan ya tafi, haka idan zai dauke shi. Har ya juya sai kuma ya dawo ya shiga, ya dade a tsaye a zauren, yana tuna moments dinsa da Sa'adah a cikinsa. Dukkansu suna tsakar gidan Suka ga Jawad ya shigo a guje, suka rungume juna da Ayman 'din Sumayya, duk da Ayman din ya bashi shekaru biyu, amma abota suke yi sosai. Inna ta tashi ta

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});