Chapter 78
Chapter 78
arewa da Nigeria gaba'daya. Lafiya Lau suka dawo kano, a gidan su Mk suka fara tsayawa suka ci abinci, Hajiya sai Ina ka saka ta ke yi da su, mussaman ta dinga murnar yadda ta ga Sa'adah ta yi kiba ta yi kyau alamun ba ta da matsala. A lokacin Sa'adah ta ga freezer Hajiya irin ta su ce, da alamun tare ya siyo musu, sai cinikin kankara da pure water take yi kuwa. Ta gabatar musu da abinci wadda shinkafa da wake ne, da miya sai salad, yayin da Sa'a tace da mai da yaji take sha'awar ci, da hanzari Hajiya tace duk Ina da su, ta fice cikin sauri tana ayyana Allah ya sa ciki ne da ita. Ta dawo ta ajiye mata tana cewa " jiya Mahmoud ya kawo mini Jawad, ku shiryawa darunsa dan yace ba ruwansa sa da ku, tunda kuka gudu kuka barshi shi ka'dai. Suka zube mata doya da dankalin turawa da tuffa, sannan suka tafi, ga mamakin Sa'adah sai ta ga ya sauka kan titi ya fada layin unguwar su, farin cikinta ya kasa boyuwa ta ce "Na gode Malam ". Tare suka shiga gidan suka gaisa da su Baffa da yake yana gida yana fama da mura, sun dan jima tare da Baffa sannan ya fice dan dubo shagonsa. Hira sosai Sa'adah suka sha a lokacin kuma ta ga gyaran da aka yiwa gidan nasu. Baffa ya kalleta yace "Iyah Dan Allah ki dinga yiwa mijinki biyayya, ki kyautata masa, ki zauna da kowa nasa bisa karamci, ki ga yadda Gidan nan ya dawo duk aikinsa ne, Ni kam ba abin da zaki mini ki sanya ni farin ciki irin ki zauna da mijinki lafiya da kyautatawa, mazajenku suna wanke mini takaicin rashin haihuwar Namiji, ba abin da zance musu sai dai Àllah ya yiwa nemansu albarka ya shirya musu zuri'a". Inna ta amsa masa da "Ameen ameen". Suna cikin haka almajirai suka shigo da doya da dankali. Mk da Sa'adah sun sha albarka da nema musu tsarin shaidan da makiya. Da zata tafi Baffa ya ce "kice da mijinki ranar juma'ah ya taho mini da Jawad na kwana biyu ban ganshi ba, kewarsa da ta surutunsa ne suka sukurkutani ba mura ba". Dariyar jin dadi ta yi tare da cewa "Zan fada masa kuwa Baffa". Ranar wata alhamis ta ce ya kaita asibiti ta cire abin tsarin iyalin da ke jikinta, da kansa ya ce ta bari suga ko tafiyar za ta yiwu, sai ta cire a can. Sosai suke zaman lafiya, saboda Sa'adah ta daina zungurar rigima, shi kuma yana kaf kaf da farin cikin ta. A haka har suka kwashi wattanni biyar. Rannann ya dauketa suka je filinsa da ake ta aiki, ya dinga nuna mata yadda fasalin ginin zai kasance, amma bata fahimci komai ba. Sai da suka dawo ya dako littafin zanen gidan ya nuna mata, ta yi muranr ganin katafaren gidan da zai zama mallakinsu, sai dai ta kalubalanci ta yaya kafar bene zata zama biyu?. "Ke kika ce kafar bene a falo kike so? wannan kuma ta baya ne sai kin shiga corridor sai ki ga kafar benen, idan Ina sama, kina da bakin ki, zan fita ta bayan, ko kuma idan Ina tare da bakina baki da matsalar komai, bari a gama, na tabbatar zai burge ki. Ta tura baki gaba ta ce"Na ga sama ma katon falo ne ga dakunan barci tamkar na 'kasa sannan har da kicin, ko dai na Amarya ne?" Ta fada tana matso 'kwalla, ya wurgar da littafin, ya ru'ko ta jikinsa ya ce, "Ke ce uwargida kuma amarya ta, da gaske nake kin cike mini gurbin mata hudu, ki daina wasiwasi akan maganata, ko an kaddara mini zan 'kara aure ina tabbatar miki, ba zan hada ki da kowa a gidan ba, daga ke sai yaranki ki yi yadda kike so". "Ban cike gurbin mata hudun ba kenan?" "Oh Sa'adah! kin zarta mata hudu ma, kawai ban son na miki al'kawarin da za'a jarrabe ni da rashin cikawa ne, kinsan bamu muke tsarawa kanmu rayuwa ba, idan haka ne kuwa bai kamata mu yi katsalandan akan goben mu ba, Ina tabbatar miki a burina ke kadai kin isheni rayuwa, sannan har yau ban taba jin son wata a zuciyata da ya kai matsayin da zan aurota ba". Ta lafe a kirjinsa tana jin dadin yadda ya ke rawar jiki idan za ta botsare masa. Kudin da Mk ya samu sun yi albarka kwarai da gaske, ya fadada shagon askin sa, ya sake budewa Ahamad wani shagon, hatta gidan da suke ciki ya sha gyara na mussaman, ya sakewa falonsu kujeru da sauran abubuwan more rayuwa da ya dace da ra'ayin gimbiya Sa'adah.ya kuma biya kudin aikin Hajj. Sa'a kam ba a maganar yadda take lasar kudi har gold ya sai mata, waya ce dai bai siyi wacce take so ba, amma ya bata waccan da ta raina da kuma ainihin tata da ya karbe. Baba Isa da su Baba umaru duk Sun Sami tagomashin inconclusive, duk da dai dama akai akai yana waiwaryasu da abin da zai iya na Alheri da neman albarkar su. Shigowar what'sapp ya taimaka wurin tabarbarewar tarbiya, a farkon shigowar sa ya rudi mutane da yawa mussaman Mata dan hatta abinci sai andauka an dora a WhatsApp, gida mai kyau kuwa kullum cikin tallansa ake yi. Ya zama ba sirri, mussaman idan mace tana cikin wadata ta hanyar status take bayyana matsayin ta, hakan ya sake jefa Sa'adah cikin buri sosai kullum cikin kara son kayan garari ta ke . Sannu a hankali aka fara bude groups daban daban ciki har da na tsofaffin dalibai, babbar mastalar group din su Sa'adah hade yake da mazan set dinsu tunda makaranta tasu hadaka ce da maza. A haka Khalil ya samu numban ta, suke gaisawa lokaci zuwa lokaci, duk da baya nan yana Egpt yana karantar sociology. Ta hanyar what's app ya mallaki hotunanta dana Jawad, idan ta yi status zai yi saving, ba a karan kanta ta ke tura masa ba. Haka Kuma taron tsofaffin dalibai (reunion) sai ya zama ruwan dare, ko Ina taron tsofaffin dalibai ba 'kak'kautawa. A wannan lokacin FGC Kano ta shirya nata tunda ga kan daliban farko har zuwa daliban da suka kammala a shekarar taron. Taron ya kai taro, mafiya yawa daliban ma'aikatane ko manyan Yan kasuwa' har tsoffin Malaman duk sun halarta, dan haka Mk ma ya je, manyan mata masu aji, wadda suka yi wanka da ilimi da gogewar rayuwa duk sun kewaye harabar makaranta. Sai farin ciki ake yi, mafiya yawa kuma cikin shiga ta alfarma suke, Sa'adah na cikin jerin da basu da makusa tun daga kan suturarta har zuwa fatar jikinta, kawai na'kasun ta 'daya ba a motar kanta ta je gurin ba, bata ji muzanci ba, sai da Mk yace mata zai tafi idan sun kammala ta wuce gidan Inna zai 'dauketa acan. Kusan 'Yan set dinsu kowa da mota ta je har 'yanmatan cikinsu, Halima a motar Safina suka je, motar da Sa'adah taga Farida a ciki ta matu'kar tsaya mata a rai. Hira ake ta yi, ana zuga wadda rayuwar su ta yi nasara ta hanyar kambaba lamarinsu, wasu kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157