Chapter 89
Chapter 89
kun mayar masa da 'ya Bazawara? kaico na taya ku jin kunya". "Yanzu ku tashi ku kaini gurin Alh Isa". Sai da Mahmoud ya taimakawa Mk sannan ya mike. Fada sosai Mk ya sha a gurin Alh Isa, sai daga karshe ya sassauta ya ce " Ka yi kyan kai da ka yi saki 'daya tal, fatana ka janye ka mayar da matarka, kowa hakuri ya ke yi da abokin zamansa ,ta ci darajar mahaifinta". Kan Mk na kasa baice komai ba sai da Baban ya kammala sannan cikin ladabi ya ce "A mini afuwa Baba, a yi hakuri, a sani cikin addu'a ina cikin ru'dani mai yawa, ina rantsuwa da ubangiji ina cikin ru'danin da nake jin inama ajalina ya riske ni a yau saboda tsananin asarar da nake jin na tafka, ba yadda zan yi ne, abin ne ya fi 'karfina" Dukkansu jikinsu ya yi sanyi mussaman yadda yake maganar cikin rawar murya tamkar ba Mukhtar ba, namiji mai karfin zuciya. "Allah ya daidaita ya kawo mafita " cewar Alh Isa da ya rasa mai zaice, dan ya lura Mukhtar na cikin rashin nutsuwa da firgici, ya tabbatar kuma yana da gaskiya, sannan mai 'daki shi yasan inda yake masa yoyo. Dukkansu suka amsa da "Ameen, ya yin da Hajiya ba haka ta so ba, so ta yi ya wula'kanta mata shi, ya kuma tirsasa masa ya mayar da matarsa ko ba ya so. Har da Alh Isa suka 'dunguma zuwa gidan su Sa'a, Hajiya ce kawai ta ce ba zata je ba, bata san da idon da za ta kalle su ba. A tsakar gidan Baffa ya jagorancin zaman, Alh Isa ne ya yi karfin halin bayyana mutuwar auren wadda ya matu'kar dukan zuciyar iyayen na Sa'adah, juyin duniya ba wadda ba'a yi musu ba, amma sun 'ki bayyana menene dalilin da ya haifar da wannan tashin hankalin, kukan da Sa'a ke yi tamkar za ta shi'de ya sake 'daga hankalinsu. A hankali Mk ya ce "Baffa Ina rokon ka, kar yanke mini kauna, ka yafe mini, kaddarar muce ta zo da hakan, har wayewar garin YAU bamu san zamu tsinci kanmu a cikin wannan mawuyacin HALIN da muke ciki ba, ina kuma fatan itama ka yafe mata, ba laifinta bane Baffah". Gurin ya yi tsit sai shshshekar kukanta kawai ake ji, Mahmoud ya kamu da ciwon tausayin masoyan biyu, mussaman Sa'a kallo daya za ka mata kasan tana cikin tsaka mai wuya. Baffa ya nisa ya ce "Ba aurenta ne ya hadamu ba Mutari, ba kuma zai zama dalilin rabuwarmu ba, nasan halin girma irin naka, tsiyar a gunta take, yanzu kuma zata gane tsiyar har wasali gareta, domin na tabbatar laifin nata ne, ba zata 'ki zaman aure ta yi tunanin zata zauna a gabana ba". Ga mamakin Mk sai ya ji kalaman Baffa sun sake girgiza masa zuciya. Da sauri ya mi'ke ya koma kusa da shi ya ce "Baffa Dan Allah dan Annabi ka yi ha'kuri, idan ka yi haka bazan yafewa kaina ba, ka yiwa Allah ka barta ta ji da tashin hankalin da na jefata, ba laifin ta bane, nawa ne, Ni za ka hukunta ba ita ba". Ido kawai Baffah ya zubawa Mk da yake gurfane a gabansa yana rokonsa idansa jawur, ga wata irin rama da ya yi ta farat daya. A ransa fadi yake Iyah kin tafka asara, kubucewar miji irin Mutari abin ki shimfi'da tabarma azo a miki jaje ne. Ya tabbatar laifin na Iyah ne, amma ya 'boye laifinta, ya kuma tsaya kai da fata wurin nema mata sassauci da aminci a gurinsu. Baffa ya dafa kan Mk ya ce " Madallah da mutanan kirki irin ka, madallah da mutane masu irin dabi'ar ka, madallah da zuciya mai adalci irin ta ka! Saboda kai zan bar Iyah ta zauna a gidan nan, ban taba jin takaicin rashin ya'ya da yawa ba sai yau, da ace Ina da wata 'yar! da wallahi taron nan bazai watse ba sai na musanya maka da ita". Kwalla ta 'kwacewa Mk ya na jin kunya da tausayin Baffa na sake masa rubdugu, wacce irin kauna ya ke masa haka, anya bai yi rashin kirki da ya kasa yin ha'kuri da 'yarsa ba?" Ba zato suka ji Mk na cewa "Baffa me yasa ba zaka ba ni umarni na mayar da ita ba, sai ka yi fatan ka bani yar'uwarta idan hakan ya yiyu ka haramta mini ita gaba'daya fa?". Ba ki 'daya jikinsu ya dan yi karfi saboda kalaman Mk, wadda suke bushara da zai iya daidaitawa da matarsa, yanzu ko anjima. Inna ta ce "Tunda baka da wata da za ka bashi, ai sai ka mayar masa da wadda ka ke da itan". Cikin kuka sosai Sa'adah ta ce " Na gode Innah". *Surayya Dee* ✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *Gaisuwa da fatan alheri ga wadannan groups din* *LAFAZEE FANS* *DANDALIN MUM KHADY* *HAFSAT SODANGI fans* *DAGA DAJI 1&2 fans* *PAID GROUP na BINTA ABBALE* *DANDALIN SADA ZUMUNTA NA ANNURI.* *JIDDA REAL FANS* *FADILA LAMIDO FANS* *SADNAF NOVELS GROUP* *TASKAR AISHA MICHIKA* _*Dama sauran wadanda ban ambato ba, mu hadu a shafin gaba, Kuna da yawa Allah ya bar kauna_*. *MK, SA'A DA FARIDA NA GAISUWA* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 79_80. "Ba zan ba ka umarnin da na san kunya da nauyi ne zaisa ka yi shi ba. Ba ni na maka umarni ka auri Iyah ba, ku ka hada kanku, ka aureta bisa ra'din kanka, ka zauna da ita cikin shekaru bakwai, Ni da mahaifiyarta shaida ne akan kyakkawan rikon da ka mata, haka nan, ka na girmama mu da dukkan zuciyarka, kana jin nauyi na tun kafin na baka aurenta, idan har za ka iya sakin Iyah, to ni kuwa bazan yi son zuciya ba, na tabbatar abin ne ya fi 'karfin ka". Ya nisa ya cigaba da cewa "Zan so kwarai ace na mutu na barta a hannun ka, domin Ina da yakinin ba za ta wulakanta ba, amma ya na iya da HALIN 'dan YAU mai yin aiki da son zuciya, daga baya kuma ya jinginawa tsautsayi da 'kaddara". Alh Isa ya muskuta ya ce "Tun kafin mu zo nan, na umarceka da ka janye, ka mini gardama, amma yanzu kana cewa ya baka umarni ka mayar da ita, Ni baka jin nauyi na Mukhtar?" Kunya iri iri ta sake rufarwa tashin hankalin da Mk ya ke ciki, a sanyaye ya ce " A a Baba bayan nauyin ka da nake ji, wallahi kallon uban da ya isa ya zartar da hukunci akai na na ke maka! Abin da yasa ban amsa ba, ina jin tsoron kada na mayar da ita a yanzu auren ya lalace gaba daya, saboda zuciyoyin mu cike suke da bacin rai mai ya.." Cikin dimaucewa Sa'adah ta katse shi da cewa "Ni zuciyata ba komai sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157