Chapter 73
Chapter 73
cigaba da aikinsa amma bashi da sukuni ko kadan, ya kuma yi al'kawarin ba zai ce ta daina kukan da take yi ba. Aikuwa kusan raba dare ta yi, tana masa gunjin kukan da babu shagwaba, sai zallar bacin rai, irin kukan da me yinsa yake son a rarrashe shi, lura da hakan da yayi shikuma ya yi biris da ita, dan kuwa bai ga dalilin kukanta ba, shi ta musganawa, ta masa rashin kunya, bata bashi hakuri ba, shine take sa ran shi ya risina mata, lokaci ya yi da zai daina biyewa son zuciyar sa akan lamarin ta. A inda take zaune barci ya sureta, sai sakin ajiyar take yi. Sai da ya gama aikinsa, ya kammala komai, ya dauko Jawad ya kwantar da shi, ya dauko bargo ya lulluba mata, sannan ya kashe fitila ya kwanta bayan ya rungumo Jawad a jikinsa. Da asuba ta tashi ta ganta lullube da bargo, ta ji dadi, sai dai rashin tashinta ta yi sallah ya dakushe waccan jin dadin, ta kalleshi har ya dawo daga masallaci, ta zuba masa idon da ya kumbura saboda kuka, murya a dashe tace "Malam abin har ya gagareka tashina na yi sallah?" Ya yi mata shiru tamkar ba da shi take yi ba. Takaicinsa ya sake kumeta, tace "Ma'aiki dai yace Allah ya jikan mijin da ya tashi cikin dare ya kuma tashi iyalinsa suka yi sallar nafila, to ina kuma ga wadda ya tashi, ya kuma tashi iyalinsa dan sallar Farillah? ka rasa wannan ladan, ba nice da asara ba". Ya zuba mata ido yana kallon ta, Yana jin sabon tashin hankali na shigarsa, tabbas ta kerewa tunaninsa, an mata famfo fiye da duk yadda yake zato. Haka ta gama sakin magaganu sannan ta fita zuwa dakinta, don yin sallah. Kan Mk ya kulle, ya rasa mai zai mata, ya yi fushin, ya bagarar da ita, Amma duk a banza, wai ya zai mata ne? kawai sai ya tsinci kansa da daga hannunsa sama yana cewa "Allah kasan irin son da nake yiwa Sa'adah, Allah ka shirya min ita, ka bude kirjinta ta gane gaskiya, ta fahimci bani da nufin zaluntarta, ka zaunar da mu lafiya, Allah ka kara min ha'kurin zama da ita cikin adalci". Ya kishingida yana tunano kafin shigowar su Halima cikin rayuwar aurensu, ko ya ya taga ya canja mata, ta dinga tambayar me ya same shi, ko itace ta masa laifi? Ta dinga bashi hakuri kenan, ko yace bata masa komai ba, kawai yanayi ne, ko baya jin dadi ne, duk da haka hankalin ta baya kwanciya sai ya dawo da walwalarsa, amma a yanzu kusan sati uku suna dauki ba dadi, amma kullum da abin da zata yi da zai sake bakanta masa Rai, karon farko da ya fara zargin Anya kuwa dama Sa'adah da gaske tana sonsa? Ya dinga hasaso yadda yake gudun zuciyarta, har wasu da yawa suna ganin tsoronta yake ji, alhalin ba haka bane, kawai tsananin sonta da yake yi ne, yasa baya shiri da duk abin da zaisa ta koka, mussaman na rashin wani abu, zai ha'kura da dukkan bukatun kansa, matu'kar ita zata wadatu. Amma duk su Safina sun lalata mata tunani, sun jefa mata shubuha, wai yan mata ne da shi na banza! Tabbas suna neman raba shi da ita ne. A fili ya furta " Allah kana ganin masu son shiga tsakanin aure, Allah ka min maganinsu". Sai da ya isa makaranta! Ya na cikin motarsa ya ciro wayarsa, ya lalubo lambar Anty Sumayya, cike da girmamawa ya gaisheta, sai kuma ya yi shiru ya na jin nauyin zartar da kudiransa. Jin yanayinsa yasa ta tambayarsa ko akwai matsala ne? Cikin jin nauyi ainun yace " So nake ki yiwa Sa'adah magana, mun dade cikin rashin nutsuwa, na yi iyakacin kokarina dan mu fahimci juna abin yaci tura, bana son na tayarwa da su Baffah hankali". Hakuri Sumayya ta dinga bashi, tare da al'kawarin yanzun nan zata kirata. Kai tsaye yace "ba waya a hannun ta". Jikin Sumayya ya sake mutuwa, shiyasa kwana da kwanaki tana gwada layin Iyah baya shiga, ta damu kwarai da rashin jinta, sai da Inna tace mata, lafiya ce take buya, Ni kaina an kwana biyu bamu gaisa ba, da kuma wata matsalar ce ai da mun ji, tunda mijinta kusan kullum sai yazo unguwar, kowacce juma'ah kuma zai shigo ya gaishe ni, ya bar Jawad sai zai tafi ya zo ya dauke shi, na fahimci Iyah! indai naji ta shiru haka, to cikine da ita. "Yanzu kana gida ne?" Ya girgiza kansa tamkar tana ganinsa "Ina makaranta, sai da yamma zan koma". Ai kuwa da yamma yan isa gida ba jimawa, Kiran Sumayya ya fado wayarsa, bai dauka ba, ya bawa Jawad wayar tare da cewa" sauri ka kai mata, Maman Gombe ce" dake tuni sun bar Jos tun shekaru biyu da suka wuce. Da gudu kuwa Jawad ya fita sai dai kafin ya isa inda take ya danna ok, ya fara yiwa Sumayya surutu, ita kuma ta biye shi, duk da ba komai take fahimta a hirar tasa ba. Fada sosai Sumayya ta yiwa Sa'adah, ta yi shiru tamkar tana jinta, sai da ta gama ta saka mata kuka tana fadin "Yana zaune da yan'uwansa kalau, amma ni yana ba'kin ciki da hadin kan dake tsakanina da ke, Ina zaune da shi ne kawai, amma ba irin wulakancin da baya mini, ya fifita farin cikin yan matansa akaina, ya koyo wata dabiar da ba tasa ba, ko kukan jini zai ga inayi ba ruwansa, shine har ya kawo karata?". Mamaki ya kama Sumayya tace "Ni kike fadawa wadannan maganganun? Eh na tabbatar Mijinki ba karamin ha'kuri yake da kaifin harshen ki ba, amma ki saurare ni da kyau, wlh idan baki canja ba, za ki jefa kanki a nadama mai yawa, wato ke har yanzu baza ki yi hankali ba? Kowacce mace da akwai inda take ha'kuri, ance miki auren wasa ne, ke naki ma wallahi ba matsala bace, kawai dorawa kanki kika yi, Ina ruwan ki da yanmatansa, ko aure yace zai kara Ina ruwan ki? Tun zuwan ku Jos na lura sai kin koya masa bagarar da lamarin ki". "Dan ke mijinki ba mai hayaniya bane, ba mai kule kulen mata bane shiyasa kike ganin bani da matsala" Sa'adah ta fada a tunzure. Cikin bacin rai sosai Sumayya ta ce "shikenan ki yi duk abin da kike so, ya dauka ina da wata kima a wurin ki! shiyasa yake ganin zan iya muku sulhu basai iyayen mu ba, amma tunda ban isa ba shikenan! Rayuwarki ce, kina da ikon yin duk yadda kika so, sai dai ki sani wadda bai ji bari ba, ba zai ki ganin hoho ba". daga haka ta kashe wayar ta, ta bar Sa'adah ri'ke da waya tana kunshekin kuka. Jikinta ya yi sanyi, tana Jin Aunty Sumayya uwace ta wuce ta yi misayar yawu da ita! Dan haka sai ta sake kira, Sumayya ta daga tana cewa "menene?" Cikin kuka Sa'adah tace "Na ji! kiyi ha'kuri". Sumayya da bata da zafi, tace "yauwa Iyata, ni nasan indai a cikin Innarmu kika fito ba zaki 'ki jin abin da na fa'da miki ba, saboda kinsan nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157