Chapter 72
Chapter 72
masu juyawa matansu baya idan sun sami biyan bu'katar su" Ya zuba mata ido yana jin wani iri Abu mai kama da tsanar ta na son yiwa zuciyar sa dirar mikiya. Ya nuna kansa da yatsansa, yace "Ni ki ka zaga?" Idonsa ya kada ya yi jawur, ya rasa inda zaisa ransa ya sami sau'kin zafin da zuciyar sa ke yi. Ya girgiza kai yace " Na gode, amma U will pay for it Sa'adatu".ya juya ya fice da sauri. Ganin yanayinsa yasa ta jin nadama na dan shigarta mussaman yadda ya nuna kansa yana tambayar shi ta zaga? tasan bai taba zaton zata iya zaginsa ba, ita kuma ba'kin cikinsa ne yake neman kashe ta a tsaye, sannan ma a ina ta zage shi? Fishi ya dauka sosai, sun kai sati a haka, abin ya fara fin 'karfin ta, rama take yi a tsaye, ko uffan baya cemata, Idan yana gida Jawad na manne da shi yana bashi labarin yaci abu kaza da iri kaza, ko yace su Anty Safina sun kawo masa abu kaza. Hankalin ta bai tashi sosai ba, sai da yayi shopping, taga iya abin da ya zama dole ya siyo, wadda ya saba siya na kyautatawa duk bai siyo ba, duk wani tarkacen kayan kwa'dayi babu a siyayyar nan, hatta kayan miya da yake zuwa janguza ya lodo musu, wannan karan ko guda daya bai siyo ba. Sannan a drower yake ajiye kudinsa baya mata iyaka, ya zara , ta zara, har su 'kare a haka, a wannan lokacin sai ya zauna ya yi 'kiyasin 200 zai isheta kullum da sunan kudin cefane, dan haka sai ya adana kudinsa yake bata wannan darin biyun, Jawad yake bawa ya kai mata. A wannan lokacin da ya rikice mata, ya canja sosai, sai ta gane ashe dai da kirkinsa har yawa ya yi. Ta fara neman hanyan sulhu, amma ta rasa yadda zata yi, yaki ya bata dama ko kadan, ko ta kai masa abinci baya ta'bawa haka take daukan abinta, ta fara daukan wanka da kwalliya, shikuma sai yake runtse idanuwansa daga kallonta. Ta rasa mai kuma zata yi, sai ta dawo da gyara masa dakinsa, kullum idan ya fita, zata shiga ta gyara, gyara na mussaman, ranar da ta fara, da ya dawo ya gani, a ransa yace zaki san ba ke ka'dai kika iya neman masifa da tashin hankali ba. Ganin ta debi kwanaki tana bin hanyoyin neman sulhu, amma ya yi biris da ita, sai ta canja salo. Rannan da daddare ya dawo, ta kai masa abinci da tea din da ya zame masa ka'idar sha duk dare, tana ajiyewa yace " fita da su na gode". Ta yi shiru tana kallon sa shikuma yana zaune, yana nazari a waya, amma yana jin kallon ta a jikinsa. "Dan Allah Malam ka sha shayin nan na roke'ka". Ya girgiza kai yace "Na koshi ne, ki ajiye zan sha da safe". Da murna tace "Na gode". Ta mayar kicin ta adana abincin a fridge, a gurguje ta yi wanka, ta bi dukkan jikinta ta shafa Arabians perfume masu kamshi sosai. Ta dauko rigar barci ruwan madara, mai santsi ce kuma very transparent, ta gyara gashin kanta ta shafe shi da man gashi na Kuza. ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, tabbas ko ita ta burge kanta, ta tsinci bakinta da yin tasbihi da godiya gurin ubangiji,hakika an kyautata halittar ta. Har taje falo kuma sai ta dawo, tana bin cinyoyinta da kallo, iyakacin Rigar rabin cinyarta ne, ko kusa da guiwata bata zo ba, bugu da kari, bata sa komai a kasan rigar ba. Shaidan da zuciya suka fara wasan kura da hankalinta, suna kitsa mata idan taje a haka, ta yarda itace mai laifi, bayan duk irin yadda ya nuna mata ita da babu basu da maraba. Ta tuna yadda ya shafe sama da sati biyu bai nemeta ba, shaidan ya sake tunzuro ta, yana jaddada mata irin zalamarsa akanta, idan ba wata ya samu a waje ba, yaushe zai iya jure tsawon kwanaki bai rabeta ba, tabbas mata yake bi na banza. '' Ta koma ta kwanta a gadonta, tana Jin hawaye na bin fuskarta. Sai juyi take yi, tana kallon yadda Jawad yake barcinsa cikin nutsuwa, tana jin inama itace shi, da bashi da wata matsala a duniyar sa, indai zai ci abinci, a masa wanka, a bashi sweet shikenan baisan komai na bacin Rai ba. Ta kasa barci ta zabura ta sauko daga gadon, tana jin dolensa ya fada mata mai yake nufi da ita, ya kuntata mata, ya kuma fita fishi🤔 Ta kunna fitilar dakin, ta fice ba tare da ta kashe ba, saboda Jawad . A zaune ta same shi, yana marking din exams din 'dalibai. Ya amsa sallamarta, hankalinsa na kan takardar da ke gabansa. Ganin bai 'dago ba, yasa tace "Ina son magana da kai". Yana cigaba da marking yace "Amma dai kinga aikin da ke gabana ko? Sai ki jira na kammala, ko ki tari lokacina na gaba". Hawaye ta ji na neman kwace mata, da ta tuna kafin su fara takun saka, baya iya yin aiki sosai matu'kar suna tare, ya fi kauri wurin tsokanarta, ta hanyar dumbulan kirjinta, ko ya biyeta su yi ta shiririta, tana bashi labarin ai tana yawan mafarki ta zama Hajiya, ta zama big madam, shikuma ya yi kudi, ya zama Alhaji, ya gina musu katon mansion. sai yace Ina fatan dai ba kiga na 'kara aure ba? Wani lokacin tace bata gani ba cikin da'din Rai, wani lokacin tace abin da yake ransa ne, sai ta hau bori, shikuma ya lalace wurin rarrashin ta, a haka har su cinye lokaci mai yawa basu farga ba. Amma a yau, gata a gabansa yana nuna mata bashi da lokacin saurarenta, aikin da yake yi ya fita muhimmanci kenan?. Da gaske ita da Babu 'daya ne a gurinsa? sai kawai ta fashe masa da kuka irin wadda ta tabbatar yana gigita shi. Surayya Dahiru ✍️✍️. 30/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *Surayya Dahiru*. Lafazee writers. *Doka mai lamba ta 68 ta nina cewa satar fasaha babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*. *A kiyayi ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 67-70. Ya yi shiru yana jin kukan da take masa, yana ayyana rashin mutuncin ta kullum kara gaba yake yi. ransa ya baci iyaka, mussaman yadda ta ware murya tana masa kuka tamkar wadda ya ke mata dukan kawo wu'ka. Ya kasa cewa komai, domin zuciyarsa sai fada masa take, ya daketa kawai, ko ya huce kadan cikin takaicin da take guma masa, itama kuma sai ta yi kukan mai dalili. Tsawon lokaci tana kukanta, jikinta ya yi sanyi tubus, a dalilin halin ko in kula daya ya mata, da gaske dai Malam ya gaji da ita, hakan ya sake sa ta fashe da sabon kuka fiye da wadda take yi. A harzuke ya nuna ta da yatsa yana cewa " tashi ki koma dakin ki, kici gaba da kukan a can. Idan kuma ba ki gama min tuya a gurin makwabta ba, sai ki kara himma har su shigo su ceceki." Jin hakan yasa ta rage sautin kukanta, shikuma ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157