Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ita ce mahaifiyar MK, Hajiya Rabi yaranta uku kacal, Hafsatu ce Babba, sai Mukhtar sannan auta Ahamad, da Mk ya girme masa da shekaru kusan goma Mahaifin MK mutum ne mai sau'kin kai, mai kokarin wadata iyalinsa da komai na bukatar rayuwa, dukkan su, sunyi karatu, matan dai suna kammala sakandire yake aurar da su, yayin da mazan ke zurfafa karatunsu a jami'o'i daban-daban a cikin kasar nan. Gidansu akwai zaman lafiya, duk da ba a rasa yan kananun gutsuri tsoma irin na gidan Polygamy Family, amma dai nasu da sauki ainun kasancewar iyayensu matan ba su cika samun sabani ba. Idan ma sun samu to suna bari a tsakaninsu ba tare da sun bari yaransu sun shiga rigimar da ba tasu ba. Wannan dabi'ar tasu, tasa hankalin mijinsu ya kwanta da su, inda yake musu hidima su da ya'yansu kan jiki kan karfi. Mahaifinsu a tsaye yake kan sha'anin tarbiya, sannan ya dace da mata na-gari da suke taya shi, dora yaran akan kyakkawar turba, domin kuwa duk yadda namiji ya kai da kula da tarbiyar yara in bai yi dace da mace ta-gari ba, to da wahalar gaske yaran su bi tsarinsa. Mukhtar ya fara karatunsa a kwalejin ilimi ta tarayya dake garin Bichi, bayan ya kammala sakandiren hadaka ta gwamnatin jaha (Unity Boys Karaye). Sai da ya kammala NCE, sannan ya yi JAMB ta D.E, ya yi sa'a ya samu level 200 a jami'ar Bayero, inda ya karanta harshen turanci (English Language), yana shekara ta biyu ne Allah Ya yi wa mahaifinsu rasuwa a hadarin mota ya je dauko Bilkisu a makarantar kwana, wacce tare suka rasu da Bilkin. Wannan mutuwa ta matu'kar taba ahalin wannan gidan, dole suka tattara suka ha'kura suka bi su da adduar samun rahamar Ubangiji. Haka iyayensu mata suka ci gaba da zama suna ci gaba da kula da ragowar yaran da ke gabansu wanda Sameera ce kawai ta rage ba a aurar ba sai maza su kuma suna ta karatunsu cikin nutsuwa. Da ma can suna da sana'oinsu, sai suka samu sau'kin tafiyar da gidan da kuma tallafin 'ya'yansu maza da mata, musamman MK da ya kasance shi ne babba, kuma shi ya debo kusan halin mahaifinsu, na hakuri da yawan kula da lamarin gidan. Yana da sau'kin kai ta yadda duk yan'uwanshi suna jin da'din mu'amala da shi, kafin ya fusata yana jimawa, amma fa idan ya yi fishin wuyar sauka ne da shi. Abu mafi kyau cikin halayyar MK Bichi, ma'abocin addini, mai kokarin kiyaye dokoki ne na gaske, sannan duk layin da ba gaskiya, ba za ka same shi a ciki ba. Akidar son bokon da ya taso da ita bai sa ya yi watsi da kyawawan al'adun Malam Bahaushe ba. Sannan MK ma'abocin 'kamshi ne tun yana Secondary, da kamshinsa ake gane ya zo guri, bayan haka kuma He is Frank and friendly to all. Wannan ke nan. Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍🏼✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *KAR KU BARI A BARKU A BAYA WURIN KARANTA LABARIN HAZI'KAR MARUBUCIYA*. *⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️* *Jameey yar'mutan kankia*. *Promo* *Promo* *Promo* _Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake_. *#300-sau biyu a rana* *#500 -sau ukku a rana* *#700 -sau hudu a rana* _Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316_. *MASU SON A TALLATAH MUSU HAJARSU 'KOFA A BUDE TAKE* _TUNTUBI_ 08032773332. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 32-33. Tana isa kofar gida ana kiran La'asar, sai da gabanta ya fadi saboda yadda za ta sha tuhumar inda ta tsaya har zuwa wannan lokacin a wurin mahaifiyarta. Ilai kuwa a tsakar gidan ta tarar da ita sai safa da marwa take yi, jin sallamar ta yasa ta tsaya cak, tare da zuba mata ido, amma ganin ta futu-futu kuma idanuwanta a kumbure sai ta sami sau'kin tashin hankalin da ta shiga, don ta tabbatar Iyah ba za ta iya biyawa wani wajen a haka dukun-dukun ba, amma duk da hakan sai da ta ce "A ina kika tsaya har zuwa wannan lokacin?" Fuska daure ta ce "kwanakin da na yi ban je makarantar ba shine suka ci zalina." Ajiyar zuciya Innar ta sauke sai kuma ta ce "Madalla da wannan cin zalin." Sannan ta dauki buta ta zaga ban'daki. Sa'adah daki ta yi tana tube kayanta, zuciyar ta fes ,tana tuno hirar su da MK da ya mantar da ita takaicin da ya kunsa mata a safiyar yau. Tana idar da sallah ta wanke uniform din da ya baci da 'kura sannan ta zuba abinci, kai tsaye falonsu ta shiga wanda ba komai sai leda a shimfide da labulaye, sai yar karamar talabijin kirar (sharp) a kan dan karamin tebur, kusa da mahaifiyarta ta zauna da ta ke kulla bushasshiyar kubewa. Ganin Innar ba ta 'daga kai ta kalle ta ba yasa ta fadin, "Inna ko ki tambaye ni, ko na ji ciwo a cin zalin da aka mini?" Cike da rashin kulawa ta ce "Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, tunda kin yi girman da za ki zabawa kanki abin da ya dace da ke ai magana ta 'kare" Jikinta ya mutu ta ce "Inna kin ce magana ta wuce, amma kina ta share ni kina nuna ko oho da ni" Ta ture abincin tare da fashewa da kuka. Da farko share ta ta yi, amma jin yadda take ta sauke ajiyar zuciya, ga kuma hawaye nata tsere a fuskarta, sai ji ta yi raunin da bata son ta nuna mata ya kubce mata cike da tarin soyayya irin ta uwa ta tausasa murya ta ce "Share hawayen kin san dai ba na son kukan ki ko?" Ta tura baki cike da shagwaba ta ce "Inna ai da ne ba kya son kukan nawa, yanzu sau nawa za ki ga ina kuka amma ko ki nuna kin gani bare ki rarrashe ni?" Murmushi ta yi ta ajiye ledar da take hannunta ta zuba mata ido sannan ta ce "Iya bawai kukan naki bai dame ni ba ne. Ni kadai na san yadda zuciyata ke zafi idan na gan ki cikin rashin sukuni, halayen da nake gani a tare da ke ne ba su mini ba, ina matu'kar kaduwa da yadda kike kokarin jefa kanki a rayuwar da ba za ta bulle da ke ba" Sa'adah da jikinta ya yi laushi amma sai ta yi karfin halin cewa, "Don Allah Inna wai mene ne nake yi wadda bai miki ba?". Muskutawa ta yi sannan ta ce "Iyah kin san dai ke din nan ba 'yar kowa ba ce, mu iyayenki ba wasu ba ne illa masu neman abin da asirinmu zai rufu, amma ke kina daukar ra'ayin ya'yan masu wadata, ba kya duba idan ba yawan gashinku daya ba, yawan kitson ku ba zai daidaita ba! Watanni kadan ya rage ki kammala makarantarki, kin san kuma aure za a miki amma duk saurayin da zai zo gidan nan da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});