Chapter 107
Chapter 107
mata, domin turaren da mahaifiyarta ta dinga bin duk wata ga'ba tana shafa mata na alfarma ne, takanas ake yiwa manyan matan da suka amsa sunansu a sanin duniyar kamshi. Sannan ta bata wani irin tsumi da tunda aka fara aurenta kullum sai ancika mata ciki da shi, akan Dole Farida ke Sha, saboda kasancewarta masaniyar magaganuwa bata yarda da Shan kowanne irin abu da sunan magani ba. Wannan kamshin ya sake rikita Mk yana jin tamkar wani maganadisu ke jansa ga Farida, shi ka'dai yasan yaddda ya kosa su kadaice. Duk yadda Farida ta ke da kunya ta yi iyakcin bakin kokarinta ta bashi hadin kai, duk da yadda ta ke cin kwakwa a hannunsa kasancewar ita din cikakkiyar budurwa ce ta daure ya samu nutsuwa sosai. Koda ya kammala kifa ta ya yi akan cikinsa fatar jikinsu na manne, yana jin nisha'di sosai ya dinga mata addu'a, yana gode ma ubangiji na yadda duk shine ya fara bude matan da ya aura, ya tsare kansa bai taba Zina ba, ubangijinsa kuma sai ya mutuntata shi ta hanyar bashi katangaggun mata. Zuciyarsa ta buga da ya tuno Sa'a yasan sharrin zuciya ne da yake jin tamkar tana ha'intarsa ne, amma shi da kansa yasan zai yi wahalar gaske ta aikata wannan al'amarin. Jikinsa ya dinga bari har Farida ta dinga jin barin, saboda yadda ya ke jin wani iri abu da baisan dalilinsa ba, yau gashi da Farida a cikin yanayin da Sa'adah kawai ya ta'ba tsintar kansa a ciki, ko ya take ji a dalilin aurensa yasan idan itace ta yi aure tabbas sai ya kwanta a gadon likita. A sanyaye Farida ta ce "baka da lafiya ne? jikinka na rawa fa". Murya a dashe ya ce" farin cikin yadda na same ki ne, duk son ki ne yake kidima Ni" A ransa kuma fa'di yaushe zan iya fa'da miki abin da ya kidima ni ai ya zama tamkar cin fusaka ne, gangar jikinmu a hade amma tunanina da zuciyata na wani waje daban. Ita kuma zuciyarta ta yi fari kal har tana ganin sannu a hankali zata iya mantar da shi Gogel kamar yadda Gogel din tasa ya manta da lamarinta a baya. Yini zur Mk ya yi da Farida bai yarda ya mayar da ita ba sai bayan Isha, wadda sai da ta yi kuka, domin kuwa da murje idonsa zai yi ya kwana da amaryarsa, kafin su tafi ta fahimci mabukaci ne na gaske, domin sai da ya sake yin second round ,sannan yana daukar lokaci yana abu 'daya tabbacin yana da lafiya yana kuma kula da lafiyarsa. A iya wannan awannin da suka yi sai da Farida ta dinga yiwa Iyah jajen rashin mijin da iya sarrafa mace, lalle Gogel jaruma ce da ta iya shafe wannan lokaci babu zumar da ya 'dade yana lasa mata, ita yau kadai da suka kasance da shi addu'a take yi, da neman tsarin abin da zai rabata da Mk. Fata take ta kasance da shi muddin rai, zata yi dukkan ladabi da biyayyar da zata dauwamar da ita a zuciyarsa, zata yi ha'kuri da duk wani abin da baya so koda ita tana so, matu'kar zasu samu zaman lafiya , ta kuma rayu da shi, idan har zai iya rabuwa da Gogel tsawon lokaci bai waiwaye ta ba, to ta tabbatar ita idan ta yi kuskuren da suka rabu shafeta zai yi gaba'daya. Suna tafe yana tuki yana ta mata hira da suke nuni da kololuwar jin dadin yadda ya sameta, ita kuma tana ta murmusawa alamun tana Jin dadin yabawar ta shi, a ranta tana fa'din karatu a Jami'a baya sa mace ta lalace sai idan dama lalatacciya ce. *** Har Mk ya tafi ba su hadu da Sa'adah ba, domin ko da yaje gidan ana gobe zai tafi, ya fadawa Baffah zai tafi amma nan da sati biyu su Jawad za su bishi, cikin karfin hali Baffa ya yi masa addu'a tare da fatan alheri. Inna kuwa ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar sa, tare da yi masa fatan alheri a aurensa. Ya jima a zaune bai ji Inna ta hau Kiran Iyah ba, dama ita ce take yin hakan a kokarinta na su dinga gaisawa har a samu ayi sulhu, amma wannan karon bai ji hakan ba, illah shigewa daki da Inna ta yi ta bar shi da Baffah akan tabarma. Yayin da ita kuma Sa'a tana kwance akan gado tana fama da zugin zuciya duk da dai Alhamdulillah ansamu cigaba kwarai da gaske akan kwanakin ukun da suka shude. Tana jinsa Amma sai ta ji a duniya ba halittar da bata son gani kamar Mk, tabbas ya wulakanta ta, ya tozarta mafi munin tozarci, hawaye ya dinga silalowa ta gefen kunnenta, ta dinga hasashen me ya Mata na alheri ne, me ya mata na kyautatawa wadda bai cancanci ta ji wannan tsanar da take ji akansa ba, ta gama duk lissafinta ta yi alkalanci, ta yarda a zamansu bai zalunce ta ba, ta kuma gamsu ya kyautata mata, ta kuma gasgata itace ta janyo komai. Amma kuma hukuncin da ya dauka akanta ya yi tsauri matu'ka da gaske, zargin da ya jefeta da shi ya ketare iyaka, haka nan kin mayar da ita, kafin ya sake aure tozarci ne Babba ya mata, kishi ya daure mata kirji, duk irin alheri da dawainiyar da ya mata har bayan ya rabu da ita a yanzu duk sai ya tashi a banza a idonta, tana jin ba wani alherinsa data sani da zai lullube cin mutuncin da ya mata, a kuma wannan lokacin ta yanke duk wata mu'amala da shi, tana jin idan har ta sake yiwa Mk kallon masoyi, ko kallon Rahma tabbas ta zama asararriya. Kunya sosai ta hana Mk tambayar Baffah Sa'a! Sai ya buge da sake bawa Baffah hakuri, tare da neman afuwa. Duk da a ran Baffa ba ya jin da'din yadda yake ganin Iyah adalilin Mukhtar, sai ya ce " Ba komai Mutari, har yau kuma ban kullace ka ba, kawai dai ina son ka ka daina mini kallon wannan matsalar zata lalata amincin da ke tsakanina da Kai, kallon uba kake mini, Nima kallon 'da nake yi maka, har abada mun hadu ga Jawad nan a tsakanin mu". Jikin Mk ya sake yin sanyi tunda a da cewa yake yi, idan da saura zama a tsakanin ka da Iyah da kanku zaku shirya kanku, bana ji a jikina an rabu kenaan ba, sai kuma yau ya ce ga Jawad a tsakani, kenan Baffah ya karaya ya daina jin zasu sake zama ma'aurata a tsakaninsa da Iyah. Ya dade zaune Baffa na ta yi masa nasihar ya kula da amanar yarinyar da aka bashi tunda zai dauketa ne ya kaita wata duniyar da ba ta san kowa ba sai shi, sannan ya sa ido sosai akan Jawad kar ya bari ya koyo dabi'un yahudu wal Nasar😀 Da kyar ya mike ya na kallon dakin Sa'adah da fitila a kunne tabbacin idonta biyu, ya tuna idan ya zo gidan ta dinga sintiri tsakanin dakinta da tsakar gida, ta dinga bare bare kenan, ba ita ba hatta mahaifiyarta rawar jiki take yi, ta dinga fa'din Iyah kaza, zo ki kawo masa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157