Chapter 152
Chapter 152
ya kamata ta fara tarewa, tunda itace suke tare, bai kamata ace ita zata je ta tarar da Sa'adah ba, shikuma ya yi hakan ne dan ya tabbatar da Sa'a ce uwargida ba dan wani abin ba. Amma sai ta ce "Allah ya Sanya alkhairi". Ranar laraba aka gama shirya komai na bangaren Sa'adah! duk inda tsari da haduwa wurinta ya kai, a ko ina kuwa, ba kananun kuda'de aka fitar ba. A ranar dai ta laraba Sa'a na zaune a tsakar gidansu ba hijabi a jikinta adalilin Inna ta je unguwa, ba zato ta ji sallamar Innar a tsakar gidan. Gabanta ya yanke ya fa'di, ta hau dube duben Hijabinta ashe a 'daki ta barshi. Zabura da waige-waigen da take yi ne ya ja hankalin Innah ta tsura mata ido, take ta gano abubuwa masu yawa da suka sauya a tare da Iyah. Kirjinta ya matu'kar cika, sannan ta yi fari ta 'dashe tamkar mai shafa man bleaching, sanin da Innah ta yi duk kwalliyar Sa'a bata yarda ta canja launin fatarta ba. Ta kalli fuskarta tana ganin yadda ta 'danyace, alamun dai mai shigar ciki 'karara. Dabas Innah ta zauna tana hirji. Ta jima tana kokawa da numfashi, sannan ta ce "mafarkina ne zai tabbata Iyah, ko kuwa yanzun ma mafarkin nake yi?" SURAYYA DAHIRU ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ 113-114. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *PROLOGUE*. *Masoyan FARIDA*! *Team FARIDA na so na ambato sunanku, sai na gane yawanku ba zai bari ba, Farida tana sonku, tana yaba muku, Ta ce na ce muku son so Fisabidillahi*.🥰 *MARUBUTA* *Hajiya Saliha A.A Zaria* *Hajiya Hafsat Sodangi*. *Hajiya Maimuna Beli* *Aunty Sumayya Takori*. *Hajiya Zulaihatu Sani Kagara* *SADIK ABUBAKAR*. *Fadila lami'do*. *Binta Abbale*. *Hassana 'Danlarabawa* *Maman Mama*. *Ayusha Muhd* *Kulsum Baffah Azare* *Umm Azghar*. *Gidan Iko* *Asiyah(asi beauty)* *Aisha jos* *Hafsat Bature* *Rabi'atu Shitu* *Aysha Dansabo*. *Da dukkan yan kungiyar lafazi writers da ma sauran marubuta gaba'daya* *Ina godiya sosai tare da fatan alheri.* *Allah ya 'kara Basira.* *Da* matu'kar kunya Sa'a ta ce "wanne irin mafarki kike magana Innah?" "Kul kika yi mini iya-shege Iyah! Ai kin san dai mai nake nufi, mike tsaye na ganki soasai". Ta 'ki mikewa sai 'boye jikinta da take yi. Salati sosai Inna take tana cewa Ni dama na da'de ina mamakin yadda aka yi kika sauko har kina nuna zakuwar ki akan ki tare, dan munafunci har kina cemin wai saboda ra'ayina zaki ha'kura ki tare ko ba kayan daki, ashe ke kin tare ma kawai ankara ne ban yi ba. To yanzu sai ki fa'da mini lokacin da kuka kunsa cikin dan asan ko auren na ku bai yiwu ba." Da rawar murya Sa'a ta ce haba Innah yanzu sai ki yi tunanin zan iya yin wannan ta'asar?". "To ina zan sani tunda daga ke har Muutar din ba mutunci ne da ku ba , bare kunya. Wato shiyasa kullum sai kin san yadda Kika 'kirkiro fita, ko dai da sunan zuwa gurin aiki, ko wani uzzirin da ba za'a hana ki fita ba? Oh ina zaune anmayar da ni garmaho, ko a dakin nan kuka yi abin da kuka yi?" Kuka Sa'adah ta saka, tana jin wata irin kunya tamkar ta tsaga kasa ta shige. Ta kasa magana, tana jin haushin Mk da ya janyo mata wannan muzantar a idon uwarta. Ana cikin hakan Baffah ya shigo ya ce "me ya samu uwata take kuka har da hawaye ne?" "Kukan iskanci take yi, ba dama ta yi ba dai-dai ba, ayi magana sai ta bare ja'irin bakinta ta yi kuka tamkar yarinya kankanuwa." "Me ta yi da ba zaki iya hakuri zuwa jibi ta tafi dakinta, itama hankalinta ya kwanta ba?" "Hmmm! ciki ne da ita, daga na tambayeta yaushe suka yi cikin dan asan matsayin aurensu shine take wannan gunshekin kukan tamkar na daketa ne, ke kam wallahi kin ji kunya, ba dan ni na haife ki ba, da tuni ki ba'kanta ni a idon duniya". Kunyar da Sa'a take ciki ta sake nunkuwa, dan haka ta sake 'kara sautin kukanta dan ta kawar da su daga sake kunyata ta. Aikuwa dai Baffah ya ce "To ai a hankali zaki bita, ni na gasgata Iyah ba zata kunyatamu ba, ba ta yi shashanci a 'karancin shekarunta ba bare a yanzu da ta yi hankali, na kuma shaida Mutari ba zai ha'ince ni ba". Wani irin farin-ciki ya kama Sa'adah tana gasgata Mk da ya ce Baffah Babansa ne ba nata ba. Innah bata gasgata ta ba, amma Baffah ya shaideta ba zata yi Zina ba, haka ya shaidi Mukhtar ba zai lalata masa 'yah ba. Kuma hasashen Baffah shine gaskiya. Kawai Innah mafarkin da ta yi ne, yake sata wasiwasi. Ya sassauta murya ya ce "Yi shiru ki mini bayani" Ta kasa cewa komai saboda tsananin kunyar da ta tsinci kanta a ciki. Ya juya ya fita yana cewa yanzu nan na hango shi ya zo unguwar bari na ji daga bakinsa. Ganin Baffah ya fita! Ya saka Inna cigaba da sababinta, "munafukar banza, kika dinga cika bakin ba kya sonsa, kika yaudarar da ni da cewa ba zaki tare babu kayan daki ba, ashe kina zagayewa kuna abin da ranku ya so, saboda tsananin fitina da rashin kunya" Daga ganin yadda kika aune, ansan ciki ya kwana biyu a jikinki, yo ina ganin HALIN YAU ni Salamatu!". Sa'a ba baki sai kuka. Baffah kuwa shagonsa ya 'kira Mk. Cikin nutsuwa sosai ya ce "Mutari ka ce mini jibi juma'a Iya zata tare?" Kai tsaye ya ce "Eh Baffah". Ya numfasa ya ce "yanzu na shiga gidan na ji wani irin al'amari da ban fahimice shi ba, na tarar da Iyah da gyatumarsu a halin 'bacin rai saboda ta fahimci tana da juna biyu". Mk ya mi'ke da sauri , zuciyar Baffa ta buga a tunaninsa kaduwa ya yi da jin maganar saboda ba shi da alaka da cikin. Da azama Baffah ya ce "Ina zaka? Nutsu ka saurare ni, baka da alaka da cikin da yake jikinta ne?" Ya koma ya zauna ba kunya ya ce"Haba Baffah! Ni fa zaburar da na yi, zuwa zan yi na fahimtar da Innah ta daina yi mata fa'da, Ni zata yiwa, tunda nine Babba! Domin na san kai zaka shedi ne ba zan yi lalata da jininka ba! Amma sai na ji kana tambayar ko bani da alaqa da al'amarin. Kawai ayi ha'kuri Baffah! Abin da za a kallah a samu nutsuwa matatace, na kuma shaida akan ka'ida komai ya faru". Hankali Baffah ya kwanta sosai ya ce "To Allah ya rufa asiri". Mk ya mi'ke yana cewa "Yau ba doguwar hira Baffah na ji kunya ba ka'dan ba". Murmushi Baffah ya yi tare da cewa "ja'iri da kana jin kunya da baka yi abin da ka yi ba". Ya rufe shago ya koma gidan ya tarar har lokacin Innah na zubawa Sa'a sababi da gorin ta ji kunya, ta yi ciki a gida. Ita kuma sai kuka take yi tana jin takaicin abin da Mk ya janyo mata.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157