Chapter 20
Chapter 20
na class master dinsu, a A class ya bawa Farida. A wannan karon har Sa'adatu ya bawa kyautar the most hardworking student in the class, Kamar kullum Khalil Ibrahim ke daukan 1st position, shi ya 'Kira a 'karshe bayan ya bawa Sa'a. da monicca as 2nd, da wani Abdulrashid da ya zo na uku.amma da yaje karba sai yasa left hand ya Kuma juya fuskar shi, wannan rashin 'da'a da ya nuna ya hassala Mk ya fasa bashi kyautar ya kuma hukunta shi ta hanyar sa shi, sharar school area. Tunda ga nan aka fara cece kucen son Gogel yake banda haka, ta yaya ga Halima ta zo ta hudu bai bata ba, ga na biyar, duk ya tsallake ya tafi Kan 8? asalima sai da wannan kyautar ya kawo mata matsala tsakanin ta da Khalil da kuma Halima. Na Halima kyashi ne, shikuma Khalil kishi ne, gani ya ke kawai soyayya suke yi amma ai kowa yasan yadda ya takura mata, menene dalilin gift din? alhalin akwai wadda suka fita cancanta amma bai basu ba. Kusan wannan ta'kardamar ne dalilin afkuwar soyayyar ta su dan ta dade tana jin kishinsa akan Farida bata gane kishi bane sai a wannan lokacin daya sake da ita, ya gamsu tana karatu kamar yadda ya kamata. Ranar juma'ar da akayi hutu, tana cikin ranakun da bata Mantawa cikin rayuwar ta a makaranta, a ranar ne ta nutsu ta 'kare mishi kallo na tsanaki, a lokacin da ya shigo dan ya musu bankwana sai kuma bayan hutu. Dogon saurayi mai matsakaicin jiki, ma'ana siriri ne, amma kuma bashi da rama ko kadan kai tsaye za'ace mishi fari, duk da idan irin su Farida na gun, duhunsa za'a gani, doguwar fuska mai dauke da dogon hanci, da madaidaitan idanuwa, farare tas, da zagayayyen 'karamin baki mai dauke da 'kananun ha'kora jerraru, ya kuma zagaye bakin da gemu. yanayin sa tamkar 'kani ne ga tauraron wasan kwaikwaiyon nan Yakubu muhd saboda yadda suke yanayi. sanye yake cikin shadda fara 'kal, ma'abocin tara suma, mai kuma yawan gyarata dan kullum comb din shi na aljihunsa, hular yan bautar 'kasa ya saka, kafar sa dauke da open takalmi ba'ki, hannunsa daure da agogon silver samfurin (D&G). tun kuma a lokacin yake amfani da turaren Versace,'kamshin sa na cikin abubuwan da dalibai ke magana akai. A wannan kallon da ta mishi na 'kurillah ta janyo wa kanta, domin bata dauke idon ta akan shi ba, sai da son shi ya cika zuciyar ta dam, irin son nan da yake shiga ba tare da an ankaraba, lokacin da za'a ankare din ya riga da yayi illar da ba yadda za'ayi dashi. Da kanta ta dinga cewa Madallah da 'ka'idojin musulunci, sai da akace kallon shari'a 'daya ne tak, amma ni na mishi kallon 'kwal uwar 'daka. Nasiha ya musu, akan ko a gida su dinga bitar karatunsu, su kuma zama yara masu tarbiya, ta yadda duk inda aka ga 'dalibin FGC KANO aga ya banbanta da na kowacce makaranta soboda ladabi. 'karshe ya kulle bayanin shi da lallai su kyautata wa iyayen su, su musu biyayya, su kuma taimake su akan sha'anin ayyukan gida. Ya kalli side din maza yace "wadda kuke tu'ki, ku bi a hankali kusa nutsuwa". Banda kallon shi ba abin da Sa'a keyi tana jin turancin sa tamkar Baturen da yanke wa yaren cibiya. Yana kammala wa yayi waving hannun shi alamar bye, ya fice da sauri. Basu bar class din ba sai da Safina ta yi sulhu a tsakanin Halima matazu da Sa'adatu Gogel, dan haka rabuwa suka yi ta salin alin a tsakanin su tare da al'kawarin zasu hadu a gidan su Humaira asabar din sama, bata gobe ba. Tafe suke ita da Zainab da Asiya wadda yayar Zainab din ce. kamar ance ta juya ta hango Uncle Mk da Farida a tsaye jikin wata bishiya da dukkan alamu ba a zo 'daukar ta ba, hira suke hankali kwance. Take ta ji tamkar ta mutu, zuciyarta ta daure,'kirjin ta yayi nauyi ainun, tafiya kawai take amma bata sanin inda take jefa 'kafarta. Suna tsaye a bakin gate din makarantar suna jiran abin hawa ta ga yazo ya wuce su akan mashin 'dinsa da a wancan lokacin ake mishi la'kabi da tsuntsun soyayya. Hannu ya daga musu amma sai ta juyar da fuskar ta, tayi kamar bata ganshi ba, Zainab ce kawai tayi waving 'din shi. Tana isa gida 'dakin ta, ta wuce ta fa'da kan katifarta wani kuka ya kwace mata, tayi abinta ta 'koshi kasan cewar Innar ta na wanka, daga kukan barci yayi gaba da ita, sanin da mahaifiyar ta yi na fashin salla take yasa bata tashe ta ba. Haka ta yi hutun nan su ku ku, ciwon so na wahalar da ita, a tunaninta tasan so akan khalil, Ashe ba son sa take ba, kawai shakuwa ne da kuma yadda yake mata hidima, a yanzu ne take dandana azabar soyayya, yanzu ne take jin so tun daga zuciyarta, idanuwanta, da gangar jikinta gaba'daya. Idan ta tuna Farida yake so, sai taji tamkar za ta sume. A yadda ta ji ciwon ganinsa da Farida a tsaye yana mata magana cikin walwala komi yana iya faruwa da ita idan ya kasance kullum zata na ganinsa tare da ita. Zaune ta ke tana fargaban komawar ta makaranta wani satin, a da ta dauka zullimin zuwa makaranta ya 'kare tunda yanzu ta tsira daga tozarcin Uncle Mk! ashe tsugunne bata 'kare mata ba?. Agogon bango ta kalla taga 2:30pm da sauri ta 'mike ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin lallausar atamfar quali-wax mai kalar samaniya(Skye blue)da ratsin ja, Riga da skirt ne, dinkin yayi matuqar zama a jikinta,'katon jan 'dan kunne mai round tasa, a lokacin yayin kwalliya irin ta wannan zamanin ba tazo ba, amma duk da hakan ta she'kawa fuskar ta kwallliyar da ta dace da ita. Mayafi jah ta ya fa, sumfurin(internet). ta sanya takalmi half-cover amma hills. da yar mitsitsiyar jakarsa wadda zuwanta jos ta siyo su masu Jan duhu. ta fesa turare ta fita zuwa 'dakin Inna. Inna na shirya, mi'ke wa tayi daga kishingidar da ta yi, hannun ta ri'ke da carbi tunda ta idar da sallar azahar bata tashi ba. "Yanzu Iyah ba za ki daina zabga turaren nan idan zaki fita ba? Ba kyau fa, ki kiyayi taba shari'a wallahi" A hankali tace "Allah Inna 'dan ka'dan ne, kawai 'kamshi ne dashi". "To tunda kin san yadda yake dole ne, idan zaki fita sai kin saka? Ki fa dinga jin tsoron ubangijin ki, kina kiyaaye ka'idojin shari'a". Kafin tayi magana, ta sake cewa "A gabana kika ce da Baffan ku, bayan la'asar za ku dawo, ki sani idan kika wuce wannan lokacin ba zan 'ki fada mishi ba" "In sha Allah bazan kai maghrib ba Innah" "Sannan kuma kiji tsoron Allah idan mu bama kallon ki, shi yana kallon ki. inda kika tambaya nan kawai aka lamince miki zuwa. Sai kin martaba kanki, kafin wani ya martaba ki, sannan kuma duk saurayin da ya tsayar da ke kice mishi yazo gidan ku, ya nemi izinin magana dake a wurin mahaifin ki." A sanyaya ta amsa da "Zan kiyaye Inna" Sannan ta juya ta tafi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157