Chapter 155
Chapter 155
yi, tausayin ki nake ji". Ba walwala a fuskarta ta ce "Na fahimta, sai kun dawo". Ya yi sukuri ya numfasa ya ce "Then smile". Ta tura masa baki gaba tabbacin ba maganar murmushi. Ya dara ka'dan ya ce "Akan 'dan fari kike wannan fishin, ke ko alkunya baki iya ba?" Ai kuwa nan da nan tasa hannunta ta rufe fuskarta tana fa'din"Bana so Malam " a shagwabe. Yasa hannu ya bude fusakr sai ta runtse idanuwanta tana murmushi murmurshi, kunya, kunya. Da haka ya lallaba ya tafi suka rabu k'alau. Zuwa yanzu hankalin iyaye, da dangin ma'auratan ya kwanta. Haka Mk yana iyakacin kokarinsa na kamatan adalci na gaskiya a gidansa. Amma idan ya kebe da Sa'a baya iya mallakar kansa. Ta bangaren matan nasa sun gamsu Mijjinsu ba munafikin namiji bane, sai dai kowacce tana ganin yana fifita yar'uwarta. Farida har zuciyarta ta gamsu yana yi mata adalci, amma ta san yafi son Sa'adah, Dan haka take zargin yafi walwala da kuzari ranar girkin Sa'a. Sa'adah kuwa gani take yi, Mk tsoron Farida yake yi, mussaman yadda yake tirsasa Jawad sai ya zauna a wurinta, sannan yafi fita unguwa da Farida akanta. Kawai hakuri take ta yi, dan kar ace itace babba sannan itace mai yawan korafi. A haka rannan sun je gaida Hajiyar Bichi da bata jin da'di, da kyar Mk ya shawo kan Iyah ta yarda su tafi tare, dan kuwa da tace ya tafi da Faridan ita zata je daga baya. Zuwa wannan lokacin cikinta wata bakwai, ta yi wani irin girma, fuskarta ta fara aunewa, haka baki da hanci tabbacin yadda cikin Jawad ya mayar da ita haka ma wannan zai yi mata. Farida ta yi matu'kar mamakin yadda ta ga Sa'adah da tsohon ciki, tunda ba kasafai suke haduwa ba. Wani irin kishi ya shaketa, amma sai ta yi ta addu'a tana namen tsari da yin jayayya a hukuncin Ubangiji. Kai tsaye Sa'a bayan mota ta shiga, matu'kar zasu fita tare dukkansu, ta sallamawa Farida gaban mota, wanda hakan na matu'kar yiwa Mk da'di. Duk yadda take boyen cikin sai da Hajiya ta gane Sa'a ta kusa sauka tabbacin da ciki ta tare, tunda basu cika wata hudu da tariyar ba. Sun dawo gida, maimakon Farida tabi Mk zuwa side dinta, sai kawai ta bi Sa'adah akan ta baata dambun da ta yi, tunda ta ga ta kaiwa Hajiya. Suka shiga, kamshin wurin yana matu'kar birge Farida amma ba zata iya tambayar wanne irin spices ne mai bada wannan kamshin mai kamawa ba, ga turaren wuta sai kamshin ya hadu ya ba da wani irin kamshi mai kwantar da zuciya. Duk da cewa side din Farida shima kamshi na mussaman yake yi, amma kamshin wurin Sa'a yafi kwanta mata a rai ko dan kishi ne oho. Sa'adah ta zauna tana haki, ta ce shiga ki dauko muku ya nan a cikin warmer. Ta shiga kicin din tana kallon komai, kayan tsilla tsilla amma kuma unique. Ta fito ta ce "Na gode sosai Gogel". Takaici ya kama Sa'adah wato Farida ba zata daina yi mata izgili cikin dabara ba. Ta tuna sunan garin su Farida Torondi, Amma bata ta'ba kiranta da hakan ba, ta tuna yadda yan set dinsu suke ce mata Taller saboda tsayinta, amma ita bata fa'da mata hakan ba. Ta sake tuna yadda ko Farida bata fa'da a gaban Jawad sai dai Anti! Amma shine ita zata dinga ce mata Gogel, ta tuno har a asibiti ta yi mata kashedi, amma saboda tsokana sai ta sake fa'da. Ta yi tsaki tana tunanin abin da zata yi mata idan ta sake. Ai kuwa washagari zata fita wurin aiki ta leko ta kawo mata dish dinta. Suka gaisa lafiya Lau ta kai kicin ta ajiye mata. Zata fita ta kalli yadda Sa'a ta zama gari guda. Ta ce "Gogel indai ba twins bane a cikinki, gaskiya kin kusa sauka, sai dai kuma na ga sai yanzu ne muke shirin four months a gidan nan". Kafin ta rufe baki Sa'a ta yun'kura ta ce "Idan zaki iya tuna kwanakin da kika yi ba kya ganinsa da rana, ba ya cin abincin ki da rana, to sune kwanakin da aka samu cikin, shi ya yi abinsa bayan an shafa fatiha ba wai shege bane". Nan da nan Farida ta muzanta ta ce "me ya kawo wannan maganar kuma Gogel?" Ai kuwa Sa'a ta ce "Tsugudidinki da tsokanarki, ta nunata da yatsa ta ce "Taller ki fita a idona tun muna shaida juna". Ga mamakin Farida sai ta ji Sunan da Sa'adah ta kirata da shi na Taller ya yi mata zafi ba ka'dan ba. Idonta ya ciko da 'kwallah ta ce "Sa'adah daga wasa?" Daidai lokacin Mk ya shigo! Sa'adah ta ce "ke Kika san wannan, to bana son wasan indai irin wannan ne". Ai kuwa Farida ta hau hawaye. Sa'a tana kallonta bata yi mamakin hawayen data fara dan ta ga mijinta ba, da'din abin dai bata isa tasa ya daketa ba. Ai kuwa Mk ya nemi jin ba'asin kukanta, ta ce Ba komai". Ta juya ta fita, shima ya bi bayanta, bai yarda ta fita da damuwa ba, sai da yaga ta saki ranta, da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, ya rankwafa ta windo yana cewa "drive with care please". Yayin da zuciyar Sa'a tamkar ta fashe saboda duk tana hangensu ta windo. Sai da Farida ta tafi sannan ya koma wurin Sa'a ya sameta, ya dinga yi mata sababi akan ta zo wurinta ne zata wulakantata har ta sakata kuka, har yana fa'din ke baki san halin Farida da son raha ba, ki dinga jin tausayinta mana". Ba'kin cikinsa yana neman kassarata. Ta hadiye kukan ta ce "Ai yanzu na gama ganeka, ita bata laifi, komai ta yi daidai ne, kome take so haka zaka yi mata, saboda ita din Babanta zai siya mata kowanne irin miji". Ai kuwa ya hassalo yana fa'din "wulakanci ki ya tashi ba? Ni kika fa'dawa wannan maganar?" Ta kasa magana saboda a yanzu shakkarsa take ji sosai, ba kamar da ba, hawaye ya balle mata. "Ta ce ta zo har 'dakina ta tsokane ni, bayan ka san har fa'da maka na yi akan ka yi mata togaciya, amma ba bincike ba komai, ka bi bayanta, ka rarrasheta, ni kuma ka zo kana mini jidali". "Jikinsa ya yi sanyi, fishinsa ya sauka, ya isa gareta da nufin rungumeta, ta goce ta ce "Tun bamu je ko ina ba kana son sai na gaza". Ya sassauta murya ya ce "Tausayinta nake ji, bata da lafiya sosai, bata samu haihuwa ba, sannan na fi son wata akanta, fa'da mini dan Allah bata cancanci a ririta farin-cikinta ba?" Ta zuba masa ido ta ce "Ban son wannan tausayin da ka tsananta akanta, ina jin fargabar abin da nake gani a idanuwanka akan lamarinta". "Ni meyasa baka jin tausayi na irin haka?" Ba ja in ja ya ce "Ina tsananin sonki Ubangiji ne shaida, kina da cikakkiyar lafiya, Ubangiji ya hore miki, kina haihuwa Ubangiji ya arzurtaki, Ubangiji ya arzurtaki da mahaifin da ba kowanne 'da ne yake samun irinsa ba. Fa'da mini ta inda baki kereta ba". Ya ru'ko ta, tana cigaba da kuka tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157