Chapter 9
Chapter 9
a ranshi yanzu, tunda akan kunnenki Baba direba ya tabbatar da shi kanshi ya fahimci irin son da yake miki, ke ma kuma ya lura kina son shi, haba Sa'adah!" Kukan da Sa'adah ke ma'kalewa ya kwace mata sosai, har Zainab ta ji to ko akwai wata magana data fada cikin kuskure wacce tasa ta kuka haka? Amma da ta tuna Sa'adah sarkin kuka ce ko ba dalili, yasa ta samin nutsuwa. Shiru ta yi, ba ta yi yunkurin hana ta kukan ba, ta san ko ba komai dai za ta sami salama a zuciyarta, sai da ta tabbatar ta yi ya ishe ta sannan ta ruko hannunta tana fadin ya isa haka, ki yi hakuri komai zai wuce ya zama tarihi, ki yi addu'ar zabin alheri, bawai zabin ranki ba." Ta mike tana cewa, "Kin ji har ana kiran Maghrib bari na tafi sai na sake shigowa, ko kuma sai na gan ki." Sa'adah ba ta ce mata uffan ba, ita ma Zainab din sanin halin 'kawarta tun fil'azal yasa ba ta damu ba. Ta juya ta fita, a tsakar gida ta tarar da Inna ta goya Khalifa ya nata barci, "Ah goyo ki kayi haka Inna? Ai sai yasa miki ciwon baya." Murmushi Inna ta yi tare da cewa, "Ku dai yaran yau da bakwa son goyo ne kuke kallon zai sa ciwon baya, alhalin shakuwa da tausayi ke 'karawa a tsakanin uwa da danta, amma ku boko da gayu ya hana ku goyo sai dai a hannu" Dariya Zainab ta yi tana fadin "Inna Allah ina 'ko'kartawa." "Allah Ya sa!" Inna ta fada tana kunto shi, yaro yasa kuka, wai shi an saukko da shi, ai ko Inna ta ce, "Juyo na sa miki shi a bayan." Cike da kunya da girmamawa tace, "To" Ta sunkuya ta sa mata shi har zanin Inna ce ta daura mata, sannan ta bar ta ita kuma ta hau kiciniyar gyara goyon. A gurguje suka yi sallama ta tafi ita kuma Inna ta yi bandaki da buta a hannunta. Ta idar da sallar Maghrib tana zaune kan sallayar tana jan carbi, wayarta ta hau 'kuwwa, hannu tasa ta janyo ta ganin sunan Hajiyar Bichi, yasa gabanta ya fadi, duk da suna waya lokaci zuwa lokaci, amma ba tasan dalilin faduwar gaban da ta ji a yau ba. katsewa ta yi sai ta kira ta, Hajiya ta ambata sai kuma tace, "Assalamu alaikum!" Ciki-ciki Hajiyar ta amsa. Sai jikin Sa'adah ya yi sanyi ta ce, "Lafiya kuwa Hajiya?" "Ba lafiya ba Sa'a, yanzu a ce za ki tafi wurin Jawad amma ki kasa fada mini? Na san kuma kinsan ubansa baya nan?" "Hajiya ni ban sani ba". "kin sani mana ai ba zuwa kike ranar da ake taron ba, amma wannan karon kin je saboda wanda kike gujewa haduwar ta ki da shi ba zai jeba, sai kuma Allah ya yi nufin haduwar taku wanda shi kadai ya san manufar hakan. Ban ga kuma laifinki don kin kame kanki ba. Laifinki daya da kika san dukkan ahalinki ba za su sami zuwa ba, sai ki fada mini mu tafi bibbiyu, wannan abu da kika mini sai nake ganin kamar ni ma fushin da kika dauka ya shafe ni ganewa ne ban yi ba sai yanzu." Cikin son kare kai da kuma iyakacin gaskiyarta tace, "Wallahi ko ka'dan Hajiya ba haka ba ne, ba abin da za ki mini nan duniya na yi fishi da ke, har gobe ke uwa ce. Tunani na bai ba ni na yi hakan ba, na ma yi tunanin direba zai kai ku tare da Antinsa, amma ki yi ha'kuri Hajiya" Take ko Hajiyar ta ce, "Na huce dama rashin fahimta ne, ki gaida Innar taki, kuma In sha Allah ina nan tafe cikin satin nan" "Allah ya kawo ki Hajiya!" Ta ajiye wayar tana jin idan akwai asarar da ta yi cikin rabuwa da MK to kuwa rashin nagartatciyar suruka irin Hajiya na kan gaba, jin kanta ya mata nauyi ne yasa ta ci gaba da ambaton Allah. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍️ [5/15, 19:03] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.} https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *SADAUKARWA GA* *SADIQ ABUBAKAR*. *ALLAH KA JIIKAN* _HAUWA M. HASSAN_ *(FINE GIRL)* _UBANGIJI KA ALBARKACI SU FA'EEZA_. 13-14 Tsawon kwanaki addu'ar za'bin alheri ya dinga yi tsakaninshi da Sa'adah ba 'kak'kautawa, kuma ALHAMDULILLAH, ya ji takurar da yake ji akan zama da ita ta kau, ya sami sau'kin nauyin da zuciyarshi ta yi akan ta. Ranar Juma'a bayan an sau'ko Masallaci kai tsaye gidan su ya zarce kamar yadda ya saba a falo ya tarar da Hajiya zaune kan sallaya, tana lazimi. Ya jima yana zaune kafin ta shafa addu'arta ta juyo ta kalleshi, a nutse ya shiga gaishe ta tare da tambayar jikinta kasancewar kwanaki biyun nan fama take ta yi da zazzabin cizon sauro. "Jiki kam na ji sau'ki sai rashin 'karfin jiki wanda sai a hankali." Ta fada tana daddanna 'kafarta. "Hajiya 'kafar ciwo take miki ne?" Ya fada cike da kulawa. Ta ce, "Ba wani ciwo kawai kasala ce!" "Sannu idan kin gama shan maganin ba ki ji daidai ba, sai na mayar da ke wajen likita." Da sauri ta ce "Kai raba ni da zancen Likitan nan na ji sauki." Dariya ya yi! dama tsokanace wannan zazzabin ma da 'kyar ta yarda ta je asibitin bare ta yarda ta koma. "Har yau ba ka ce mini komai akan maganar Sa'a ba?" Murmushi ya yi "Oh! Hajiya ai na ga ba ki da lafiya ne." "A a na ji sauki " Gyara zama ya yi sosai ya fuskance ta, "Hajiya!" Ya kira sunanta. "Na'am!" Ita ma ta amsa tare da mi'ka dukkan natsuwarta gare shi. "Kamar yadda na ce miki zan yi addu'a, to na yi! kuma na ji tsoro da razanin da nake ji a tattare da zama da yarinyar nan ya gushe daga zuciyata, amma..." Sai kawai jin ta ya yi tana ambaton Alhamdulillah! tausayinta ya kama shi na ganin tsananin murnar da take yi akan abin da ba tabbacin yi yuwar faruwar shi. Ya san Sa'adah, ta kyautata mata matu'ka. Lamarin da Hajiya ta tattara dukkan kaunar da take mishi ta mi'ka mata, duk irin laifin da za ta mishi tofa a idon Hajiya ba laifi ba ne sai ta ce ai yarinya ce, 'kuruciya ce ba kuma hankalinsu 'daya ba. Har ya fara yi wa Sa'adah kallon macijiya ta sare shi, ta kuma koma gefe ta lullube uwarshi da alheri, haka nan hatta 'yan uwansa, mussaman Samira da Hafsatu basu dauki lamarin Sa'adah da wasa ba, saboda yadda ta kyautata musu iyaka, ya san ba ta da rowa, tana da saurin sabo, ba ta kuma sa ido a lamarinsa da 'yan uwanshi, komai zai musu kuwa, wani lokacin ma ita take ankarar da shi. Shi har mamakin ta yake yi yadda duk wani rikicinta, fa'danta, rashin kirkinta, da kuma rashin ha'kuri duk akan shi ya 'kare. Ta 'dago tana kuma ambaton ALHAMDULILLAH. "Hajiya abin da nake so ki gane yarinyar nan fa yanzu gaba'daya ba yadda kike zaton ta ba ne, na tana son dawowa 'dakinta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157