Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da damar yin walima wannan sunna ce sai ku yi. idan har wannan tsarin ya yi, akan hakan za ka turo mini magabatanka, Saboda idan sun zo, zan sanar da su." Godiya sosai Mk ya sake yi tare da fadin, "In Sha Allah yadda duk ka ce haka zan yi Baffa, na gode sosai da karamci Allah ya saka da alheri." Da haka suka rabu MK na jinjina halin wannan dattijon, ko irin su nawa ne suka yi saura a cikin al'ummar mu? Gefe guda kuma tunanin yadda Sa'adah za ta karbi lamarin yake yi, ko ya ya za ta ji idan aka ce ba za a yi mata lefe ba? Sannan ya za ta yi idan ta gane cewa ita ma haka za a kai ta ba kayan daki, ba biki irin na zamani?😁 Da kansa ya ji dariya ta kufce masa haka ya samu gefe ya yi dariyarsa mai yawa, sai da ya gama a fili ya ce, "Sa'adah big girl ba lefe!" 😁 MK shiru ya yi bai fada wa Sa'adah tsarin Baffa ba, bai san mai yasa yake jin tsoron fada mata ba, ya ja bakinsa ya tsuke, ta ji maganar a bakin wanda ya tsara lamarin. Takanas 'yan uwan mahaifin MK, Baba Umaru, da Baba Idi, suka taho Kano suka hadu da Alhaji Isa, suka rankaya gidan su Sa'adatu nema wa MK auranta. Kai tsaye ya ce ya ba su sannan sadaki kawai za su kawo masa. Bai boye musu tsarinsa na rashin yin hidima ba. Dukkansu, sun yi farinciki, sun kuma yi amanna da tsarinsa, suna fadin ai mu ma da ga yau za mu yi koyi da kai don mu sami sauki a cikin zamantakewarmu, sannan darajar aure za ta karu za a daina fargaban yin sa, saboda an kewaye shi da hidimomi masu wahalarwa. Baffa ya sake cewa "Na baku wuka da nama duk lokacin yaron ya kammala shirinsa kusa ranar aure da kan ku, sai ku sanar da ni, ina kuma rokon ku fada masa iya abin da zai iya shi zai yi, fatana dai Ubangiji ya albarkaci auren." Godiya sosai suka yi suna yaba halin kwarai irin na mahaifin Sa'adah, suka jaddada masa ba da jimawa ba kuwa zai ji ranar da suke ganin ta dace da shirin MK, suka sake yi masa godiyar wannan girman da ya ba su. suka rabu cike da farinciki, a hanyar su ma tattauna karamcin da suka gani suke ta yi. Alh Isa ya ce, "Ai ni tun zuwan da na yi a farko na gane Mukhtar ya nemo aure a gidan mutunci, sai dai mu yi fatan Allah ya zaunar da su lafiya." Dukkan su, suka hada baki wurin fadin, "Ameen." Baba Umaru ya nisa ya ce, "Saboda karamcin wannan Mutumin, bayan sadakin da zan biya wa Mutari har kudin da zai shirya wa yarinyar daki zan ba shi ya kara saboda iyayenta su san muma mun iya karamci." Su Alh Isa su ma suka hau fadin, "Ai kuwa mu ma za mu sake sabon shiri." Sai da suka je gidan su MK suka yi wa Hajiya Babba bayanin halin da ake ciki, sannan suka tafi. Dukkan dangin MK sun karbi tsarin mahaifin Sa'adah, na ba zai yi kayan daki ba, musamman da bai nemi a ba shi wani kudi ba, illa ma lefen da ya ce su ma kar su yi. Da daddare suna falon gidan gaba'dayansu har Hajiyar Bichi, kasancewar duk sun zo gidan saboda haihuwa da Sameera ta yi, yau kuma aka yi suna, shi ne suka zarto gidan su. Hafsatu ce kawai ba ta nan, saboda a Lagos take aure, Hajiya Babba ta sanar musu. Ta kare maganar da cewa "Kayan da na fara tarawa na lefe kuwa tabbas zan ba ta, don da sunanta na ke sayan su." Hayaniya ta cika falon na yadda suka ji dadin tsarin suka hau fadin, "Ai kuwa dai za mu dage mu yi kayan daki masu kyau." Abbas ya dubi MK ya ce, "Amaryar taka tana da 'kanwa ne?" Falo ya sake daukar hayaniya Akil ya ce, "Saboda ka ji ba lefe ba bidi'oi?" Shi dai MK bai sa musu baki ba, suka yi shewarsu, suka gama. Haka ma Hajiyar Bichi uffan ba ta ce ba! Haj Babba ce da ragowan yaran suke ta dabdalarsu. Kwanaki uku tsakanin zuwan iyayen MK, Alhaji Isa ya sake yin tattaki da kansa ya sanar da Baffa suna son a yi auren bayan karamar sallah watanni biyar masu zuwa. Bai musa ba ya ce, "Allah ya sa ranmu zai kai" Baffa bai yi kasa a guiwa ba ya hakurkurtar da Alhaji Mamman, da ke ba yaro ba ne rabuwa aka yi irin ta salin alin, duk da bai so hakan ba, amma ya hakura, ya kuma roki Baffa ya ba shi damar ganinta, a karo na karshe. Baffah bai ki ba ya ce zai iya ganin ta. Maimakon ya jira a turo masa ita sai ya ce bari ya je ya dawo. Ashe sayayya ya tafi lodowa, bayan ya dawo bai jima ba, ya ba wa Sa'adah manyan leda har biyu shake da kayayyaki, yana fadin, "Na gode da mutuntuwa, Ubangiji Ya sanya alheri a tsakanin ki da wanda za ki aura" Ya yi mata sallama ya tafi yana jin ciwon rasa ta don so yake mata na fisabilillahi. Sai a lokacin Sa'adah ta ji sanyin jiki tana jin tausayin sa na ratsa ta. Tana shiga gida, ta zauna kusa da Inna ta fara bude ledar da ya kawo mata. Ta shiga dubawa, manyan leshi masu tsadar gaske guda biyu, da shadda getzna, ita ma biyu, da kuma atamfa Super Wax ita ma biyu, kowanne kuma da mayafinsa sai turaruka. 'Dayar ledar kuma takalmi da jaka ne har set shida masu tsananin kyau da tsada, da envelope wanda da dukkan alamu kudi ne, za ta ya ga ke nan, Inna ta ce, "Kar ki bude ki bari Baffan ku ya gani". Inna tana daga kaya tana fadin, "Wannan ya gane cewa aka yi ya yi ha'kuri? irin wannan kayan sai ka ce mai hada lefe?" Sa'adah dariya ta yi sannan ta ce, "Kai Inna duk da dai kayan masu daraja ne amma ai ko an sayar da su sai dai a hada lefe irin local din nan." Zuba mata ido Innar ta yi, sai kuma ta yi kwafa sannan ta ce, "ko ma yaya ne ai an yi 'ko'kari wata ai ba ma za a mata lefen ba, bare ta ga ya yi ka'dan." Cikin dariya sosai Sa'adah ta ce, "Yo kuwa Inna wacce ba za a mata lefe ba ai sai bazawarar da ta sarayar don tana bu'katar auren, da kuma budurwar da ba ta da daraja ake neman kai da ita." "Dariya ita ma Innar ta yi tana cewa "Ashe yayarki ma ba ta da daraja! don kuwa babu lefe aka aurar da ita, ba kuma neman kai mu ka yi da ita ba." "Auran Anty Sumayya ai irin na zamanin jiya aka mata, kar ki ba da misali da auranta" Ta nisa ta ce, "Iyah ba ki ga kuma saboda mijin natan ya san mutunci ya zame mata irin mijin da ba a cika samun su a Yau ba! Ke da kanki kin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});