Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

halinta na son kayan 'kawa. Hatta kayan fitar biki masu kyau aka tanadar mata shike nan sai hankalinta ya kwanta. musamman da Sumayya ta ha'kur'kurtar da Baffa ya yarda za a kai mata gadonta 'kirar Dubai. Kafin ranar 'daurin aure gidan amarya ya fito fes komai ya ji, Sumayya ta yaba 'kwarai da kokarin MK da iyayensa, saboda haka sai ta sa aka mayar da gadon dake dakin MK zuwa dakin dake cikin falon wanda babu komai a ciki, shi kuma aka saka masa hadadden gadon Dubai. Kicin aka sake 'kawata shi da tsirarrun kayan alfarma, aka rufe gidan ana jiran isowar TV da Fridge da kuma amarya! don Mk tuni ya tare a cewarsa gadi yake yi.😁 *05/06* Ranar aka daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel, a Masallacin Sahaba dake Kundila, kamar yadda Baffa ya ce ba za a yi party ko ka'de-ka'de ba hakan ce ta kasance. Amma kuma ya tsaya an yi abincin 'daurin aure da yini na fitar kunya, duk wanda ya halarcin auren Sa'adah mace ko namiji ya ci abinci mai rai da lafiya don kuwa Bijimin sa Baffa ya yanka, duk tanadin Baffa a shirya abincin fita kunya ya kare. A lokacin sarkar gold din dubu hamsin babba ce, ita ya siyawa amarya da shawarar Sumayya da take ta 'koda irin kokarin da MK da iyayensa suka yi. Sai kuma 'dinkunan da ya mata na kwalliyar amarci. A Daren da aka daura aure suna zaune a gabansa ita da Sumayya da mahaifiyarsu, bayan ya yi addu'a ya ce, "Duk wani burina a yau ya cika Iyah, ina kyauta zaton na dan'ka ki a hannu na gari don Allah ki bi mijinki, nasan kinsan idan mijinki, ya yarda da ke to Ubangijinki ma ya yarda da ke, idan kika ri'ke wannan kadai za ki gane komai za ki yi a 'dakin mijinki ibada ne. Ibada kuwa sai an daure domin za ka ci karo da abin da kake so da wanda ba ka so. Na ro'ki ki yi koyi da yar uwarki wurin boye sirrin aurenta, har yau din nan Sumayya ba ta taba fa'din ga laifin mijinta ba, mun sani ba fa don ba ya mata laifin ba ne, haka shi ma yana ri'ke da ita cikin ha'kuri da girmamawa. Ina sake miki nasiha ki zama mai ha'kuri, baki da'yan aure wallahi hakuri ne ya fi yawa, ina fatan ki yi ko yi da mahaifiyarki wurin ha'kuri da biyayyar aure!" Ya janyo ledar dake gabansa ya fito da sallaya da kur'ani ya mi'ka mata, ta miko dukkan hannunta biyu da suka sha adon lalle ta kar'ba, yace "Ki rike ibada da kyau ita ce za ta jagorance ki duniya da lahira." Ya kalli Sumayya yana fadin "Ina abin da nace ki ajiye?" Da sauri ta mi'ka masa dama ta shigo da shi ya karba ya sake mika wa Sa'adah yana fadin, "Ki rike tsabta da kwalliya da ma ba na jin ki a wannan bangaren. Inda nake da shakku akan biyu ne. ki 'karanta buri Iyah kin dai san ni ubanki ba kowa ba ne, ki yi alfahari da abin da yake hannunki, ki daina sha'awar wanda suka fi ki ko kuma wanda ba tsarin tarbiyarku daya ba, a yanzu da za ki koma 'karkashin mijinki, ina hada ki da Allah kar ki dinga dora masa hidimar da ba zai iya ba, ko ba ra'ayinsa bane. Da ace za ki rabu da harkar kawaye to ina tabbatar miki za ki 'karantawa kan ki buri saboda ba kya hangensu. A karshen karshe na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, ina fatan Allah Ya lullube rayuwarki da albarkaSa, ya ba ki zuri'a mai albarka, ya kuma hore miki ha'kurin zaman aure." Daki ya yi shiru sai shesshekar kukan Sa'adah, Baffa ya nemi Inna ta ce wani abu, ta girgiza kai tare da cewa, "Duk abin da zan fada na dade ina mata bita indai mai ji ce ai ta haddace su. Fatana Allah Ya albarka ci aurenta." Cikin soyayya mai yawa Baffa ya kalli Sumayya ya ce, "Saura ke babbar yaya uwa ta biyu!" Ta yi murmushi cikin sanyin murya ta ce, "Komai kun fada Baffa, fatana a ce duk ta ji ku da kunnen basira, ta kuma ri'ke 'yan'uwansa da girma, musamman iyayensa. Ki rike su da mutuntawa komai za su miki kar ki nuna kin ji haushi ki yi hakuri, ki sake ninka kulawarki a kansu, duk kuma wanda ya je gidan, ki karbe shi da sakakkiyar fuska su ji tamkar a gidan yar'uwarsu mace su ke saboda sakewa da walwala." Baffah ya nisa yace " idan Kika bi maganganun mu kin tsira! Idan kuwa kika je kika biyewa 'kawayen banza da son zuciya ki tabbatar ke 'kadai za ki dauki 'bacin ran da zai same ki, ki bi mijinki ko zaluntarki yake yi ki bishi da addu'a idan abin ya gagara, sai mu shiga, amma idan ke Kika bijire to fa kisani baki da wurin zama a gidannan". Ya rufe zaman da doguwar addu'a ya kuma rike ta a hannunsa ya tafi kai ta 'dakinta da kansa a motar Alhaji Isa da ya zo daukar Amarya. 'Yan'uwan Baffa da na Inna da suka zo, sai mamakinsa suke yi da ya hana su zuwa kai amarya, ya tafi da kansa ya kai 'yarsa dakinta. A lokacin kam ya zo da sabuwar dabi'ar da ta sha banban da al'ada, ashe shi yasa yasa aka kai su suka ga gidan amarya tun jiya? *SURAYYA DAHIRU*. ✍️✍️ 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *TUKUICI GA* _*AISHA IBRAHIM BAFARAWA*_ (*BEAUTY*) *MK DA SA'ADAH NA GAISUWA* 👍 49-50. *GIDAN AMARYA* A gidan su Baffa suka tarar da su Baba Umaru da Baba Idi da kuma MK. Tunda Baffa ya fa'da musu a wurin 'daurin aure cewar shi zai kai amarya 'dakinta kar a turo mata, sai suka fasa komawa Bichi a yau, suka ce su za su karbi amarya da kansu. Haka Baba Umaru ya tisa MK da jan kunne iri-iri akan ya ji tsoron Allah ya ri'ke matarsa cikin tausayi da adalci, komai za ta yi ya dauke kai ya fahimtar da ita cikin ruwan sanyi. Baba Idi ya nisa ya ce, "Sannan zan fa'da maka gida naka ne, amma kayan ciki na matarka ne, kana dai ganin irin mutunci da karamcin da aka maka, to ina ro'konka! ka nuna kai ma ka san mutunci ta hanyar zama da yarinyar nan da kyautatawa, ba hankalinku 'daya ba, mata lamarinsu yana da gigitarwa. Amma idan aka yi ha'kuri da su, aka musu afuwa sai a ji dadin zama da su, saboda masu rauni ne, kuma masu tausayi ne". Alh Isa kuwa cewa ya yi, "Abin da zan fada muku ni ne uban Mukhtar, ni ne uban Sa'adatu, sannan ni ne alkalinku dukkanku 'daya kuke a gurina.

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});