Chapter 81
Chapter 81
tsayawa ya bi ta kansa. Ta shiga damuwa da tsoro irin wadda bata taba shiga ba, tsoron ta 'daya idan iyayenta suka ji mai ya jawo wannan tashin hankalin, wanne irin kallo zasu yi mata,? Ta 'kudiri aniyar yau zata bashi, ha'kuri ta kuma nemi ya barta taje ta gaida Aunty Sumayya. Haka akayi, taran dare ta yi wanka, ta shirya cikin kwalliya ta burgewa, tana jin dirin motarsa da kiciniyar bude gate, ta fita a hanzarce ta shiga kicin mai ma'kwabta ka da 'dakinsa ta tsaya. Ai kuwa ya shigo da sauri, ganinsa rungume da kayan wankinsa da ya kai wanki, jikinta ya sake yin sanyi, komai zata yi masa, idan zai kai wanki zai shiga har 'dakinta ya hada kayanta akan nasa ya kai musu wankin amma banda Wannan karon. Kafin ta yi yunkurin shiga dakin nasa sai ta ga ya fito ya fita da alamun ya yi mantuwane, dan haka sai ta yi wuf ta shige 'dakin, yana shigowa kuwa ya rufe 'dakin bayan mukulli har da sakata ya sanya. Yana shigowa ya ganta lafe jikin wadirof, ga mamakinsa sai yaji kwalliyar da ta yi, bai ji komai na burgewa akanta ba, hakanan kamshin ta da ya cika masa hanci bai yi tasiri a jikinsa ba, kyakkawar fuskarta da ke sanya shi nisha'di, a yau ba'kanta masa rai ta yi, hakanan surarta da ke jefa shi cikin shauki, a yau takaici ya ji ya maye gurbi. 'Bacin ransa ya dawo sabo fil tamkar yanzu take gasa masa maganganun da suka zame masa tamkar 'digar dalma a zuciya, suka yi awon gaba da kaso mai yawa na matsananciyar soyayyar da yake mata. Baice mata komai ba, ya shiga rage kayan jikinsa, ya shige wanka, tana tsaye ya fito ya shirya, ya tada sallar shafa'i da wutiri. Sai da ya idar ya zauna bakin gado ya kalleta, ya ga duk ta takura, ta susuce, ta lalace, idonta ya fada alamun dai tare suke 'dan'danar 'bacin rai. Kafin ya yi magana ta rigashi! Ta tsugunna ta ri'ke gadon ta ce "Dan Allah Malam ka yi ha'kuri, ban taba jin nadama irin wadda nake ciki ba". "Ba ki mini komai ba, abin da ke zuciyarki ki ka amayar, sai dai ina so ki sani wallahi ba ki fara nadama ba, ina tabbatar miki za ki shiga NADAMAR da ta zarce wadda kike ciki, da kinsan yadda na tsani ganin ki da hakan ka'dai ya isa ya saki nadama, da kinsan yadda kika wanke kanki a zuciyata da kin gane asarar da kika yi ba ka'dan bace". Kuka ya goce mata, ta rarrafo da nufin ri'ke shi, ya zabura ya mike tsaye cikin bacin rai ya ce "idan kika yi kuskuren sa hannun ki a jikina, na rantse miki sai na miki abin da za ki gamsu ba ki da sauran 'kima a gurina. domin duka zan miki irin yadda ake na'dawa 'yantattatun matan bariki idan angama cin moriyar su". Kukan ya tsaya mata! da gaske ta yi kuskure, irin kuskuren da ake yi sau daya amma sai an nemi hanyoyi gyara dari bai gyaru yadda ake so ba. daga jiyo magana a bakin shedanun mata ta ara ta yafa, har ta zo ta fa'dawa mijin aurenta wadda da gaske samun irinsa zai yi wahala. Ta zauna 'dabas tsakanin gado da wadirof ta dinga kuka, mai cin rai, na tsantsar nadama. Daga inda yake ya ce "Ta shi ki bar mini 'daki ban bukatar ki a cikinsa". Ta kasa koda kwakwkwaran motsi. tace "ka yi hakuri ba dan ni ba, ka dubi girman Allah ka yi hakuri". Jikinsa ya yi sanyi yace "Na ji, amma dai tashi ki fita, ina bukatar ka'daici ne, duk sadda nake da bu'katar ki a dakin I will let you know". "To ka daina rufe 'dakin, na yarda duk sadda na zo ka kore ni, amma ka daina rufewa". Ya zuba mata ido yana jin takaicinta na sake kama shi, amma da yake so yake ta fita ya shaki iska marar takura sai yace mata to a takaice. Ganin ya amsa mata sai ta tashi ta bude 'kofar ta fita tana fadin " ka yi hakuri, ka yi barci mai cike da walwala". Ya bita ya rufe kofar, ya dawo ya karanto adduar barci ya kwanta. Washagari da sassafe ta shirya masa abincin karyawa ta zauna zaman jiran ya bu'de 'kofar, ai kuwa yana budewa ya ganta da tiren abinci, a bakin kofar dakin, yasa kai zai wuce ta ce, " Ina kwana?" Ya amsa a gajarce, "ga abinci na gama". ya girgiza kai ya ce "ki daina wahalar da kanki wurin yin abinci saboda Ni, na riga da na 'yanta ki daga dukkan yi mini hidima kowacce iri ce". "Cikin rawar murya ta ce "kace fa ka yi hakuri?" "Da ban yi hakuri ba, da baki ganni akan 'kafufuna ba, da ina can akan gadon asibiti saboda ba'kin cikin ki, da ban yi ha'kuri ba, da ban tsaya ina miki magana ba". Ta goge hawaye ta ce "ka kara hakuri dan Allah nasan na yi ba dai dai ba". Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba, ya fara tafiya, da azama tace " Malam! Umman fanshekara gobe zata tafi Gombe, dan Allah ka bar ni mu tafi tare, ni sai na dawo ko jibi ne". Ya juyo a zabure tamkar wadda ta fadi mugun abu ya nunata da yatsa ya ce" dama nasan duk wannan saukar da kan da kika yi, kina da bu'kata ne, ba kya tashi mutunta ni, ko kwantar mini da kai sai kin ganni da kudi, ko kina son na barki kije wani guri". Cikin kuka sosai ta ce "Haka ka dauke Ni?" "Kin wuce hakama ke kam, saboda ke ciki ce mai manta kyautar jiya, mai manta alheri, da kina da hankali, da baki cemin za ki tafi yawo Gombe ba, kawai tafiya za ki yi kanki tsaye". Ta zuba masa ido ta ce "dubo Anty Sumayya ne yawo?" A kausashe ya ce "ke kika san Sumayya, ni mai na hada da ita! ko dole nace?" Tashin hankali 'baro 'baro ya bayyana a jikinta gaba'daya, lalle da gaske Mk ya shiryawa tashin hankali iri iri, wai Anty Sumayya ce yake fadin sunan ta gatsal, duk da ya girmeta da shekaru biyu amma Anty yake cemata, sannan kuma har yana cewa mai ya ha'da da ita?. Ta kalleshi baki na rawa ta ce "Dan Allah Malam ka yafe mini, mu zauna lafiya ba zan iya kar'ban wannan tashin hankalin daga gareka ba, na rantse maka ba zan kuma maka laifi ba, zaman lafiya zamu yi, fiye da yadda ka ke so". Ya yi murmushi ya ce "na la'anci zaman lafiyar da ki ke so mu yi Sa'ade, zuciyarki bata da alheri, kwakwalwarki ba ta da tsinkaye, harshenki yafi na maciji dafi, ba sauran zaman lafiya tsakanin mu, idan har kika zauna lafiya da ni ban yafe miki ba". "Zuwa Gombe, ko yanzu kina iya tafiya, sai dai idan ina da hakki akan ki, ba za ki ga alheri a yayin tafiyar da dawowar ba in sha Allah". Ya ja dogon tsaki yana fadin shashar yarinya da bata san mutunci da kyautatawa ba". Ya sake jan dogon tsaki ya fice,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157