Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 83

Chapter 83

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

'kasa tana ta kuka, kukan kuma shi yake tayar da hankalin Hajiya. "Wai wannan kukan na menene haka Sa'a? Kin ga kuwa yadda fuskar ki duk ta aune?" Murya a dakushe ta amsa da cewa "ki ce ya daina mini fishi, sannan idan na dafa abincin ya dinga ci". Kafin Hajiya ta yi magana, Mk ya yi fit yace "Ni yaro ne da za ki dinga control 'dina? Na 'ki na ci abincin na ki" "Kin ji da kunnen ki ban isa da shi ba, dan haka ki share hawayen ki, komai da ki kasan hak'kinsa ne ki masa kar ki gaji, ubangiji ne yace ki masa biyayya, idan ya zalunce ki, ba zai barshi ba". Ta mike tana gyara zaman Hijabin ta, ta sake cewa "Ki yi hakuri, kar ki biye masa, kinsan idan tururuwa ta so lalacewa fuffuka take yi, Allah ya miki albarka kin ji! Ki tashi ki yi wanka ki ji da'din jikin ki". Ta juya ta fita ba tare da tabi ta kan Mk ba, da ya bita a baya yana cewa "Hajiya! ko kula shi bata yi ba ta yi ba, a waje juyin duniya akan ta shiga motarsa ya kaita, kamar yadda ya kawota, ta 'ki bude baki ta masa magana bare ta amince, haka ya dinga bin ta har titi, ta tari adaidaita sahu tana shiga, shima ya yi wuf ya fa'da, har suka isa Na'ibawa ba abin da ya ke yi sai tunanin mai zai yiwa Sa'adah ya huce. Ba zai iya tuna lokacin da Hajiya ta masa irin wannan fishin ba. Suna isa ta sau'ko ta wuce gida, ya tsaya ya biya kudin, sannan ya bita cikin gidan Yana isa ya tarar da ita zaune a tsakar gidan, bata shiga dakinta ba tabbacin ba zata saurare shi ba. Ya tsugunna, ya dinga bata ha'kuri, ya dade yana fama, kafin ta ce "Nunawa ka yi fa ban isa na zartar da abu a kanka ba, ganin na isa ne yasa ta ce na yi maka magana, kai kuma ka bata amsa da ta ke nufin ban isa ba, dan haka duk ranar da Sa'a ta fara ganina ba 'kima kar ka ga laifin ta". Ya yi shiru yana ayyana wai su mata haka suke ne? manya da yaransu sun iya kacaccala magana, su juya ta, komin gaskiyar ka sai sun nuna su ka zalinta ko ka ketawa haddi? Kan dole ya ce "Ki yi hakuri Hajiya Dan Allah! sannan ina tabbatar miki da ikon Allah ba macen da zan zauna da ita alhalin bata ganin girman ki". "Fatana ki huce, ki yafe mini bacin ran da na sanya ki". Fuska ba walwala ta ce "idan har kana so na huce, hankalina ya kwanta, to ka zauna lafiya da matarka, na lura itace bata da gaskiya, amma abin da zaka lura ko a lahira wani na cin albarkacin wani, ka manta komai ta yi maka, ka mata afuwa, ba hankalinku daya ba". Ya nisa ya ce "Allah Hajiya ban so ki ka shigar mata ba, so nake kawai ta banbance tsakanin zaman lafiya da kuma zaman tashin hankali, ta fitine ni wallahi". "Kaine Babba hakuri za ka yi! sonka take yi, shiyasa ta ke kishin ka, tunda ka fahimci matsalolinta sai ka kiyaye abin da zai tunzura ta, har hankali ya shigeta, wata rana ko ance ta yi wani abin ba zata yi ba". "Shikenan na ha'kura saboda ke, amma wallahi ki dinga mata fa'da Hajiya! tana sake yin mini yadda ta ga dama ne saboda kina bin bayanta, kwalbar ha'kuri na ta kusa fashewa akan lamarinta". "Kai kuma haka za ka yi? mahaifinka mai ha'kuri ne akan sabgogin mata, kafin muga fishinsa mukan 'dade, duk yadda zan bata masa rai kuwa da zarar nace yi hakuri to maganar ta kare". Shiru ya yi! A ransa kuma sai cewa yake yi ba za ki gane mai yarinyar nan take mini ba ne, inda a iya kishin ne ai da sauki. A fili kuma ya ce "shikenan Hajiya ta ci albarkacin ki magana ta kwanta". " So nake ta mutu murus, ba wai ta kwanta ba". Ya yi dairya ya ce "ki mata fa'da, idan ta kwantar da hankalinta, magana ta wuce, amma idan tana tayar min da hankali ai dole laifin baya ya dinga tasowa, yana zama sabo". "Zan ja kunnenta sosai, amma ka ri'ke a ranka na kashe wannan matsalar, kaima ka kashe ta a ranka, sannan kar ka kuma zuwa cin abinci gurina idan kun yi fa'da, bana so! bana so". Ya amsa da "to sannan ya mata sallama ya tafi, yau har zaure ta taka shi tana cewa "ka zarce gida kai tsaye ka nuna mata na isa da kai." Ya amsa da fadin "To In sha Allah". Madallah da uwar miji irin Hajiyar Bichi, masu maida surukansu tamkar ya'yan su, suke musu adalci irin wadda ko wacce uwa take so ayiwa 'yarta. Gidan kuwa ya zarce, ya sameta a inda suka barta har lokacin kuma kukan ta ke yi, sai dai alamun sun nuna ta yi wankan duk da ba kwalliya ta yi ba. Ya tsaya a bakin 'kofar falon ya zuba mata ido yana jin takaicinta na kama shi sosai. A kausashe ya ce "Rashin mutuncin ki kullum 'kara tunbatsa take yi, ki mini cin mutunci, ki raina arzikina ki nuna mini bariki ya fi aurena, sannan ki zame ki kai 'karata, saboda kin koyi munafunci?" Ta kasa magana sai kukanta da ya 'karu. Shi kuwa ya zarce da fadin "Tunda kin zama macijiya ki sare ni, ki koma ki baibaye uwata da kalolin alherinki na makirci da tuggu, to Ina tabbatar miki nima daga yanzu kome kika mini sai na fadawa Baffa, su dinga raba 'bacin ran tare da Hajiya". Ya ja tsaki ya shige dakinsa. Ta jima tana zaune cikin rashin sanin abin yi, sannan ta tashi ta bi bayansa, cikin sa'a bai rufe 'dakin ba, yana zaune a bakin gado iskar fanka na kada shi. Akan gadon ta zauna kafadunsu na gogaiya da juna, ta ri'ko hannunsa tare da jingina kanta a kafadarsa murya ba amo tace"Am sorry Malam! Wallahi zuciyata ba za ta iya 'daukan fishinka irin haka ba, ka yafe mini' ka manta dan girman Allah". Ta karasa cikin kuka na sosai. "A hankali yace "Na ha'kura, amma mantawa sai a hankali, idan kin kiyaye, kin kuma rufe 'kofofin da zan dinga tunawa din! ki sani ba dan Hajiya ba, da ban san ranar da zan miki afuwa ba, saboda kin riga kin shayar da ni mamaki da ba'kin ciki mai yawa". "Na yarda na yi ba dai dai ba, dan Allah kar ka yanke mini kauna, ka sake bani dama". Ita da kanta ta yi dalilin da sai da suka hadu a lokacin, tun Mk na basarwa, har ya kasa cigaba da jarumtar ya ru'ko ta suka sami nutsuwa, haka nan sai da haduwar ta yi awon gaba da kaso hamsin na bacin ran da ke zuciyarsa. Tun a wannan rikicin Sa'adah ta fahimci ta rasa damammaki a gurin Mk, ya matu'kar rage rawar jiki akanta, ya daina tattauna halin da yake ciki da ita, haka nan baya zama ya shiririce mata da hirarrki kamar da, za su yi hirar amma

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});