Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 115

Chapter 115

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bugawa fiye da kima tana fargabar menene zai biyo bayan wannan zaman? Ta dinga jin takaicin kin shiga gaban motar, da ta shiga ai tasan shine dole zai ja motar, Kuma dolensa ya zauna iya kujerarsa sannan ya kula da tukinsa. Amma yanzu ya babbake har gefen jikinsu na gogar juna, gilashin motar irin na munafunci ne wato tint, ya matseta sosai tamkar su hudu ne a bayan motar. Ba'kin ciki ya isheta sai kawai ta fashe da matsanancin kuka mai sauti sosai, Mk ya yi tamkar bai ji ba, yayin da Mahmoud ya juyo da sauri tunda a tsaye suke traffic ya tsayar da su. "Menene kike yi haka Sa'adatu?" Zuciyarsa ta buga ganin yadda Rabin jikin Mk na jikinta, wani irin abu ya tsayawa Mahmoud da bai yi zaton zai ji ba, ya juya da sauri ya dauke fuskarsa yana ambaton innalillahi. Kukanta ya dinga tsuma Mk ya dinga jin tamkar ya danneta ko ya samu sau'kin halin da yake ciki. Ya lura fishi na fitar hankali take yi da shi, idan ya ce zai lalla'ba ta to ya kai shekara yana fama adalilin taurin kai irin nata. Ba zato Sa'a ta ji Mk ya ja uban tsaki mai tsayi, sai kuma ta ji yana cewa "Mahmoud saka mini wa'kar Auren Dole ta Ali jita". Dariya Mahmoud ya yi ya ce "bansan jita yayi wakar auren dole ba, ta aure mai da'di nasan ya yi" A gajarce Mk ya ce "to lalubo mini wadda zata dace da halin takurar da nake ciki, banda Hajiya da Baffa sun matsa mini, ina zan zo gurin wannan shugabar masu wula'kancin da niyyar wata magana, ai tun wulakantani da ta yi a ziyarar Jawad na gane idan ka shekara dubu baka mutum ba, kar ka tambaye shi komai binciki halinsa". Ya nisa ya sake jan tsaki ya ce " Ta tisa ni tana kukan gulma da iskanci, alhalin kasan ranta murna da farin-ciki ne fal, dan kuwa ban tsammaci zata iya barci ba, mafi yawa butulcin mace ke kaita wuta, abin da aka jima ana rokon ya tabbata ne, ya zo kuma sai a bude shafin iyashege, har da kuka kala kala tamkar wata yar yarinya alhalin gyara da kwalliya ne kawai domin ana kallon Jawad za'a gane ta tsufa". Wani irin daskarewa Sa'adah ta yi, wato Mk da rashin mutunci ya zo, ta tabbatar da hakan tunda a gaban Baffa ma ya yi mata diban karan mahaukaciya, amma ba laifinsa bane, Baffa ne ya bada ita, dama kuma ance naka ne yake bada kai. Duk yadda ta so shanye maganar Mk kasawa ta yi, ta yi jarumtar shanye kukan ta ce "duk tsufana dai ka girme ni, kuma ina rokonka ka koma ka fadawa wadda suka yi maka dolen aurena! na ce bana sonka, bana sha'awar zama da kai, domin wadda ya soni ina budurwa, yanzuma da na tsufa son nawa ya nan a tare da shi saboda ba sha'awata yake yi ba, idan kuma na so ma saurayi zan aura wadda ni zan cire masa samartakarsa fiye da yadda na ta'ba cirewa wasu". Ai bata karasa ba, ya shammaceta ya wawurota ya kama bakinta ya murde da karfin gaske, dan kansa ya saketa bayan ya tabbatar ta ji a jikinta. Jikinsa na rawa ya ce "wallahi idan baki kiyaye harshen ki a gabana ba, zaki sha wahala ai yanzu ke ba yarinya karama bace da zaki dinga mini kaifin harshe". Mahmoud kuwa da ya lura da abin da Mk yake yi ya kasa juyowa balle ya bude baki yayi magana saboda tamkar ya fashe da kuka haka yake ji. Kuka sosai Sa'adah take tana fadin idan yafi karfinta ai bai fi karfin ubangiji ba, ya fa'da mata bakar magana, dan ta rama shine zai mata wannan wulakancin? Har suka iso layin gidan Sumayya kuka sosai take yi, yayin da Mk ya biris tamkar bai ji ta ba, wani wula'kanci da Mahmoud ya yi mata, maimakon ya isa gidan sai ya samu gefe ya yi perking ya kunna musu a.c ya fice ya barsu, a kokarinsa na su dan sami daidaito shima kuma ya fita ya shaki isakar da zai dan samu sukunin zuciyarsa, da gaske da son Iyah zai mutu a ransa, wannan na cikin kaddararsa rashin cikar buri. Tsawon mintina Sa'a na kuka sosai, Mk da ya tabbatar ta yi shi ba ka'dan ba, ya santa da son a rarrasheta. Dan haka ya matsa sosai daga jikinta, ya yi gyaran murya ya ce " kukan ya isa haka My first love". Wani azabben kishi ya duro mata na ba zata, ta sake karfin kukanta tare da cewa "karka kuma cemin first love dinka, domin ni ba ita bace, kaima kasan ba ni bace. First love dinka tana can tana jiranka wacce ba zata tsufa ba tunda bata da kamar Jawad, Ni barni a makiyarka domin bansan komai da ka mini, kuma kake kan yi mini ba Sai kiyayyya da zalunci hadi da wulakanci". Jikin Mk ya yi sanyi ya ce da bakinki kika ce ban miki komai ba sai kiyayya da zalunci?". Da azama ta ce "kwarai kuwa! zan kuma rokeka ka koma ka fa'dawa Hajiya da Baffah su janye dolen da suka yi maka, domin ni ba sonka nake yi ba, ko ina sonka to na ha'kura, domin a yanzu sun nuna mini ka fini a gunsu tunda sai yanzu ne zasu maka dole,to ni kuwa ina tabbatar maka na wuce haka wallahi". Ya ce "Zan so kwarai mu fahimci juna, domin ni ban zo gurinki bisa ra'ayin wani ba, tsokanar ki nake yi, na gane ke ce cikon farin ciki na, ki zo mu rayu tare na sauran shekarun da ubangiji zai ara mana a gaba. kin san ina son ki, kin san ke kika mini laifi, na dauka ko wani kika ji ya ce na zalunce ki, zaki kare ni, amma fa'da mini me nayi miki na zalunci?" Ta yi shiru tana kuka kasa kasa, tana jin tamkar ta tashi ta yi ta rawa dan ta nunawa duniya irin farin cikin da kasan zuciyar ta yake ciki. Ta kasa cewa komai, ya nisa ya ce "Yanzu mu ba yara bane Sa'adah, ya kamata mu bar komai mu manta komai, mu gina sabuwar rayuwar da babu gillin bacin rai a ciki, ubangiji shine shaidata ba komai a zuciyata na yafe miki, na kuma manta komai". "Kema ki daure ki manta duk wani zaluncin da kike ganin na yi miki, ina tsananin son na rayu da ke my Sa'adah". Da kuka sosai ta ce "Ba haka bane a zuciyarka, kaima kasan ba haka bane, akwai dalilin da ya saka ka yafe mini amma ba dan kana sona ko dan kana son ka rayu da ni ba, daga ranar da ka jefe ni da mafi munin al'amari, a ranar na gane baka sona, wata kake so, kake neman hanyar da zaka rayu da ita, tunda ni amfani na ya kare a gurinka, ka riga ka dandana ni, shiyasa ka 'karanta tunaninka, ka kasa shaidata, ka kasa gane abin da zan yi da wadda ba zan yi ba, dama Kuma ai tun bamu yi aure ba, kake jifana da wannan zargin, yanzu kuma idan na koma maka ai cewa zaka

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});