Chapter 15
Chapter 15
ya tabbatar ba makarantar dan talaka ba ne, da bashi da ko mai da kowa sai Allah, shiyasa ya zaunar da ita yace, "Iyah kin san ni ba mai kudi ba ne, bani da halin sa ki a wannan makarantar, ki ci gaba da wadda ki ke yi, kin san dai, ko yanzu idan kin samu mijin da na yarda da nagartar shi auren ki zan yi. Shuru tayi amma a ranta tana jin ba 'karamin abin kunya ba ne ace ta sami damar shiga babbar makaranta irin wannan, amma ace ba ta tafi ba, ba ta san ma da wanne ida za ta kalli 'yan ajin na su ba, mussaman Zainab Salisu Ma'aji da su ke kusan unguwa 'daya, kuma ita ma taci makarantar tana da tabbacin za'a kai ta tunda ta na da yayye ma'aikata. Kasancewar ta mai tsananin tsabta da gayu sai ake mata kallon tamkar ta fito ne a gidan wadata, ita kuma ganin haka yasa ta yin alfahari mussaman da ba ta da makusa a halittar ta. 'Karfe takwas na dare ta dauki wayar innarta, ta shige 'dakin da ya ke mallakin ta ne, Yar uwarta Sumayya da a yanzu suke zaune a Jos babban birnin jahar Plateau da yaran su biyu Abba da Khalifa, ta shiga yi wa flashing, cikin 'kan'kanin lokaci ta biyo baya, tana 'daga kiran, ta sa mata kukan da ta kasa yi a gaban mahaifan nasu, jin kukanta ya matu'kar tada hankalin Sumayya, ta shiga tambayar ta menene, me ya same ki? jin yadda Sumayya ta 'daga murya a gigice ya janyo hankalin mijinta wadda ya ke kur'bar shayin da ta hada masa, cikin kukan ta fa'da mata yadda ta ci makaranta irin FGC KANO, amma kuma Baffan su ya ce ba shi da kudin sa ta a wannan makaran ta. Jim sumayya ta yi kafin ta ce "To ban da abin ki Iyah! Ba sai ki yi ha'kuri ba, kinsan dai nan duniya idan Baffa bai mi ki abu ba, bashi da hali ne, da girman ki da komai ki zauna ki na kuka, akan abin da ki ka san ba da gan gan aka 'ki miki ba?" Shesshkar kukan ta cigaba da yi, Sumayya ta sake cewa "kukan shagwaba ki ke yi Iyah! ni da ba a barni na gama ba fa? Turo baki ta yi kamar ta na ganin ta, tace "To ai ke yanzu maganar ki ta wuce, kuma gaskiya Aunty, ki dena cemin Iyah". da sauri Sumayya ta furta "Yi hakuri Anty Sa'adatu" 'Dan murmushi ta yi hade da jan majina, sannan ta ce"Ina su Abba? Sumayya ta ce "gasu can sun yi barci sun gaji" A haka Sumayya ta lalla'ba 'kanwar ta har sai da ta yi dariya sannan su ka yi sallama, amma Sumayya ta dinga jin jina halin kanwarta na yadda ta ke kai kanta inda Allah bai kai ta ba. Mijin Sumayya da ya fahimci maganar su, sai ya 'kudure abu a ranshi amma bai mata maganar ba, kamar yadda bata sa shi cikin maganar su ba, idan akwai abin da ya ke 'kara mata 'kima to rashin hayaniyar ta da 'karancin buri ne, da wahalar gaske ta bude baki ta ro'ke shi wani abu kai shi zai iya cewa bata ta'ba ba. Abin da ya mata shike nan, sai shi ne da ya fahimci halin ta, sai yake yawan kyautata wa iyayenta, mussaman da ya fahimci suna bu'katar taimakon amma halin su, na wadatar zuci da rik'e girma, basu ta'ba nunawa ba, bare a gane. Kwanaki uku a 'tsakani ya tura ku'di masu yawa ta hannun amintaccen amininshi akan ya je ya kai wa surakin nasa, ayi wa Sa'adatu hidimar makaranta, wadda da 'kyar Malam Basiru ya karba. Ya 'kira Sumayya ya ma ta fa'da akan mai za ta 'dorawa mijin ta nauyin da ba nashi ba? Rantsuwa ta dinga yi akan ita bata fa'da masa ba, sai dai idan ya ji sadda suka yi waya da Iyah ne, sannan kuma bai fa'da mata, zai yi wani abin ba. Yace to " Ki masa godiya kudi masu yawa ya aiko, ki kuma 'kara masa biyayya, ki 'kara ha'kuri dashi" Shikenan sai aka fara shirye shiryen shigar ta makarantar har komai ya kammala. Ana cikin Shirye shiryen sai ga Baffa yazo da dimemiyar katifar yan makaranta har da filo dukkan su(Vitafoam)ne,da kuma bargo duniyar kule amma 'karamin size, sabo dal a cikin jakar shi. Da mamaki Inna ta hau duba katifar ta na fadin "wannan katifar ai ta yan makaranta ce". Sai da ya zauna akan tabarmar da aka shimfida domin shi sannan yace "Wallahi Salamatu wani yaro ne muke gaisawa da shi,tun ba yanzu ba, 'dan gaban tireda ta yake da shago, kullum yazo sai ya gaishe ni, a haka muka yi sabo na gaske. Yau kwanaki uku na fada mishi yarinyar waje na ta ci babbar makarantar gwamnatin tarayya. Bawan Allah sai ya zaci ta kwana ce, ashe wai akwai bangaren ta kwana (boarding), akwai ta je ka ka dawo(day)". Ya numfasa ya dauki kofin ruwan da aka ajiye mishi ya sha, sannan ya 'dora da cewa "Sai ganinsa na yi 'dazu da katifar nan, wai ya kawowa 'yar makaranta, nace kai ma ka na fama da kan ka, ya za ka takura kanka"? Tunda dalibi ne a jami'ar Bayaro, yace min yana shekarar 'karshe, na'ki karba tare da nuna masa ita ba ta kwana ta ci ba, dan haka ya mayar ya amshi kudinsa, nan ya rantse ba zai koma da ita ba, tunda ya riga ya siya, ya kuma yi niyya, abata ta dinga kwana a kai. Kuma abin mamaki har da ku'di wai a siyi littafai" Sai lokacin Inna tace "oh mukam mun gode Allah, Allah ya saka masa da alheri, Allah ya sanya alheri da farin ciki a rayuwarsa". Take kuma ya ce "Iya zo ki dauki katifar nan da bargon nan naki ne, wani yaron arzi'ki ne ya baki, sai ki sa shi cikin adu'oi'n ki". Da murna ta ja katifar tana fadin Nagode Allah ya saka da alheri. "Ya sunansa Baffah?" "Sunansa Muuktar amma ni Mutari na ke ce mishi ya kuma amsa ci ke da girmamawa". Inna ma ta bi sahun Iyah a wurin murna tana sake dauko sabbin addu'a, "Madallah da wannan yaro, Allah ya bashi ilimi mai amfani,ya bashi mace ta gari". Da ga Iyah har Baffan suka hau rige rigen amsawa da Amin. Inna ta sake cewa "sunan shi mai da'di amma ka ke ce masa Mutari? Ni kam Muutar zance" Suka sa mata dariya, Sa'adah na cewa ai ko dai Inna gara ma ki ce Mutarin. A daren ranar ta fito da yar tsohuwar katifar ta, da ta zama tamkar tsumma, ta shimfi'da sabuwa cike da zumudi, a ranta tana ta kwararawa wadda ya siyi katifar fatan alheri. Shigar ta makarantar sai ya 'kara mata girman buri, saboda yadda ta hadu da 'kawaye fe'kak'ku wadda suka fita rawar kai da waye wa. Kusan dukkan daliban makarantar ya'yan masu dashi ne, ko kuma na ma'aikatan gwamnatin da suke daraja ilimi. Arts Class ta zaba a burinta na son zama Barista, ba'a kammala farkon zangon karatu ba (first term) sai da sabo da sha'kuwa ta shiga tsakanin ta da Halima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157