Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wannan dogon zaman a waje ba, tana gida ita kadai. Haka suka ci gaba da cin amarci ba kakkautawa cike da soyayya da kulawa, tun Sa'adah na jin zafi da tsoron haduwarsu har ta saba ta fara fahimtar dadi da nutsuwar dake cikin haduwar. ```Alkalamin *Surayya Dee*. ``✍🏼✍🏼 [6/5, 14:08] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Fatan alheri ga Amare* *Hafsa Sani Abubakar* *Halima Sani Abubakar* _Ubangiji ya albarkaci auren ku, ya Baku zuri'a mai albarka_. 53-54. *BAYAN SATI SHIDA* Zuwa wannan lokacin, sabo da shakuwa mai karfi sun shiga tsakanin ma'auratan biyu, soyayya da aminci sun sami wajen zama a gidansu, kowa kokarin kyautatawa dan uwansa yake yi. MK ya dauki soyayyar duniya ya dora akan Sa'adah da da hali kirjinsa zai bude ya cusa ta, saboda yadda ya ke jin ta a zuciyarsa, musamman yadda ba ta gajiya da bukatunsa. Duk da dai ya gane ita ma mabukaciyar ce ta gaske ga tsafta ga iya sarrafa girkin gargajiya, saboda ire-iren su aka fi yi a gidansu. Babban abin da ya ke gigita shi a kanta, shagwaba da iya kwalliya, kullum sabuwa take zama a idonsa, kullum da sabon abin da zai gani a tare da ita, babban abin birgewa ta kama dukkan ahalinsa ta ri'ke da hannu biyu, ta zama yar gida a gidansu, akai-akai take kiran Hajiya Babba da Hajiyar Bichi tana gaishe su. Sun zo sau daya sun ga gida, da amarya. Tana kokari sosai wurin yin abinci akai gidan su Mk mussaman masar Bauchi da miyar ganye, da kuma Dambu. Kasancewar mahaifiyar ta daga Bauchin take, sosai ta iya masar Bauchi. Kullum yana gida, hatta FGC Kano ma ya daina zuwa, shago kuma sai Azahar yake fita, da zarar karfe biyar ta yi zai juyo ya bar su Abbas da kula da wurin, Mahmoud ya masa tsiya ya gaji. Shi kansa Mahmoud din tunda ya je ya ci girkin amarya, dambun shinkafa ta yi musu da ferfesun naman rago, sai kunun aya bai sake yi wa MK tsiyar ya zama bita-zai-zai ba, musamman yadda kamshin turaren gafgaf da kajiji ya kama gidan gaba'daya, dole idan mutum ya yi katarin samun irin su Sa'adatu ya manne musu ya kasa fita ko ina. A wannan tsukun ASUU ta janye yajin aikin da ta ke yi, a kuma lokacin aka tabbatar da MK da Mahmoud da sauran da suka yi sa'ar samun koyarwa a Jami'ar Bayero takarda shedar fara aiki. Ranar da ya fara fita aikin dukkansu sun galaibaita, sati shida kullum suna manne da juna, ko fita ya yi Allah-Allah yake ya dawo. Don haka yanzu ma da zarar ya ga yana da tazarar lokaci, sai ya dawo gida ya ci abinci, ya yi abin da zai yi, sai kuma ya yi wanka ya koma, idan kuma ba shi da sauran darasi shike nan sai ya yi zamansa gurin amaryar sa. Watannin su biyu da aure Sa'adah ta tsiri fushin da babu dalili, share shi take yi, ta daina hira da shi daga eh sai um um, ta rage walwala idan yana gidan, idan tana falo ya zauna, sai ta san yadda ta yi ta bar falon, haka nan daki. Ba ta gudunsa, amma shi kadai zai yi kidansa yayi rawarsa, babu gudunmawa daga gare ta. Wannan canjin ya matu'kar 'daga masa hankali ya yi tambayar duniya tace ba komai, kuma lafiyar ta 'kalau. Rannan da daddare ya dawo da ga Masallaci, jikinsa a sanyaye ya zauna kusa da sallayar da ta ke sallah ya jira ta idar. Tana ganinsa ta yi kamar ba ta gan shi ba ta fara kokarin tashi a gurin ya kira sunanta a kaurare. "Sa'adah zauna magana za mu yi". Ba ta 'ki ba, ta koma ta zauna amma fuskar nan a 'daure, sannan ta juyar da kanta gefe, ta ki kallon inda ya ke. "Na tambaye ki mene ne yake faruwa kin ce mini ba komai amma kuma kin canja mini, kin tayar mini da hankali, wallahi da kinsan yadda nake ji a zuciyata da kin tausaya mini cikin kwanakin ukun nan. Shiru ta yi, tamkar ba da ita yake ba, ya matsa ya riko hannunta, ta fizge tare da zura su cikin hijab, wata irin fargaba ta kama shi, bakinsa har rawa yake yi ya ce "Har abin ya kai mu ga haka, laifi na yi ke nan?" Nan ma shiru ta sake yi. "Don Allah Sa'adah me na yi miki? Ki fada mini, ba ni za ki duba ba, Allah na hada ki da shi". Jikinta ya yi sanyi sosai, ta kasa cewa komai sai da ya sake rokon ta sannan ta bude baki ta ce, "Ni gaskiya zaman ne ba zan iya ci gaba da yi ba, na gaji". Gabansa ya yanke ya fa'di. Murya ba amo ya ce "Me na yi miki?" Shiru ta yi, hankalinsa ya yi mugun tashi ya fara fa'din, "Ban miki komai ba fa Sa'adah, don Allah idan wasa kike mini ki bari bana so". Yana rufe baki ta ce " "Wallahi ba wasa na ke yi ba, zaman ya isa haka nan". Ya tsura mata ido tsawon lokaci ba kakkautawa yana nazarinta, ya lura da gaske take yi, bugun kirjinsa ya karu, gumi ya fara karyo masa, jikinsa na bari ya ri'ke kafadunta da karfi, ya ce "Kar ki mini haka Sa'adah don Allah, ina sonki fiye da kaina, fada mini inda na gaza, me na ke yi wanda ba kya so?" Ta yi shiru amma fuskar nan a daure tamkar hadari, hannunta ya ruko da karfi ya dora a kan kirjinsa ta ji yadda zuciyarsa take bugawa da sauri. "Kin ji yadda zuciyata ta ke bugawa, tun daga ranar da kika canja mini Sa'adah har yanzu ban huta daga wannan bugun ba, ya sake matsarta sosai ya ce "Ko aikina ne ba kya so? Idan shi ne sai na je na ajiye musu". "Ni ban ce ba, idan ba ka yi aiki ba 'kasa za ka ci?" "Me yasa kika cire kanki, da gaske za ki iya rabuwa da ni?" "E mana indai zan tsira da mutunci na." Kansa ya kulle ainun ya kasa gane me take nufi. "Ban gane idan za ki tsira da mutunci ba?" Ta zumbura baki ta ce "Kai ba Bahaushe ba ne?" Ransa ya fara 'baci, ya kalle ta cike da bacin rai ya ce "Kar ki fara Sa'adatu, kar ki fara mini rashin kunya ba zan 'dauka ba". Ya mike ya fice da ga falon ya nufi dakinsa. Zuciyarta sai rawa take yi, ita kanta jarumta take yi, ta kuma riga ta kudire sai ya janye waccan kalmar da ya jefe ta da ita, amma ta lura ransa ya baci sosai don ta fahimci indai ya ce mata Sa'adatu to ransa ya baci da ita ne. Da kyar ta tashi ta yi

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});