Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 114

Chapter 114

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

assalatu da ta ji Anayi a masallaci. Ta tashi duk jikinta a jike tsabar fargaba da rudu, ta mike a hankali tana neman tsari da samun shege a cikin zuri'arta. Yammaci sosai kafin Sa'a ta shirya ta fito da Shirin tafiya gidan Sumayya. A tsakar gidan ta sami Inna, ta ce "Inna zan tafi". Ta daga ido ta kalleta ta ce "Ince sai wani satin kike da zama a kotu?" "A a Gobe ne Innah". "To ki gaishe da Yayar ta ki, sannan ki fa'da mata lalle ta sake taya mu da addu'a". Har Sa'adah ta kusa kaiwa zaure Inna ta dawo da ita, ta zaunar da ita ta fa'da mata komai na mafarkin da ta yi, ta rufe da cewa "Dan haka ki nisanci Muutar. Kunya ta kama Sa'adah amma ta daure ta ce "in Sha Allah hakan ba zata faru ba ubangiji ba zai kunyata ku ba Inna". Sa'adah na aiki da (supreme Court) ta court road. Watan jiya Alh Mamman ya kawo mata (upper) takardar samun aiki har gida, wadda wannan na cikin abin da ya sake dagulawa Mk lissafi, domin kuwa a bakin Ahamad yà ji Sa'a ta samu aiki, duk da tafi zaman gidan Sumayya adalilin daga gandu zuwa court road ba nisa. Ya fi mata sau'kin zuwa. A bincikensa ya gano Alh Mamman ne ya samo aikin, ya dinga jin takaici yana kallon Alh Mamman a matsayin a karambana, da ga fitowarta a makaranta sai ka nemo mata aiki? Tamkar ance masa ana bu'katar hakan, kai dattijan mazan nan wuyar sha'anine da su idan suna son Yar yarinya. Ko kunya ba ya ji, zai dage yana son Sa'adah alhalin yana da 'dan da yake sa'anta ne. A fili Mk ya ja tsaki ya ce "zanga yadda za'ayi ka mallaketa shekaru da yawa ka kasa rabuwa da ita, tamkar ita ka'daice yarinyar mace bayan ga yanmata nan masu shekaru irin na ta". Ya sake jan dogon tsaki yana cewa "Halima tana nan har yau a kasa ta ke da gudu zata soka, amma wannan kam a yanzu ma ba samunta zaka yi ba". sai dai a zuciyar sa ya tabbatar son gaskiya Alh Mamman ya ke yi mata, wani irin abu mai nauyi ya danne shi a zuciya, wadda shi ya damalmala masa lissafi har ya ji ba zai sami nutsuwa ba, idan ba shiryawa ya yi da ita ba, ya lura ba zai ta'ba iya jarumtar wani ya aureta alhalin yana da rai ba. A zaure ta tarar da Baffa da Mk da kuma Mahmoud a zaune kan tabarma suna tattaunawa, sai da zuciyarta ta buga tunda ta ganshi da Mahmoud lah shakka maganar kome ya zo yi, a ranta ta dinga jinjina rashin ta ido a gurin namiji, yanzu da yake son komen ya na'de kafar wando zai nemi komenta duk yadda ya jingineta shekaru bakwai, Anya kuwa Mk yana da adalci a yanzu? A ladabce ta ce "Baffa sannu da yammaci, zan tafi, sai wani satin Kuma". Da wani irin farin ciki ya amsa mata da fa'din "To ki gaishe su, ki kula da kanki, Allah ya tsare". Ta amsa da cewa "Ameen". Ta kalli 'Karfi ta ce " Baban Dadi barka da yamma ya iyali?" Ya amsa ta saka kai ta fice bata ko kalli inda Mk yake ba, bare ta gaishe shi ko da gaisuwar da zai raina ne. Ran Baffa ba karamin baci ya yi da abin da ta yi ba, ta ganshi da ba'ki, ta gaishe da 'daya, ta wulakanta 'daya, idan dai da gaske bata son Mutari a yanzu menene zaisa ba zata gaishe shi ba? "Iyah" Baffah yasa baki ya kirata da karfi, ta dawo tana cewa "Ga ni Baffah"! "Me yasa kika gaishe ni, Me yasa baki wuce kanki tsaye ba? Ai na yi zaton ko da rago Ki ka ganni zaki tsaya ki tambayi lafiyarsa saboda ya shiga rigata, akan idona ki yiwa Mutari wannan wulakancin? Amma ba komai ai ni kika yiwa ba shi ba, Na gode miki je ki, yi tafiyar ki". Ta kasa tafiya, ta yi sukuri tana jin takaici na kamata, hawaye ya balle mata, Mk yana kallonta ta gefen ido, yana ganin yadda ta turo baki gaba, sai ya dinga jin wani irin tsumi na tsumashi, abubuwa masu yawa akanta suka dinga bijiro masa, ya dinga jin wani irin abu na taso masa. A hankali, kuma cikin bacin rai ta ce " Mutarin Baffah ina yini?" Dariya ta kwacewa Mahmoud ya dinga kyaykatawa Baffa kuwa ya gintse tasa dariyar ya dubi Mk da ya hade girar sama da ta kasa kuma bai amsa ba, hakan da ya yi ya sake hassalo da Sa'a. Baffah ya cije ya ce "Yanzu kuma laifinka ne ta gaisheka baka amsa ba, tunda hakane sai ka tashi ka kaita, ai bazai yiwu ka sace mata iska a banza ba, dole ka hutar da ita tsayuwar jiran mai adaidaita sahu dama kuma garin hadarine sossai". Mahmoud ya yi maza ya ce "To Baffa bari mu kaita mu dawo, mun gode Allah ya kara girma". Baffah ya shige gida ya barsu a zauren Sa'a ta na jin tamkar ta yi ta zunduma ihu. Hawaye ya dinga tsere a idonta, wannan irin bada ita da Baffa ya yi? Duk wula'kancin da Mk ya mata wato Baffah bai ga laifinsa ba, daga zuwa da magana zaice ta shiga motarsa ya kaita a matsayinsa nawa din ta? Zauciyarta ta kuntata sosai tana jin gara ta tafi da kafa a kan ta shiga motar Mk. Har suka fita kofar gida kuka take marar sauti, Mahmoud ya bude mata gaban motar, ta cije, a hankali ya ce "a titi muke fa, sannan umarnin Baffa zaki bi, ba son ranki ba" . "Akan me za'a tilas ni shiga motarsa,?" Ta fa'da cikin rishin kuka. "Yi ha'kuri ai dukkan mu umarnin Baffa zamu yi wa biyayya akan kunnen ki dai ya hukunta Mk ta hanyar mayar da shi dureban ki, adalilin amsa gaisuwar ki da bai yi ba. Kina kallon bai yi musu ba sai ke?" Hawaye ya zubo mata ta ce "Ni na yafe masa zan tafi da kaina". Mahmoud ya ce "Ai tunda Kika bari Baffa ya shige cikin gida dolen Mukhtar ya miki direba kar ki yadda ki sab'awa mahaifin ki adalilin wani Mukhtar". Take Sa'adah ta gane gaskiyar Mahmoud ne, tunda rashin gaisuwar da bata yi bane ya janyo mata wannan hukuncin mai kama da saukar aradu. Maimakon ta shiga gaba inda Mahmoud ya bude mata sai kawai ta bude baya ta shiga. Da azama Mahmoud ya isa setin direba Mk ya juya musu baya tamkar baya wurin hakan da ya yi ya sake tunzura Sa'a tun fil'azal ta tsani a nuna mata rashin kulawa. Mukullin hannun Mk Mahmoud ya karba, a hankali ya ce "shiga baya mu je". Ba musu Mk ya bude bayan motar ya zauna, Yana rufewa Mahmoud ya ja motar. Zuciyar Iyah tamkar ta fa'do kasa dan tsananin ba'kin ciki mussaman da ta tuno irin addu'ar da dinga yi, tun bayan da ya auri Farida na kar Allah ya sake ha'data ko da zaman mota ne da Mukhtar balle kuma zaman aure, sai gashi karon farko da zaman motar aka sake ha'dasu, zuciyar ta dinga

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});