Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

lokacin kuma zuwa take ta dauketa acan zata wuni sai dare take kawota a mota dan basa bin hanya da ita duk da da nisan da sai anshiga motar. Wata daya da sati biyu suka dauka kafin tafiyar ta kammalu suka tsayar da rabar tafiya. Mama Kallan Sayyid tayi ranar da zasu tafin tana rungume da Baby Fatima ta zuba masa ido tana kasa iya cewa komai sbd batama san me zata fadan ba. Baby fatima ya kalla kafin ya kalli maman yana bude baki Ahankali yace "Mama nai miki Alqawarin zan dawo miki da ABDULAZIZ LIMBA a gabanki ko a yaya yake insha Allah sannan zan kula dashi fiyeda nawa kan" Numfashinta ta hidiye cikin sanyi da samun dan sanyi a ranta tace "Allah ya tsareku gaba daya ya dawo daku lfy yasa shima yana lafiyar" Alh Saad ta kalla cikin mutuntawa da kulawa tace ta gode. Baba alhassan ma addua yayi musu yana yiwa Alh Saad godia. Mota suka shiga drivern gidan Alh Saad dinne zai kaisu Airport su mama na kallo motarsu ta fice daga gidan. Ajiyar zuciya Baba Alhassan ya sauke ita kuma Mama kasa sauke ajiyar zuciyar tayi ta juya ciki tana sake rufe Fatima dake bacci a jikinta tana dan motsawa ahankali. Tinda suka isa airport Alh Saad ya kalli Sayyid wanda kai tsaye kallo daya zakai masa kasan ya sauya daga asalin Sayyid dinsa na baya idan ka sansa. Har a cikin jirgi bayan sun zauna babu walwala a tattareda Sayyid din dan haka bai takurasa ba ya kyalesa dan yasan zuciyarce ba dadi ko kadan. ****** Lafiyayyan toilet ne dayake da girma sosai komai a tsare, Qamshi ne me sanyin dadi da nutsuwa yake tashi a cikinsa hakama da dan hayaqin zafin ruwan da ake wanka dasu dayake dan gauraya toilet din yana saka koina a toilet din daukan dumi ahankali. Wanka takeyi a natse qamshin shower gel dinta me kyau da tsada yana sake tashi harta gama wankan ta kashe shower din tareda miqa hann ta janyo towel ta dauro a jikinta ta fito cikin Lafiyayyar jacuzzi din ta nufo gaban mirror daya kusan cike rabin bangon toilet din ta tsaya cak ta zubawa kanta idanuwanta da suka fara sauyawa ahankali. Hannunta na dama ta dago ahankali ta dora akan kirjinta seti da zuciyarta dake bugawa ahankali cikin cikakkiyar lafiya.. Tabon dinkin gurin ta shafa ahankali tareda lumshe fararen kyawawan idanuwanta tana sauke numfashi ahankali me dumi... Tin daga lokacinda ta wayi gari ta samu kanta a sabuwar rayuwa daukeda sabuwar zuciyar datake bugawa a kirjinta tasan duniyarta ta sauya ta dawo sabuwa a daidai lokacinda ta cire rai da rayuwa gabaki dayanta, Allah ya bata damar cigaba da rayuwa a lokacinda take saka ran ta farko ta samu kanta a duniyar barzahu, Duk wanda zuciyarsa take bugawa a kirjinta tana masa fatar samun rahamar ubangiji dashi da danginsa a duk inda suke, Harta bar duniya bazata dena yi masa addua ba sbd sadaukarwansa gareta. Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana lumshe idanuwanta tana sake jin bugun zuciyar wadda take tata ayanzu yana ratsata cikeda shauqi da samun nutsuwa da yanayin da bata saniba a baya na bugawar Lafiyayyar zuciya a kirjinta. Ayau kusan wata hudu da kwanaki kenan da aikinta amma haryanzu ta kasa sabawa da sabuwar rayuwar data samun koyaushe jinta takeyi kamar sabuwar mutum sedai kauna da tsananin son datakewa yan uwanta familynta babu abinda ya sauya saima qaruwa da yayi sbd jajirwansu gareta. Kaman yanda samun lafiyarta ya sauya rayuwarsu gaba daya a qanqanin lokaci sbd sabon farin ciki da jin dadine tareda sabuwar rayuwa ta dawo musu sabuwa dan haka komai nasu ya dawo tamkar baya kusan ma fiye dan farin ciki da kwanciyar hankalin dasuke dashi yanzu na tafiyar da komai yafi na bayan. Ta jima a tsaye kafin ta juya ta fito toilet din. Qamshin dayake tashi a bedroom din nata ne ya shiga hancinta ta dan Lumshe ido tana jinsa yana ratsata sbd komai a yanzu jinsa take kamar sabo gareta. Gaban mirror ta nufa bayan ta zaro wani towel din tana goge jikinta a hankali kamar batason taba soft fatarta sosai. Da kanta ayau ta shirya kanta sabanin tinda suka gama jinya a asibiti suka dawo gida Mimi ke tayata shiri sbd batason tayi aiki da jikinta ta gaji sbd sun saba a lokacin ciwonta abu daya takeyi zuwa biyu ta gaji sosai ba kuzari. Body milk me kyau da qamshi ta shafa tareda Turare mai sanyin qamshi ta miqe ta nufi closet nata ta saka undies kafin ta saka oversize skirt and shirt na Liliana ta saka hula me laushi da rashin nauyi a kanta ta fito da slippers a kafarta sbd yunwa takeji abinci take buqata. Anty Anny ce ta nufo palon itama sanye da shaking doguwar riga mara adon komai sai kudi tana qamshi fuskanta fresh dan itama gaba daya yinin ranar bata fito daga bedroom ma bare palonsu harta fito zuwa nan sai yanzu data fito neman abincin da zata dan duk da a familyn kowa da nasa bangaren amma a hade suke guri daya babu wani rarrabewa sosai dan kusan duka a guri daya suke kowa baifi kayi tafiyar corridor ba zuwa palo da bedrooms wani hakama duk yanda kowa yake bangarensa a tare ake cin abinci dining room dinsu daya ne hakama chiefs dinsu da masu aikin. Rayuwar hutu kawai sukeyi mazan gidan ne suke fita aiki suma bawai sammakoba tinda sune masu companies dinsu amma matan kuwa da saleem ma sai lokacinda suka ga dama suke fitowa idanma ba abinci zasuci ba saika wuni a gidan bakaga ko dayansuba sai idan dare yayi ake taruwa babban palon ayita fira da yar hayaniya cikin walwala. Anny na ganin Jannah ta zuba mata idanuwanta tana kallan yanda take sake warwarewa tana komawa lafiyayyar jannah dinta wadda ita bata saniba a baya, Wani irin sirrin kyau da kwarjini ne da itama duk da bata gama zama cikakkiyar budurwar data amsa sunanta budurwanba amma haka kawai wani lokacin sai take mamakin saa irinta jannah din kowa sonta yake, Babu abinda ta nema ta rasa, Kowa zai iya komai dan bata abinda takeso, A irin wannan gatan da Jannah din take ciki me zata nema a duniyar nan ta rasa? Duk yanda familyn suke ganin babu abinda bazasu samar mata indai har tanaso akwai abinda yafi karfinsu shine ikon Allah, Ita kanta zataso Allah ya kawo abinda Jannah zataso fiyeda komai ko buqata fiyema da zuciyar da aka dauki rayuka da dama akanta amma kaf familyn babu wanda zai bata kuma dukiyarsu bazata taba iya siya musu ba, Zataso taga wannan ranar sedai batajin tana zuwa dan raine kadai bazasu iya siya mata amma ko rai din da zaace musu ana iya sakawa wani ran wani to tabbas zasu iya sedai Allah bai bada damar hakanba. Isowan Jannah gabanta ya sakata sake murmushi tana sake kallan Jannah da yanayi na tinani kala kala akan fatan zuwan ranar da jannah zata dandana rashin ba komai ake nema a samu ba. Da murmushi a fuskanta da kulawa tace "Hey Jan sai yanzu kike fitowa? Yaya jikinki? Ya kikeji yanzu? Karki manta duk abinda kikaji ba daidaiba ki sanar" Fararen idanuwanta ta kalli

Table of Contents

Chapters

163 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});