Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

aminta da hakan ya sakasa kallan Ammar shi da Dad a tare sbd sanin shine mai juyewan kai idan wannan lamarin ya taso kwata kwata bayaji baya gani kawai abu daya ya sani shine karban kalbim kota waye ba ruwansa. Dad ne ya bude baki a natse yace "Ammar abari ayi hakan sbd tafiyar da komai batareda garaje ba ko dan ita jannah din hakama aikin nutsuwar da kwanciyar hankalin zaifi, Tinda aka riga aka sameta duk inda zata shiga bazata gujewa abinda yake jiranta ba sbd yanzu zuciyar Jannah ce kai tsaye take bugawa a kirjinta babu abinda zai hana jannah mallakar wannan zuciyar me bugawa." Numfashi me zafi da damuwa Ammar ya sake kafin yaji ya aminta da hakan dan haka zasu saka masu bibiyar yarinyar da bincike sosai akanta duk da babu ruwansu ba abinda ya shafesu da inda ta fito kokuma wace ita waye danginta. ******ASALIN LABARIN/SHEKARUN DA BAYA. PROF ZAHARADDEN ZAADEN shine asalin mahaifin Yayansu uku biyu maza sai mace daya wadda yayunta mazan ke tsananin kauna sbd mahaifiyarsu ta rasu a hannun matar mahaifinsu suka taso, Prof dan bokon gaske ne wanda ilimin bokon dana addinin suka shigesa sosai hakama yanada arziki sosai wanda ya dade sa barin qasar yana malaysia acan yake zaune da iyalinsa gabaki dayansu. BOUKHAR Zadeen shine babba sai MAHMOUD Zadeen tukuna qanwarsu ZAYNEB, Matar Mahaifin nasu bata taba haihuwa dashi ba dan haka su kadaine yayansa wanda suka girma kowannensu ya zama babban mutum, A malaysia suka taso acan sukai karatu sai daga baya dukkaninsu su ukun suka dawo Nigeria tareda mahaifin nasu wansa tsufa yazo masa sosai. Bayan tsawon shekaru Anyiwa Zeynab aure da wani prof itama a porthacort, BOUKHAR da MAHMOUD kuwa kowannensu na qasa daban gurin karatu, Mahmoud ya riga boukar aure kuma daga mahmoud din har zayneb babu wanda ya samu haihuwa a cikinsu har saida Boukhar yayi aure shine ya fara haihuwa a cikinsu. Familyn ZADEEN's din sunada wani irin tarin arzikin dayake da yawan gaske da basuma san ya zasuyi dashi ba, Bayan arzikin mahaifinsu prof me tarin yawa su kansu sun tara na kansu me yawan gaske dan kuwa ko Zaynab datake mace a cikinsu itama tanada nata arzikin sosai. Suna tsananin son junansu wanda hakan ya saka iyalansu ma kansu yake a matiqar hade duk da su ukun gaba daya basa qasa daya. Mahir shine babban dan Boukhar zadeen wanda ya haifesa a Greece, Bayan haihuwar Boukhar Prof ya rasu wanda hakan ya saka dukkaninsu tattarowa suka dawo Nigeria. Mahaifinsu nada kadarori sosai wanda bazasu iya gama hadasu lokaci daya ba dan haka mahmoud ne kadai ya koma boukar kuwa dole ya zauna Nigeria tareda iyalansa. Umma matar mahaifinsu wadda ta riqesu tamkar yayan data haifa ba cuta ba cutarwa hannun Boukhar ta dawo dan yayansu ma basusan cewan ba itace ta haifi iyayensu ba sbd kulawa da kaunar dake tsakaninsu ta uwa da yayanta. Mahir nada shekara biyar a duniya Zayneb ta samu ciki wanda yazo mata da matsala sosai sbd manyanci da dadewan datai bata haihun ba. Cikinta na sake gaba girman matsalarta na qaruwa wanda daga baya aka gano tanada heart diseases wanda basu taba sani ba. Hankalin familyn ya tashi sosai wanda ya sakasu dawowa da ita hannunsu aka fara neman mata lafiya. Lokacinda aka gama bincike sosai akan ciwon nata aka gano tana buqatan heart transplant maana dashen zuciya. Hankalinsu ya tashi sosai sbd ciwon nata bawai sbd zuciyar da zaa nema dinba sbd ganin sukeyi sunada dukiyar da zasu iya siyan mutum gaba dayansa su cire abinda sukeso a jikinsa. Cikinta na kaiwa wata tara suka tattara gaba daya familyn suka koma Greece sbd haihuwarta da basa fatan matsala komai kankantarta. Tin daga kan ummah da zayneb din da boukar da matarsa da mahir da mahmoud ma acan ya samesu da fmlynsa suka dawo zama. Cs akaiwa zayneb aka ciro mata Baby boy wanda Boukhar ne ya saka masa suna Ammar sbd har lokacin mijinta bai taho ba yana porthacort da matarsa daya dan haka suka suka tattara suka watsar. Tinda zayneb ta haifi Ammar bata sake lafiya ba sai ramewa takeyi tana wani irin hasken daya saka hankalin duk wanda yake familyn nasu tasu musamman yayun nata wainda suka ringa nema mata donors tako ina amma babu inda aka samu, Sassaucin da suke samu a zuciyoyinsu shine likitoci sun tabbatar musu da akwai sauran time sosai kafin zuciyar ta gaza gaba daya dan haka suka ringa zubarda dukiya qasa qasa suna neman donor. Ammar kuwa kusan Mimi ce mahaifiyar mahir matar Boukhar din ta renesa tin daga ranar da aka haifesa itace ta zama uwarsa dan ko nonon mahaifiyarsa baisha na wata biyar ba wata hudu aka ciresa daga nonon sbd bazata iyaba ta bushe sosai. Duk wannan ciwon da haihuwar mijin zayneb din baizo yaga matarsa da dansa ba sai so daya dan haka su kuma basajin zasu taba basa ita ta koma bare Ammar da sukejinsa fiyeda komai sbd tsananin kaunar da sukewa kanwarsu. Ammar tinda ya taso ya samu mahaifiyarsa a cikin mummunan hali harya fara girma a hakan yake ganinta wanda hakan ya taba zuciya da kusan lafiyarsa dan kuwa yanada qawa zucin mahaifiyarsa sosai musammam daya fahimci baida uba bayan Boukhar wanda Suke kira da Dad Zad sai Daddy mahmoud wanda takanas ya bude babbar asibiti sbd ciwon Zayneb kawai dan samun donors. Mommah zayneb tinda ta haihu ta cire rai daga rayuwa sbd yanda takejin ita kadaice ta sani a hakan tana dauriya ne sbd ragewa yan uwanta damuwa da 'danta wanda ya sakata aransa sosai fiyeda komai. Sbd ciwon zayneb Boukhar da Ammar da mahmoud saida suka koma abin tausayi duk girman arzikinsu, Ummah kuwa babu ranar da bata kuka idan ta kalli yanda zayneb ta koma, Mimi kuwa sosai itama ta tashi akan Ammar sbd saida ya zama traumatised kwata kwata baya gane karatun komai a school duk da mahir yana kokari sosai akan dan uwan nasa amma saida teachers suka gano suka bada shawarar Ammar din ya fara ganin likita. Ana cikin hakan ne Mimi ta samu ciki wanda itama ta fara shiga matsalar rashin lafiya me nauyi sbd ga cikin dayazo da ciwo ga lalurar Ammar ga kuma ta familyn da kowa yake cikin damuwa da qunci. a wannan lokacin ZAADENs suka shiga matsanancin halin damuwa da qunci, Gasu da abin duniya me tarin yawan da basa ma san menene rashi ba ko wata kalmar datai kama da hakan amma sam basa cikin farin ciki. A haka cikin Mimi ya isa haihuwa ta haifi Saleem wanda haihuwarsa ta fara dawo sa farin ciki rayuwarsu. Mahir da Ammar kusan tare suka taso kaman ba shekaru sosai tsakaninsu sbd kaunar datake tsakaninsu tafi karfi akan wadda ke tsakanin mahir din da saleem. Haihuwar saleem da shekaru biyar Allah yayiwa zayneb rasuwa bayan ta gama qarewa ta koma kamar qaramar yarinya hakama anyi mata dashen zuciyar wanda ta samu chronic rejection maana transplant failure. Rasuwar Zayneb ta girgiza duniyar ZADEEN's gaba daya ta yanda tin daga lokacin suka sauya kaman basu din ba. Ammar ya shiga sabuwar trauma wadda ta sakasu barin qasar gabaki dayanta sbd a sauya environment a bisa shawaran doctors dake dubasa. Daddy mahmoud

Table of Contents

Chapters

163 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});