Chapter 11
Chapter 11
Rabonki ************ Gawar da aka jera part part dinta kamar gawayi a gabansu ne ya saka ummansa somewa a gurin shima zubewa yayi a gurin yana wani irin jijjigar data saka daya daga cikin abokan aikin baban nasa dake gurin rungumesa ya qanqamesa da karfi yana kira masa sunayen Allah tareda addua. Umma kuwa maza ne suka zuba mata ruwa a gurin sbd babu mata a gurin dan girman lamarin itama dan tanada dolenta ne a cikin wutar ta iso gurin batareda ta sani ba. Tana farfadowa ta sake somewa jini na balle mata a gurin wanda babu wanda ya lura sbd duhu da kuka tashin hankali duk da anriga anyi asuba a lokacin. Abdul dinne ne da aketa tofawa addua ya lura da umman tasa da gudu yayi kanta yana kallan jinin daya bata kayanta. Daidai nan sakina ta iso gurin cikin matsanancin tashin hankalin daya sake daga hankalin Abdul da tsoro sbd kwasar umman da akai zuwa gida hankali tashe. Suna isa gida mama sakina cikin gaggawa ta taimakawa fatiman jinin ya tsaya ta kwantar da ita tana karanta mata yan adduain data sani tinda ba wani ilimi me zurfi ne dasu sosai ba. Rasuwar Ayouba tayiwa fatimar mummunan dukan daya saka cikin da basusan dashiba kusan zubewa, Ayoub ne gatanta, Ayoub ne a matsayin uwa da ubanta da danginta sbd batada kowa bayan kawunta wanda ya aurar da ita ya tattarata ya watsar sbd daman neman hanyar rabuwa yake da ita ya huta daga wahalar dayake ganin yanayi da ita. Ayoub baida uwa baida uba sai yan uba da matan mahaifi wanda sukafi son balai akansa, Waye zai zama gatanta dana yayanta a duniyar yanxu? Abdul yayi kuka yayi kuka harya rasa ya zaiyi wani kukan sbd gawar mahaifinsa da aka jera masa baisan yaya zaiyi da ita ba, Durkusawa yayi gaban gawar yana sake fasa wani sabon kuka kirjinsa na wani irin radadin da baisan mene ba. Baba Ahmed wanda yake abokin aikin baban shine ya karbi ragamar komai sbd karfe tara na safe ma ta kusa kusan dukkanin maaikatansu na nesa da kusa sun iso tardda yan kallo na kauyen da makotan kauyen dan haka ba bata lokaci akai taho gida aka hada gawar aka yayyafa mata ruwan wankan gawa sbd bazaa iya maza wankan ba aka hadasa a farin likafaninsa aka nade akai masa janazah a kofar gidansa inda ya samu mutane daidai gwargwado sbd a cike kauyen yake ranar da mutane sbd abinda ya faru. Tinda Abdul ya rungumi gawar babansa dayake nade a kyalle yaji zuciyarsa na wani irin ciwo da nauyi kaman zata zazzago tareda wani irin radadi kaman tana bushewa. Kukansa daukewa yayi tsaf saida aka dawo daga kai baban ya dawo gida shi kadai batareda wani ya biyosa ba yana shigow gidansu ya tararda ummansa kwance daga ita sai mama sakina da wasu daidaikun mutane da suka gama gaisuwa suka miqe suka fice. Tahowa yayi ya zauna gefen ummansa wadda ta dago jajayen idanuwanta da sukai mata tsananin nauyi ta xuba masa shima ita ya kalla ya sunkuyar da kansa wasu hawaye masu tsananin zafi suka gangaro masa suna sauka qasa gabansa. Mama sakina ma kasa riqe kukanta tayi tafara hawaye masu zafi tana rufe fuskanta da tafukan hannayenta. Duka a cikinsu babu wanda ya damu koma tsayawa tantance irin satar da akai musu a gidan bayan fitarsu mama sakina ma data lura batai magana ba sbd radadi da ake cikinsa. Shiru gidan yayi har yamma babu wanda ya sake shigowa gidan sedai ayi sallama abdul din ya fita idan abokan aikin baban sukazo amma ko yan gidansu Ayoub din tinda safe suka zo akai komai dasu daga nan suka watse kowa yake harkan gabansa. Mama sakina tayi abinci tayi duk dubaran da zatai suci babu wanda ya iya cin komai a tsakaninsu dan haka ta hakura itama bata iya cin abincin ba sbd har cikin rai da jininta take jin ciwo da radadin da fatima ke ciki sbd kaunar datake tsakaninsu me girman gaske ce wadda suka taso a cikinta tin yarinta sbd itace ta zama kamar gatan fatima tin suna qananu har girmansu sbd ita tanada mahaifiya sabanin fatima data taso ba uwa ba uba. A gidan mama sakina ta kwana duk aike da fadan da baba ila yai mata bata koma ba dan haka ya zuba mata ido yaga gudun ruwanta. Washe gari da safe shugaban gurin aikinsu Ayoub din ya taho gaisuwa ya kawo musu abinci sosai da abubuwan buqatarsu tareda biyan kudin makarantar Abdul din wadda yake a local government harya gama. Yaso bada kudin dayake ganin kaman diyya ce zai biya amma ganin Abdul din yaro ne kuma matar ayoub din batada me tsaya mata hakama yan uwansa sun saka zalamar jiran ya bayar sai kawai ya fasa ya fadawa baba Ahmed idan Abdul din yagama karatu ya isa fara business zai basa da hannunsa insha Allah kuma zai rubuta hakan ya ajiye koya mutu bashi ne Abdul yake binsa zaa basa. Babu wanda yasan da hakan sai baba Ahmed wanda yayi naam da hakan dan haka bayan tafiyar alhaji Kabir din shima Ahmed tafiyarsa yayi sbd ba maganar aiki a gurin yanxu sbd kamfanin dai ya mutu mutus sai ansake sabon ginin ma dan haka yanzu maaikatan duk sun tafiyarsu sai kuma an sake ginin kamfanin akan wannan tukuna. Kwanan mama sakina bakwai a gidan yan kauyensu suka taho gaisuwa da matan kawun fatiman dashi kansa da wasu yan uwan sakinar da yawansu. Fatima a cikin kwanakin ta zama abar tausayi sbd abinci ma bata iya ci haka kawai cikin jikinta ya hanata lfy sbd damuwa da tsananin quncin da zuciyarta take ciki. Abdul ganin halinda mahaifiyarsa take ciki shima ya tabasa dan haka kwata kwata baya cikin walwala ko kadan daman babansa shine abokinsa kuma abokin wasansa sbd baya fita koina wasa bai sababa tin tasosawarsa. Mama sakina ma bata cikin walwalan kwata kwata sbd ganin halinda suke ciki dan haka bayan yan garinsu sun koma itama ta koma gida sedai duk bayan kwana daya sai tazo ta dubasu. Kawun fatiman da zai tafi ganinsu da abinci sosai baiji tausayi ko kunya ba ya diba abincin sosai ta tafiyarsa. Yan uwan ayoub din ma da sukaga hakan suma suka taho suka debi abincin me yawa sosai da cewa ai suma sunada gadon Ayoub dan haka tinda baibai komaiba a basu abincin. Abdul ne rayuwarsa tafara sauyawa sbd karatunsa daya fara rawa sbd kulawa da mahifiyarsa wadda ta kasa dangana da rashin baban dan haka lafiya kwata kwata tafara kaurace mata, Ta rame ta koma kamar wadda bata taba lafiyaba rayuwarta, Bata wani ci bata wani sha bata cewa komai sai dole ga cikinta yanata girma dan haka komai a gidan shine yakeyi masu, Shine yake musu wanki,ya dafa musu abinci,ya kai mata ruwan wanka yayi shara ya nemo,ya kuma tafi makaranta,sannan ya zauna yasha kuka a duk lokacinda ta kasa riqe abinda takeji tafara kuka haka yake yi a tareda ita,idan ciwo ya taso mata ma shine me zaunawa ya kula da ita ba magana haka zatai ta warke sbd basuda komai. Ahankali baba ila ya gaji ya hana sakina zuwa gidan kaman yanda ta saba dan haka duk abinda suke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163