Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki ************* Shiru yayi yana gama sauroron bayaninta da bai gane inda ya nufa kafin ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya bude baki da nutsuwa sautinsa na sanyaya yace "Mama meya faru? Me yake faruwa? Kukan dayafi na baya ratsa zuciya takeyi sosai tana kasa bude idanuwanta kaman yana gabanta tana breaking tace "Mun rasata gurin haihuwa...... Wani irin Numfashin daya saka maman kasa qarasawa ya sauke da wani irin sauti me tsananin nutsuwar son fahimtar abinda ya kasa fahimta yace "Ita Ummitan??? Kasa amsawa tayi sbd kukan dayaci karfinta mara sauti. Dif taji yaji kashe wayar batareda yace komaiba. Wani mummunan jiri ne ya dibesa kafafunsa suka sare da karfi gwiwowinsa suka daki qasa da karfi wayar hannunsa na faduwa qasa. Rawa hannuwansa suka dauka ya miqasu da sauri yana lalubar wayar hannunsa data fadi sbd ganinsa dayake kokarin daukewa da jinsa dab dif yake jin. Yanda hannuwansa ke rawa sosai yasaka ya kasa samun inda wayar take duk da tana gabansa sam baya gani. Kokarin kasa bugawa zuciyarsa keyi amma ya kasa barin hakan, Hannuwansa ya saka ya murza idanuwansa da karfin daya kusan raunana kansa kafin ganinsa kadan ya dawo ya duba wayar da sauri ya dauka hannuwansa na tsananta rawar datake kokarin hana wayar tsayawa hannunsa. Daqyar ya iya gano sunan Alh saad sbd rashin ganin da yake sake rufe idanuwansa kwata kwata. Ringing din da wayar keyi duk daya tafiya yake da numfashinsa dayake fara sarkewa yana suffocating. Alh saad cikin nutsuwa ya dauki wayar tareda sallama cikin mutuwar jiki sbd duk lokacinda Ko sunan ABDULAZIZ din yagani jikinsa ke mutuwa. "Ummitah ta haihu?? Meya sameta? Tana ina? Inason magana da ita,No i want to See her on a Videocall, Meyake faruwa, Why are you quite? Meyasa mama ke kuka? Ina Ummitah. Say something.......... Alh Saad bai zubarda hawaye a rasuwar Ummitah ba amma take yaji idanuwansa na kokarin cikowa da hawayen dake girgiza jarumtarsa da manyancinsa sbd yanda Yana jiyo wani irin mummunan breaking da ABDULAZIZ ke kokarin a muryansa, Gabaki daya tamboyinsa baya hayyacinsa yake jehosu babu abinda yakeson ji bayan amsa daya. Acan bangaren cikin sautin daya tabbatarwa da Alh saad jikin ABDULAZIZ din yai tsananin sanyi da wata qasqantacciyar murya yace "Ta haihu? Is she okay? I really want to talk to her, Am coming back tomorrow amma i cant without hearing from her, Please, Please......a cikin wani irin mummunan sauti me tsananin sanyi da rashin kuzari ko kadan ya ringa maimaita pls dinsa data saka Alh saad karasa karyewa ya sunkuyar da kansa yana shanye hawayensa ya bude baki shima a sanyaye cikin tsananin rashin kuzari yace "ABDULAZIZ karka manta Duk mai zai dandana mutuwa, Ka rasa iyayenka ka samu dangana a yanzu ma zaka dangana ne sbd Allah ya riga ya karbeta sbd lokacinta ne yayi, Abinda ta haifa tananan Lafiya kalau ita kam sedai Mu bita da Add..... Dif yaji wayar batareda ya qarasa maganar dayake ba, Daga wayar yayi ya kalla yaga tabbas ta yanke, Saka kiransa yayi da sauri yana miqewa daga zaunen dayake. Ringing wayar takeyi harta yanke baa dagaba Sake saka kiran yayi yana fatan ya dauka sedai harta kuma yankewa baa dagaba. Cigaba yayi da kiran kaman mahaukaci shima yana fatar a daga amma baa daga dinba karshe ma shiru ta dena shiga kwata kwata. Damuwa yaji duk ta cikasa sbd baisan irin damuwar da ABDULAZIZ din zai shigaba gashi bai tsaya sauraransaba bare ya kwantar masa da hankali duk da yasan babu abinda zai kwantar masa hankali a yanzu idan ba addua zasu duqufa yi masa ba. Gaba daya zuciyarsa kasa nutsuwa tayi yaji hankalinsa yana kasa kwanciya dan haka ya dauki wayarsa ya kira Sayyid Wanda aka siyawa sabuwar babbar waya dal yana dauka Yace "Sayyid Kunyi magana ne da ABDULAZIZ? Numfashi Sayyid ya sauke ahankali kafin yace "Yayi magana da mama dazu sedai basu gamaba ya kashe tace" Numfashi Alh saad ya dauke yana sake shiga damuwa yace "Inata kiransa baa dauka, Waye ya sanar dashi?? Cikowa idanuwan Sayyid sukai da hawaye masu zafi yana kallan Babyn datake rungume jikinsa tayi bacci a sanyaye yace "Babyn Ummitansa ce ta sanar dashi da kanta ta iso duniya...... qarasa maganar yayi hawayensa na sauka akan gefen fuskanta har saida ta dan motsa kadan. Shiru Alh Saad yayi yana sake shiga damuwa da rashin nutsuwar zuciya yace "Kukanta ya sanar dashi an haihu kenan?? Kasa magana Sayyid yayi sai daga baya yace "Eh" "Sayyid kuyita kiransa a samu wani yayi magana dashi pls kaji" "Ok insha Allah" Sayyid ya fada a sanyaye. Kashe wayar Alh saad yayi take Sayyid din ya saka kiransa sedai ma ko tafiya batayi yana saka kiran kiran yake yankewa da kansa. Ringa saka kiran yayi ba kakkautawa amma babu alamar ma kiran zai tafi. Fitowa yayi ya bawa Fiddausi babyn ta goyata shi kuma ya fita yanata sake kiran Hamman zuciyarsa na tsananin jin son magana dashi sbd tinda Akai rasuwar haryanzu bakinsa da nasa bai haduba bayan yana buqatan jin muryan Hamman ko zai samu Sassaucin rashin Jinin Hamman da yayi. Mama ya dawo ya sanarwa Baa samun ABDULAZIZ din dan haka itama ta dauko wayarta kowannensu yanata kira amma ba saa. Har dare suna kiransa akai akai amma sam babu sauyi. Da daddare mama da kanta ta shirya babyn a cikin kayan sanyi masu tsada da kyau ta kwantar da ita gefenta tareda Zuba mata idanuwanta tana tina ranar farkon haduwarta da Fatima Asalin mahaifiyarsu ABDULAZIZ din wanda tin daga lokacin kauna me karfi da tsafta a tsakaninsu. Fatima ta tafi tabarta, Inna ma ta tafi tabarta, Ummitah ta tafi tabarsu itama tabar musu 'ya kaman yanda Fatima ta tafi tabar musu Ummitan tana qarama, A yanzu batasan yaya zatai da ABDULAZIZ datasan duniyarsa ta rushe gabaki dayanta, Yaushe zai samu farin Zamowa ahali daya daya rage a zuriar fatima, A yanzuma zai sadaukar rayuwarsa ne gurin kulawa da tattali tareda ingata rayuwar 'yar da Ummitah tabar masa, Yaushe zai samu rayuwar farin ciki da walwala kaman kowa?? A yanzu basusan halinda yake cikiba a can qasar dayake daya samu wannan mummunan labarin. Hawaye ne sike gangaro mata ahankali ta gefen ido suna sauka akan pillon da kanta yake kai batareda ta dauke kallanta daga kan babyn wanda itama Sunan Fatimar ne sunanta sbd Shine Sunan da ABDULAZIZ yakeso fiyeda kowane suna kuma shine sunan dayace zaa sakawa Babyn daman idan an haifeta sbd Ummansa Fatima ce hakama Ummitansa Fatima ce dan haka a yanzu ma ga wata fatimar ya samu wadda tasan zai iya bada rayuwarsa akanta itama. Sayyid kwana yayi yana kiran Hamman sbd gaba daya yaji shima bayajin nutsuwa tinda baya tareda su yasan yana can cikin mawuyacin mummunan halin dayafi duk wanda suka shiga baida wanda zai rungumesa ya rarrashesa bare quncin rasuwar Ummitah yana ninkuwa ne sbd ko gawarta bai samu gani ba bare janazah dinta wanda har abada bazai dena jin wannan radadinba a zuciyarsaba kuwa. Shi kansa Alh Saad akai akai ya ringa sake kiran

Table of Contents

Chapters

163 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});