Chapter 34
Chapter 34
a dakin mijinta ta kwana sbd Shine zai tasheta tinda asuba sufara shiri bare kuma daman Ummitan da kanta ta tafiyarta gurinsa itama mama bata hanaba tinda kila idan ABDULAZIZ din ya dawo bazai barsu guri daya ba sai Ummitah ta haihu ta koma masa yanda yake ganin ya kamata ta koman. Irin tsananin Asalin son da Sayyid kewa Ummitah kusan a duniyarta ABDULAZIZ ne kadai nasa ya fi nasa sbd So me tsaftar dayake mata daga Allah ne shi ya halitta masa shi a zuciyarsa, Kwana yayi a zaune yana kulawa da ita tareda tarairayanta yana jin kaman ya rabata da cikin jikinta taji sauki hakama shi kansa ya shirya bazata sake haihuwa yanzu ba tinda ciwo da wahala cikin yake sata hakama yana tsoron wani abin ya sameta koda agurin haihuwa ne bare ya sani ko Hammanta ABDULAZIZ bazai bari ta sake haihuwa anan kusa ba idanma bai rabasu ba akan sai sun gama karatun dayace zasuyi. Karfe tara suka fito a shirye tsaf suka nufi dakin mama wadda tinda tai asuba bata koma ba tana zaune tana jiran lokacin zuwan nasu asibitin yayi. Dining suka nufa wanda suka ga ancika sa sosai ayau din fiyeda kullum hakama abincin dayake kai a yau an samu sauyinsa. Mama ce ta zauna Sayyid kuwa Ummitah yake kokarin taimakawa ta zauna Ahankali wani irin qamshi me sanyi ya fara shiga hancinsu mai nutsuwa, Ahankali Ummitah ta dakata daga zaunawan da zatai tana dago fararen idanuwanta dasuke sak da nasa ta waiwayo cikin sanyi hancinta da gurin suna sake gauraya da qamshinsa. Sayyid ma qamshin ya sanyasa sakin hannun Ummitan Ahankali yana juyowa sbd Tin ranar farkon haduwarsa da Hamman ya riqe qamshinsa sbd Kaunarsa da Allah ya dasa masa arai shima sbd Ummitah. Inda suke kalla Mama ta juya ta kalla taga mene sbd ita hankalinta da hancinta basu wani bata tinanin qamshinba. Daidai lokacin ya sako kai a natse cikin wani irin kwarjinin daya saka Sayyid sauke kansa cikeda girmamawa yana kasa qure kallansa akansa sbd ba kwarjininsa kadaiba hatta hasken fatarsa datake wani irin shining na hutu da kwanciyar hankali tareda daula datake samu ya saka kyansa yin yawa. Ummitah ce ta qure kallanta akansa tana jin dukkanin jikinta na mutuwa wani sanyi yana sauka zuciyarta yana mamayewa, Batada abinda yafi mata dadin kallo a rayuwarta sama da kallansa a gabanta, Kyansa da asalin kammminsu dasuke iri daya amma shi ya sauya gaba daya komai nasa daban yake da nata sbd rayuwar da inda suke rayuwar ba dayaba, Hasken idanuwansa zuwa dogon hancinsa ta kalla tana rokon Allah ya basa tsari da kariya daga dukkan sharrin kowace mace a duniya. Shima ita yake kallan cikeda wata irin kewanta dake cinsa kaman cikin kansa zai kunce dan haka yana isowa hannunsa duka biyu ya bude ya rungumeta yana karanta mata adduoin tsari da kariya itada abinda yake cikinta kafin ya saketa ya saki wani Kyakkyawan murmushin daya saka sayyid kasa dena kallansa da tattausan sauti yace "Sorry Ummitah ABDULAZIZ, Yaya,ya jikinki? Kafin ta amsa gurin mama ya juyo cikin kulawa da sakewa da girmamawa yace "Barka da safiya Mama, Yaya fama da sauyin guri? Na sameku lfy?? Murmushin farin cikin ganinsa tayi tana cewa "Duk lafiya kalau Sauyin guri kuma ai munata kokarin sabawa, Tafiyar dare kayi kenan? Zaunawa yayi Ahankali yana cewa "A cikin dare na iso sai ban tasheku ba tinda kun riga kuna hutawa" Sayyid ma zaunawa yayi yana cewa "Barka da dawowa" Kallansa yayi cikin kulawa da sakar masa fuska sbd ya sake yace "Thank you,yaya kaima kanata fama da kadaici right? Gyada kai Sayyid yayi yana kokarin sakewa da hamman. Ummitah na gefensa fuskanta cikeda da murmushi me kyau da nutsuwar data kwana biyu bata iyawa sbd yanayinta. Breakfast suka fara cikin kokarin sakewa dasu dukkaninsu sbd sayyid ya sake dashi tinda tsakaninsa da mama da Ummitah babu wani kamewa ko rashin sakewa. Bazai taba tina yaushe Zuciyarsa ta samu asalin farin ciki irin wanda yake cikinsa a yanzuba sbd kasancewarsa dawowa rayuwa a guri daya da Ummitah wadda babu ranarda zasu sake rabuwar gurin rayuwa daban daban har abada sedai rabuwar kwanaki na tafiya dayake yawan yi sun hadu kenan sai mutuwa insha Allah, Kallan Sayyid dake cin abinci yayi a natse yana kallan Ummitah yaji zuciyarsa na sake karban Sayyid din cikeda Kauna sbd Aurensa dayake kan Ummitah bazai rabasa da ita ba tinda shi kansa mahaifinsa a hannunsa ya basa amanarsa kuma ya karba har Abada insha Allah. Yanzu ne yakejin Nutsuwa da godewa Allah da hakan dan Sayyid dinne kadai Ummitah zata aura suci gaba da zama a taredashi, Ahankali ya bude bakinsa cikin sauti me nutsuwa da rashin sauti yace "Thank you Sayyid" Kallansa sukai dukkaninsu dukda ba sauti yayi maganar cikin turancinsa dayake kashe Sayyid. Mama ce kadai da batasan wani thank you ba bata kallesa ba. Bai wani ci abincin ba hankalinsa na kan Ummitah wadda ita kuma idan yana tareda ita take cin abincin dama bata saba cin ba sbd jin take komai nata ya bude. Mama tasan daman indai yana tareda Ummitah ba wani abincin kirki yake ci ba dan haka bayan Ummitan ta gama sai ta kallesa cikin kulawa tace shima yaci abincin. Tea da chips mara maiqo yaci yana gamawa gaba dayansu suka miqe suka bar dining din. A shirye yake sbd yasan da kai Ummitah asibitin dan haka ma ya fito da wuri da sai yakai guraren 11 bai fitoba. Key din mota da wayarsa ya fito dasu a hannunsa sai tsadaddiyar Hular fcap ta fendi daya sako ya fito. Daga shi sai Ummitah din suka fita sai sayyid mama a gida suka barta yace ta koma bacci ta huta. Shine yake driving a hankali Sayyid na zaune a gaba sai Ummitah din dake baya tana kallan garin cikeda shaawa da burgewa. Sayyid dayake yana fitowa sosai suna tafiya gurare daman can sai baya wani kalle kalle sosai sbd ya saba ganin ire iren hakan. Wani babban private clinic me tsada sosai yakaita suna isa babu wani jira ko bata time a asibitin sbd kyanta akai mata registern Prenatal visit da zata ringa zuwa. Wani Dr Ken ne ya dubata dakyau cikeda kulawa ganin Yanda ABDULAZIZ sam tsananin kaunarsa akanta bata boyuwa duk da bai saniba ko shine mijinta ko yayanta koma waye a gunta kaunarsa a bayyane take. Scanning akai mata bayan angama diban jininta da sauran samples na aune aune da zaa mata. Cikin kulawa da sake fuska sosai yana tayasu murna ya kalli ABDULAZIZ daya dawo dakin bayan angama Scanning din yace "Congratulations Sir its a baby girl" Kallan Tvn yayi Ahankali kafin ya dawo da kallansa kan Ummitan da itama shi ta kalla suka kalli Sayyid a tare wanda farin cikinsa shima yake a fili sedai a duk lokacinda ABDULAZIZ yake kusa baya zaqewa akan Ummitah dama cikinsa dayake jikinta sbd kawaici da nauyin ABDULAZIZ din. "Thank you dr" Yafada yana karban result din suka fito yana rasa yanayin dayake ji a zuciyarsa duk da abu daya ya sani shine kome Ummitah zata haifa ya fito a cikinta,jininta zai kaunacesa kaman yanda yake tsananin kaunarta. Sun dade a asibitin sbd formalities din da daukan time da kuma aune aunen,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163