Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 162

Chapter 162

Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tukuna ayi magana daga baya idan ta nutsu yanda ya kamata. Dakin yakumbo aka kaisu matan gidan da yara na musu sannu da zuwa cikeda mutuntawa da farin cikin ganin jikar zeenah ce yau a gidan. Kasa cin komai jannah tayi wanka tayi da ruwan sanyi a bandakin da baida rufi take sanyi da zazzabi suka rufeta. Daqyar yakumbo ta sakata shan sabuwar madara me dumi wadda ta dan taimaka mata amma sallah kawai tayi ta dunqule guri daya tana rawar sanyi idanuwanta na tsiyayo da hawaye masu dumi. Ummah ma taci abinci tayi wankan amma itama zazzabin ne ya kwantar da ita. Washe gari duk yanda ake tinanin ciwon yabar jannah kasa barinta yayi dan haka tsoro ya kama su Modibbo kawu isiya yace karta mutu su tattarata su sallemeta yakumba tace aa. Ummah ta warware ita dan haka tafara kulawa da jannah din wadda ta rafke lokaci daya ta sake komawa kalar tausayi. Satinta daya ana jinyarta anata maganin hausa kafin tafara warwarewa ta dawo daidai. Sai a lokacin hankalinsu kawu ya fara kwantawa harma suka zauna da ita ta fada musu komai sedai ta boye cewan da sanin iyayenta akai komai tadai sanar dasu zuciyar da aka kawo musu ashe ta kisa ce bata hanyar gaskia bane batareda saninsu ba wanda hakan ne ya saka rufesu shekara daya. Su kawu Modibbo dasu kawu isiya da kukansu da komai na tausayin yan uwansu wanda kukansu kadai ita jannah tsoro ma ya ringa bata sbd tamkar kukan yayan aljanun dare haka suka ringa matso hawayen suna darzar idanuwa kaman masu gasar kuka sbd ta gani idan su Dad din suka fito ta fada musu da waye da waye sukai kuka sbd su samu rabo me tsoka sbd basu yadda da kakaf komai aka kwace musu ba dan kamar bame yiyuwa bane dan haka zasu kula da ita kamar kwai har su Dad din su fito su samu suma su lasa arziki. Bangaren Asalin kakansu na gidan daya dade da mutuwa Modibbo yace samarin gidan su saka karfi suyi aikin qasa su gyara daki biyu ne da bandaki sai madafa a gyarawa su Dad din kafin su fito. Su Garba da fodio da Idris sune matasa samarin gidan masu ji da lokaci tini suka fara aikin kowa da abokinsa ake aikin sbd kowa da kudirinsa na shirin dawowan su Dad din rayuwa a cikinsu da santaleliyar buturiyar 'yarsu data zama tamkar bayyanar Zinariya a kauyen. A cikin gida kuwa kamar jannah bazata iya rayuwar kauyenba sai kuma tafara sabawa sbd kauna da kulawa datake samu tako ina a gidan harma da wajen gidan wanda ya saka mata farin jini. A cikin gidan akwai budurwa tsararta 'yar kawu isiya wadda mijinta ya rasu ta dawo gida da yarinyarta 'daya itace tafara zama abokiyar hirarta. Fatma itace tafara fita da ita garin da gurare daban daban tin tana tsoron mutane harta saba tana shiga cikinsu sosai, A gidan kowa ta kansa yakeyi dan haka tana ganin lokaci yafara ja ta fara koyan sanaar saqa da siyarwan da Fatma keyi itama tafara ita kuma Ummah tana taya matan su Kawu harkan nono da manshanun da sukeyi dan haka itada Ummah sai ya zamana suna dan samun abinda suke kulawa da kansu basu bari sun zamarwa kowa lalura me gajiya ba. Kaunar datake tsakaninta da Ummanta ya wuce dukkanin tinanin da mutanen gidan dana waje keyi akansu sbd Ummah babu abinda takeyi a rayuwarta yanzu bayan duk abinda zata kula ta tattala rayuwar Ummijan dinta, Duk aikin wahalar datakeyi a gidan sbd jannah ne hakama duk daren Allah kwana takeyi kulawa da jannah dinta harta saba bata iya bacci sauro bin jannah,bata iya bacci idan jannah na cikin damuwa bata iya komai saida jannah dinta. #MAMUH*_KALBIM_* _Mamuhgee_ 98 *SHOP WITH ME by RANO* 08030811300 Best children's clothing shop💯 https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7 Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema. Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta. ********** A bangaren jannah a yanzu data samu kwanciyar hankali da nutsuwar datake jin babuta sai a kauye da babu tashin hankali sai rayuwar rufin asiri, Ummah ce hasken idaniyarta da zuciyarta,ummah ce karfinta,Ummah kuzarinta,duk abinda takeyi tana yinsa ne sbd Ummah dan haka a ranta takejin Ummah uwartace da bazata iya rabuwa da itaba har abada dan haka ma ta yanke shawaran hada ahali da Ummah daga ranar da Dad dinta ya fito. Angama gyara dakunan da zasu zauna dan haka itada Ummah suka fara komawa da Fatma wadda take takure a rabe dakin yadikkonta. ******lokaci yafara tafiya sosai sbd shekara ta kusa cikewa dan haka lissafin su kawu sai ninkuwa yakeyi shi kawu isiya har batan lissafin abubuwan da zaiyi yakeyi, Shikuwa Modibbo bature yakeda niyar binsu ya zama duk inda zasu kafarsu kafarsa shima. Su garba kuwa shirin sosai sukeyi na yanda zasu tarbi ahalinda zasu iya zama sirikansu dan kuwa dadi da wuya zasu tsaya bazaa bar kauyen da jannah ba sai waninsu ya aureta ko zaa tafi kasar wajen dasu suma. Rayuwa tayiwa jannah da Ummah daidai babu me damuwar komai a cikinsu saita kewan nasu idan ta taso musu, Ciwon Ummah yana dadewa bai tashiba idanma ya tashi jannah rungumeta takeyi duk dukan dazai mata bata iya saketa haka zata ringa hadiyewa cikim azaba harda rauni da komai bata iya rabuwa da ita har saita dena ta fara kuka shine zata rungumeta susha kukansu tare su gama batareda wani yasan halinda suke ciki ba. Jannah Zad kaman yanda rayuwarta ta sauya ita kanta ta sauya tako ina, Rama da quncin data fito a cikinsa ya tafi, Jikinta ya dawo daidai bame qiba ba ba kuma ramammiya ba, Halaye da dabiunta da yawa rayuwa ta sauya mata su, Kaman yanda komai nata ya sauya hatta sunanta ya sauya sbd a yanzu kaf garin ba jannah suka santa ba da sunan da Ummanta ke kiranta aka santa dashi wato UmmiJan, Rayuwa ta koyar da ita darasi, Rayuwa a cikin mutane daban daban ya koyar da ita abubuwa da dama na rayuwa tareda sanin meye rayuwar a yanzu. Ahalin Modibbo sun kaunace ta a lokacinda batada kowa batada komai, Sun karbeta hannu bibbbiyu batareda gudunta ba sbd iyayenta sun gujesu dan haka har cikin ranta a yanzu take kaunarsu sbd a yanzu ne ta gane me dangi da yawa suke nufi, A kauye suke suke rayuwa a cikin dajin da babu wuta babu ruwa amma a hakan tasamu nutsuwar da bata samu ba a can inda daular take dan haka take rokon Allah ya bawa ahalinta ikon iya rayuwar da zasu taho su tarar anan din. Babbar muguwar halin da gidan suke dashi shine tsananin son abin duniya wanda a tsakanin kawunnin nata bata san wanne yafi wanne kwadayi da son abin duniya ba. ********BAYAN SHEKARA GUDA Ayau itace ranar datafi kowace rana a rayuwar UMMIJAN sbd itace ranar da zata isa abuja dan haduwa da

Table of Contents

Chapters

163 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});