Chapter 145
Chapter 145
wasu hawaye masu tsananin zafi da tashin hankali suna gangaro masa jikinsa na daukan rawa gabaki daya wanda ya saka kowa dayake gurin tsit kafin kukan daya kasa riqewa ya kubce masa sbd kaman ana fada masa ne Falaq tafiya zatai ta barsa kenan.. Sautin kukansa ne ya tayarda tsikar jikin dukkanin wanda yake gurin yana ratsa zuciyoyinsu, Jijjiga jikinsa keyi sosai fuskansa na tafin hannuwan mama datake hawayen tausayinsa har cikin ranta, Sayd ma silalewa yayi ya zauna a qasa hawaye masu tsananin zafi da radadi na tsinke masa sbd kai tsaye kaman dama ce aka sanar dasu ta kwanakin dasuka ragewa Falaq a duniya. Mama ma ganin kukan Sayd sai ta kasa riqe sautin kukanta ta rintse idanuwanta tana sake jin saukan hawayen AZIZ masu zafi a tafin hannunta. Dr Ashir da suke saka hawaye taruwa a idanuwansa barin gurin yayi yana jin tausayin familyn gabaki daya sbd shi kansa yasan samun donor abu ne me wuyar gaske da ahaka suna ji suna gani lokacinta zaiyi tabar duniya. Daqyar mama ta iya kama hannunsa ta dagar dashi ta kama hannun Sayd shima dayake kuka rasa 'yarsa da har yau batasan matsayinsa na mahaifintaba, 'Yar dayake kallo a lokutan quncinsa ya samu sassauci da sanyi, 'Yar dayake wa kallan mahaifiyarta daya rasa, 'Yar da har yau bata taba kallansa a uba ba bare ambatarsa da sunan uba ko so daya ba... Dakin falaq din mama ta shiga dasu ta isa dasu har bakin gadonta ta saki hannuwansu suna kallan yanda Allah ya Maidata a lokaci daya ba kyan gani, Oxygen ne da wasu abubuwan a fuskanta da bakinta harma da kirjinta, Tayi haske a lokaci daya tai wani irin jemewa idanuwanta a rufe, Kallo daya zakai mata kasan ciwo me girma ne a tattare da ita wanda Allah ne kadai yasan ko zata tashi kokuwa tafiyarta zatai itama ta huta da wannan duniyar me wahalar zama. Silalewa AZIZ yayi ya zauna a gefe yana kallanta sbd yanayinta dake nuni da azababben ciwone take cikinsa duk da bata hayyacinta.. Sayd ma sunkuyar da kansa yayi yana zuba mata dukkanin idanuwansa jikinsa a mace. Shiru dakin yayi babu me motsi, Ayau falaq datake da gatan da dayawa basada gata a kwance numfashin datake shaqa ma na Oxygen ne zuciyar da zata rayu take buqata, Kudi da gatanta ba zasu iya bata hakan ba, Soyayyar mahaifinta bazata iya bata hakan ba sai abinda Allah yaga damar yi da ita. Tsawon Lokaci ahakan har aka fara kiran asuba suka fito AZIZ na gaba Sayd na gefensa kowannensu idanuwansu sunyi nauyi sosai. Masallaci suka nufa sukai sallah suka zauna suna adhkar har gari yai haske kafin AZIZ ya dago idanuwansa ya kalli Sayd tsawon seconds kafin ya bude baki Ahankali ya furta "Ka sanar da Dr Nico komai da ake ciki a sakamu na list din gaggawar neman donor" Gyada kai Sayd yayi yana sauke numfashi. A kusan qasashe 6 Sayd ya buga da neman zuciyar cikin lokacin daya ragewa Falaq din wadda take qara wani irin sauyawa daga kwancen tana rasa duka albarkar jikinta. Duk yanda suke tinanin zasu iya riqe abin sun kasa su kansu a cikin budadden qunci suke daya nauyaya zuciyoyinsu. Gida suka dawo aka baro Fiddausi dataje can, Tsit gidan yayi ga dining an jere abinci amma babu wanda ya iya fitowa a cikinsu kowa na daki. Wanka yayi ya sauya kaya ya zauna yana buga wayoyi a wayarsa kansa na zarewa ahankali ahankali gurin neman ta inda zai samu zuciyar dasawa 'yarsa. Acan asibitin Zaadens kuwa Saleem ne ya fara dawowa daidai kafin jannah wadda ta zubawa mahaifinta dake zaune gabanta idanuwanta da sukai tsananin laushi. Mahaifinta kaunarsa a jininta take da duk laifin da zai aikata a duniyarnan bazata taba dena so da kaunarsa ba, Bazata taba gudunsa ko qyamarsa ba,bazata taba jin tsanarsaba, Kaunarsa ce take sake rufesa da tausayinsa sbd duka wannan mummunan lamarin daya faru ya farune sbd kaunarta da shedan daya shiga zuciyarsu ya gurbata tawakkalinsu. Ahankali wasu hawayen baqin ciki da dana sani tareda kunyar yarsa suka gangarowa Dad ya dago ya kalleta itama shi din take kalla idanuwanta na tsiyayar hawaye. Saukar hawayensa Kan tafin hannunsa dayake bude ne ya sakata rintse idanuwanta da karfi tana jin zuciyarta na tsananta ciwon ganinsa ahakan... Bude bakinsa yayi Ahankali cikin sanyi yace "Akwai son zuciya da rinjayar shedan a lamarin da muka aikata, Nayi dana sanin nema miki zuciyar datake jirjinki bata hanya halastacciyaba sbd kema kin shiga matsalar da mune muka janyota, Jannah ni mahaifi ne da idanuwana sika rufe akan kaunar danakewa 'yata a baya, Kuma a yanzu ma na shirya zama uba da idanuwansa zasu rufe akan kaunar dayakewa 'yarsa na aminta na shirya karban da fuskantar sharia sbd hana rayuwarki shiga quncin da babu fita, Bakida masaniya dan haka zan miqa kaina da kaina sbd na kasa baki farin ciki daga karshe sai kuka da qunci...... Wani irin kuka me tsima zuciya ta fasa tana fadawa jikinsa ta rungumesa da karfi tana girgiza kai quncinta da radadin zuciyanta na tsananta. Rungumeta yayi shima yanajin kasawarsa da lalata rayuwar duka 'yayansa a matsayinsa na uba. Maheer dake gefensu kuka yakeyi sosai shima har yana jijjiga zuciyarsa na radadi shima yana jin zai iya bin mahaifinsa a duk matakin da zai dauka a wannan rayuwar me kyau da mara kyau dan haka idan mahaifinsa ya aminta dasu miqa kansu su karbi hukuncin daya kamata ya aminta da hakan ya shirya binsa har lokacinda da zaa kashesu kaman yanda suka kashe. Kuka sukeyi gabaki dayansu a dakin cikeda tsananin so da kaunar junansu da haryanzu babu abinda ya sauya daga cikinta, Saleem ma mahaifiyarsa da likita ya sanar dashi ta samu paralys ya rungume yana wani irin kuka mai tsima zuciya. Jannah dagowa tayi ta kalli mahaifinta kafin ta maida kallanta kan Maheer dayake gefenta riqe da hannunta daya ta bude baki cikin sanyi tace "Neman tuba da yafiya a gurin Allah shine farko kafin komai, Insha Allah zamu cinye wannan jarabar Dad" Dakin Mimi suka nufa dukkaninsu idanuwa a jeme a can suka tararda mugun labarin daya qarasa collapsing duniyarsu gabaki dayanta. Sabon zama suka dora na jimami har dare. Tsakar dare Mimi ta farka ta bude idanuwanta ahankali daqyar cikin wani irin sanyi tanajin dukkanin quncin zuciyarta ya yaye ganin ahalin dai daga karshe kansu ya sake hadewa basu rabu ba duk da munin aikin dasu Dad suka aikata. Akan Saleem ta tsayar da idanuwansa tai masa kallan mintina ya saka hannunsa cikin nata yana hango kewan Ammar a cikeda idaniwanta wanda babu bakin furtawa, Maida idanuwanta akan Maheer tayi tana jin tsananin tausayin kaddarar data hau kansu wadda batasan hukuncin da zasu fuskanta ba amma koma menene tana masa fatar samun sassauci da rayuwa me kyau a gaba idan yanada rabon tsallakewa. Maida idaniwanta tai kan jannah da itama ita take kallo idaniwanta sun bushe sunyi jajir babu abinda yake cikinsu sai qunci da damuwa. Hawayene suka gangaro daga gefen idanuwan Mimin tana jin tausayin rayuwar jannah da batasan yaya zata kasance ba idan ta wayi gari batareda gata da dukkanin ahalinta... Maida kallanta kan Dad tai wanda kallo daya tai masa idanuwanta suka rufe ahankali. Maheer ne yafara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163