Chapter 99
Chapter 99
nake, muna haka naji tsayawar mota a kofar gidanmu wanda hakan ya tabbatar min da cewar Jibril ne kuma daman yana kusa da unguwar a lokacin da ya kira. “Ga Jibr.. Il nan... Yace tafiya zai yi da Noor” Na fada muryata na rawa. “Ki fita ki fada masa gaskiya dole ne ya sani” Inna ta umarceni, tashi na yi na fita ina hawaye, nasan Jibril ba zai yarda ba amman ya zama dole na fada masa, ko da na fito yana jingine jikin motarsa yana danna wayarsa da alama ni zai kira. Fitowata tasa ya dago kai ya kalleni yanayin yadda na ke tafiya na doso shi yasa ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata. “Karki fara min complain ba gurinki na zo ba Wallahi, kawai zan dauki dana ne kuma nasan idan ban zo da kaina ba ba zaki bari taje ba, and i need to be with my son” “Jibril.... Noor ...... Noor” Na kasa magana saboda kukan da ya ci karfina. Ya sakar min ido sosai yana son jin abunda zai fito daga bakina. “Noor ya bata....” “What? How?” Na kasa magana sai kuka na ke. “Look Nawwara, idan ma kin shirya hakan ne dan ki samu nisanci da ni to wannan ba hanya ba ce, dan zan iya jure komai ban da rashin Noor, dan Allah ki canja tsari” “Wallahi ba wasa na ke ba Noor ya bata” Ya tsaya kallona dan tabbatar da zancen da nake gaskiya ne ko akasin haka. “Kamar ya Noor ya bata bata ya bata ya bata as how?” Ya tambaya yana mai daga murya tare da hannyensa sama, ni kuma sai kuka na ke ina ta kokarin rufe baki. “Ki daina wannan banzan kukan naki ki fada min yadda aka yi dana ya bata” Na razarana sosai saboda yadda ya katsa min tsawa da kuma irin bacin ran dake cikin muryarsa. “Da suka fita da Bilal shine suka tsaya Agg mall siyen chocolate sai ya nemi Noor ya rasa” Ya yi dariya marar sauti “Ki ce Bilal ya sace min yaro ya siyar ko kuma ya boyeshi ya nemi kudin fansa” “No Bilal ba zai yi haka ba, Wallahi Bilal ba zai taba cutar da Noor ba” “To wa zai cutar da shi waya batar da shi a yanzu?” Ya fada a tsawace. “Wallahi Bilal ba zai cutar da Noor...” Hannunsa ya daga zai mareni sai kuma ya kaiwa gilashin motarsa bugun yana wani irin huci. “Akan dana zan iya taba kowa Nawwara kuma kowa da kowan nan har da ke, idan kin san wani abu ne kula da Bilal tau ki gaggauta kanwace shi tun wuri” Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya bar ni nan tsaye ina aikin kuka, sai ga Sakina ta fito da gudu ta nufi hanyar Babban gida, ni kuma na juya na koma, ko da na shiga Inna na ta buge bugen waya tana kuka kamar yadda Jidda take. Ko da tara na dare ya yi gidanmu ya cika da jama'a makota da kuma yan uwa, maza suna suka shiga gari inda ake sa ran za a ganshi har Agg mall din anje amman ba a ganshi ba, ko da Baba Sulaiman ya aika Sakina ta kira masa Bilal sai ta dawo ta fada mana cewar wai yana police station an tafi da shi tun dazu, kowa yayi mamakin wanda zai kulle Bilal a wannan lokacin sai da Baba Sulaiman da Inna suka fada cewar Jibril ne, a ranar duk wanda yake cikin gidan nan ya tabbatar da cewar Noor yana da Uba. Ni da Inna da Mama turai da Baba Sulaiman da Sakina da kuma Jidda muka kwasa muka je station din, daidaikun mutanen unguwa suka bimu saboda gulma. Mun tararda Jibril a can sai mahaifin Bilal da mahaifiyarsa tana ta kuka, sai wani kanensa daya. “Ina Bilal din yake?” Inna ta tambayi Mahaifinsa sai ya amsa mata cikin rashin dadin rai. “Yana can ciki sun ce ba zasu fito da shi ba, tun dazu muke a nan tsaye babu irin rokon da ba mu musu ba” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Cewar Inna, ni kuma na doshi gurin Jibril sai yayi saurin tashi ya fice daga station din, da gudu na bishi ina kiran sunansa daker ya juyo ya kalleni fuskarsa babu annuri. “Minene” “Wallahi ba Bilal ba ne ya sace shi” “Ke kika sace shi” “Wallahi ba Bilal ba ne, dan Allah ka kyale kasan yan sandan nan basa da mutunci zasu iya ji masa fa” “Ke ta Bilal kike ni kuma ta da na nake, babu ruwana da alakarku ya fito min da da na ya zauna lafiya” Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya barni nan tsaye. Wasa wasa aka kwashe kwana uku ana abu daya, Jibril ya ki bari a saki Bilal saboda yana zargin shi ya batar masa da da, ita kuma mahaifiyar Bilal da yan uwansa suna dora laifin akaina, a ganinsu ko da da gaske Bilal ya batar da Noor ai be cancanci a ayi masa irin wannan wulakancin ba, har fade take wai danta be taba zuwa cell ba sai dalilina, babu irin magiyar da bana ma Jibril amman kullum maganarsa daya Bilal ya fito masa da da, ni da shi baka iya tantance waye ya fi shiga damuwa, sai dai Jibril ya fini shiga tashin hankalin sosai saboda haukacewa yake kokarin yia kan neman dansa, har mahaifinsa sai da ya zo har sokoto saboda wannan maganar Noor, kullum mafarki na Noor sai dai har yanzu zuciyata bata zargin Bilal. Ranar talata ranar da mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir ya yasa a kashe maganar gurin yan sanda muna station mu dukanmu Jibril ya saka Bilal gaba yana masa magiya har da kukansa. “Dan Allah dan Annabi Bilal ka fada min inda da na yake? Idan kudi kake so ka fada min zan baka ko nawa ne, kuma Wallahi na maka alkawari ba zan bari a ama ka komai ba, amman Noor shi kadai ya rage min ka tausaya min Bilal dan girman Allah” Bilal ya kasa magana sai hawaye yake, gaba daya kamaninsa sun canja. “Wallahi Bilal be dauki Noor ba” Na fada cikin kuka, sai mahaifiyar Bilal ta kwatse ni. “Ke dan Allah can rufewa mutane baki, baki fada tuntuni ba sai yanzu tsohuwar munafuka, ko da yake Allah ya kara ai kai ka ce ka ji ka gani” Ban kara mata magana ba, har muka fito station din, muna dawowa gida sai ga Jibril ya iskoni har gida be tsaya a waje ba ya shigo cikin gidanmu da sallama ba tare da ya nemi uzinin shiga ba, ban tabbatar da irin ramar da yayi ba sai a wannan lokacin idanuwansa sun fada sosai. Gaban Inna ya je ya risina yana hawaye kamar karamin yaro “Inna na rokeki ki saka Nawwara ta fada min wani abu akan batan da na, shi kadai ya rage min a duniyar nan, yau kwana hudu kenan ba a ga Noor ba, duk wanda ya dauke ke Noor rayuwarsa yake so ba kudi na ba, da kudi nane da yanzu an kira an ce na bayar, babu inda ban duba ba, babu irin binciken da ban sa anyi ba amman an kasa ganin Noor”
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119