Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 105

Chapter 105

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tare da yin murmushi. Ina tunanin Mustapha ya yi min haka ne saboda bakinciki ya yi min yawa a tunaninsa zan ji zafi idan ya ce ya samu wacce yake so duk da nasan ba zata wuce Jidda ba domin alamu sun nuna hakan, ko rantsuwa na yi bana kaffara Mustapha ya so Jidda ne kuma zai aureta ne saboda na ji bakinciki tun da aminiyata ce, kuma yana son bakinciki da nake ciki na rashin lafiyar Noor ya karu akan kishi ne saboda na ki shi, ni kuma na kasa damuwa saboda daman can bana son shi kuma ina ganin sonshi a idanuwan Jidda dan haka sun fi dacewa da juna duk kuwa da kasancesar ta kasa fada min ne saboda karna zargeta ko kuma na yi tunanin wani abu. Basu wani dade sosai ba Mustapha yasa hannunsa aljihu ya dauko kudi mai dan dama ya aje mana saman gado tare da yi mana addu'ar Allah kara lafiya, sannan ya yi gaba sai na kamo hannun Jidda ya riketa har sai da ya wuce sannan na kalleta na ce “Amintakarmu ta fi karfi mu boyewa juna abu” “Nawwara ban yi nufin boye miki ba, kawai ban san yadda zaki kalli abun ba ne” “Ta fuska mai kyau zan kalleshi Jidda, na san ke aminiyata ce kuma ba zaki taba cin amanata ba, Wallahi ko da Mustapha be furta da kansa yana sonki ba zan hada soyayyarku saboda dacewar da kuka yi da juna, kuma ina ta tabbacin idan har ya aureki ba zai sake wata rayuwa marar kyau ba” “Ba a yanxurya kamata mu yi maganar nan ba Nawwara, ki kula da Noor please” Ta fada tana dafa kafadata sannan ta wuce. Ni kuma na dawo na zauna na saka Noor a gaba ina ta kallonsa zuciyata cike da tausayinsa. Misalin goma na dare Jibril ya dawo, yana shigowa dakin Noor na farkawa da kuka yana kiran sunana. “Momy Momy” “Gani nan” Na yi saurin kama hannunsa. “Momy sun yanka ni wasu sun ce zasu kashe ni” Sai Jibril ya yi saurin karasowa ya kama dayan hannunsa kuma ya shafa kansa. “Shiiiiiiiiiii you're safe kana kusa da Momy da Daddy babu wanda zai taba ka” “Daddy sun ce sai sun yanka ni sun yanka min ciki ma, kuma sun buga min kai” Sai kawai yasa dariya. “Ashe Noor dina ba jarumi ba ne, kadan fa suka yanka ka, kuma na sa police sun kama su” Matsawa ya yi sosai ya kwanta gefen Noor ya rumgumeshi ya matse hannunsa cikin nasa. “Allah ya baka lafiya ya raya min kai Noor kai kadai ka rage min sai Abbah na” Tashi na yi na fita wajen kiran likita saboda ya ce idan Noor ya farka a kirashi. _________________________________ Ku yi hakuri da wannan 🙏🙏🙏. [11/14, 4:00 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣6⃣ A GURGUJE.... Bana tunanin Bilal yana da wata hujja ko dalili na yin fushi da ni, duk kuwa da kasancesar Jibril ya sa an daureshi kuma an masa kai wulakanci da kasa guguwa a fuskar yan uwansu, amman idan har zai min adalci babu hannu a ciki balle kafata, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan domin tun lokacin da abun ya faru zuwa yau be taba daga waya ya kirani ba, idan kuma na kirashi sai ya dinga min magana cikiciki kamar baya son magana da ni, sau uku Baba Sulaiman yana daukar mutane suna dubashi bayan sallamoshi daga asibiti, ni kan ban jeba domin Inna taje ba bata dawo da farin rai ba duk da bata fada min abunda suka mata ko suka ce mata ba, na fahimcin hakan ne a fuskarta da kuma yanayinta. Al-hamdulillah sauki yana ta zuwa ma Noor ta ko ina domin a farko ya firgita sosai har na dauka ko kwakwalwarsa ta tabu ne, sai dai kulawar da likitocin Uduth da kuma addu'o'in da muke sai komai ya daidaita, tiyatar da aka masa ma cikin sati biyu ya samu sauki su kansu sun yaba da irin kyau fatar Noor, yana samun kula sosai da sosai wani abun da Jibril yake masa har mamaki yake bani kamar zai dauke sa ya cinye, a dan zaman da muka yi na asibitin Noor har ya sagarce abu kadan zai fara kuka yana kiran Daddynsa. A zaman da mukayi asibiti sau biyu Jibril na aman jini a gabana abun har sai da ya bani tsoro domin na dauka zuciyarsa ko kuma hanjin cikinsa zai amayar gaba daya, sai dai shi sai ya nuna kamar be damu ba, da alama abun ya zame masa jiki. Ana gobe za a sallamemu daga asibiti muka yi zaman kotu na karshe akan case din Baba a ranar na sha mamaki ashe matar da ta lakawa babanmu sata yayar Siraj ce daamn ina ganin alamaun haka sai dai ban tabbatar da sai yau da aka yanke hukunci na karshe, saboda yan uwan Siraj da suka zo sune wadanda aka tsaya masa a lokacin da aka yi shigar kotu ta farko case dinsa. Hukunci kazafi alkalin ya yanke mata su kuma aka yanke musu hukuncin kisa bisa ga shaidu da hujjoji kwarara da aka gabatar gaban kotu. Na yi farincikin sosai da sosai a wannan ranar daga ni har Inna da duk wani mai son ganin na kwatowa Baba hakkinsa, na yaba ma dpo daya tsaya kai da fata wajen ganin ya bi mana kadin mu. Abunda ya faru abun mamaki ne kuma abun a yabawa masa ne domin ba ko wane dan sanda bane zai kashe mutum kuma an hukunta shi kamar yadda doka ta ce, a ranar na ji kamar na zuba ruwa kasa na sha saboda farinciki mutane na ta zuwa har gida suna mana murna. Washe garin ranar aka sallamo Noor daga asibiti, a abun mamaki sai ga Zinatu ta zo ganinsa wani sukuku da ita kamar ba ita ba, na yi mamakin ganin ta zo gida dubashi bayan bata taba zuwa asibiti ganinsa ba. Da fari jajanta mana ta farayi akan abunda ya faru sannan ta dora da bayaninta. “Na san zaki yi mamakin rashin zuwa ganin Noor asibiti ko? Wallahi Jibril ne ya hanani, saboda na kirashi ina jajanta masa abunda ya faru sai ya gargade akan karna yarda na kusanci dansa, saboda yana ganin akwai aminci da shakuwa sosai a tsakanina da Siraj wata kila yana zargin zan masa wani abun ne” “Ayyah kin san dole ne ya tsorata kuma ya yi taka tsantsan saboda abubuwan da suka faru” “Amman ai ba halina daya da Siraj ba, miyasa zai yi tunanin haka” “Ban da abinki Zinatu ai shi hali ba a fuska akae ganeshi ba, shi ma Siraj din ai bamu dauka cewar zai yi haka ba, ni kaina a yanxu ba kowa zan yarda da shi ba balle kuma shi” “Haka ne, ni kaina da be koremu daga kamfanin ba, na kudiri aniyar aje aikin domin ba zan iya aiki inda ake ɗari ɗari da ni ba” “Ya sa kun aje aikin ne?” “Eh kwana biyu da faruwar hakan duka ya canja ma'aikatan kamfanin, yanxu kuma yana nan yana daukar wasu” “Ayya abun be yi dadi ba sorry” “Ba komai Allah kara lafiya, amman gaskiya Siraj ya bata mana suna Allah ya isar

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});