Chapter 7
Chapter 7
natsuwa a tare da ita idonta ya kumburo kamar ba nata ba. “Ina kika je Habiba?” A maimakon ta amsa ni sai kawai ta jefomin wata tambayar. “Inna na nan tsakar gida?” Kai na girgiza mata alamar a'a ina kallon yanyinta. Baya na yi hakan ya bata damar shigowa cikin gidan, hankalinta be kwanta ba sai kalle-kallen tsakar gidan take kamin da wuce ɗaki da sauri. Cikin rashin kuzari na rufa mata baya, ina shiga cikin ɗakin sai ta kama hannyena ta danƙa min sababin kuɗi ƴan dubu-dubu. “Nawwara ga dubu ashirin ɗin nan kije ki kai su saki Baba, daga baya sai a biyata kuɗinta” Wani jiri na ji ya kamani na kasa riƙe kuɗin, suka suɓuce daga hannuna suka watse ƙasa. Ita kanta ta tsorata da yanayi da sauri ta soma yin baya-baya tana fashewa da kuka. COMMENT AND SHARE *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 6⃣ Faɗuwa na yi saman guiwoyina na kai hannu na taɓa kuɗi, kamin na tada kai na kalleta. “Habiba ina kika samu wannan kuɗin?” “Tsinta na yi” Ta faɗa cikin kuka mai ƙarfi. Miƙewa na yi tsaye na matsa kusa da ita ina nunata da yatsa. “Karki raina min hankali Habiba, ta ya zaki tsince dubu ashiri a wannan halin?” Na faɗa ciki wata murya da ban san ina da ita ba. Sai ta rufe bakinta ta matsa baya. “Kyauta aka ba ni” Na watsa mata wani irin mahaukacin mari. “Ba ƙaramar yarinya ba ce ni, karki yi wasa da hankalina” “Mustapha ne ya ba ni” Ta sake faɗa tana dafe fuskarta saboda zafin marin da na yi mata. “Mustapha” Na maimaita sunan, tabbas Mustapha zai bata fiye da dubu ashiri, zai iya bata miliyan ma, amman idan ta ba shi mutuncinta. “Ya taya mutuncinki ne ya baki kuɗin ko kuma kin riga kin siyar masa ne?” Na tambaya gabana da dukan shida-shida, zuciyata kuma na ala-ala idan bata siyar ba. “Na siyar... Nawwara idan ba haka na yi babu inda wannan kuɗin zai fito, ki duba halin da Baba yake ciki, babu ruwan kowa da mu” Baya-baya na yi har sai da na jingina da ƙofar ɗakin. “Habiba kin kashe mu, ya kike tunanin Inna zata yi idan ta ji wannan abun? Kina tunanin wannan abun da kika aikata zai burge Baba? Da wane ido zaki kallesu” Da sauri ta ƙaraso kusa da ni ta riƙe hannuna tana kuka har muryarta na karkarwa. “Dan Allah karki faɗa musu, saboda su na yi wannan abun idan suka yi fushi da ni Wallahi mutuwa zan yi” “Kin san da wannan kika je kika siyar da mutuncinki? Allah da ya samu cikin wannan hali shi zai mana mafita, kina kunyar iyayenki amman baki kunyar Allah ki? yanzu ina kika son na ce mun samo wannan kuɗin?” Risinawa ta yi a gurin da cigaba da kuka mai taɓa zuciya. Sallamar Jidda ce ta razanar da mu daga ni har Habiba ɗin. Da sauri na fita waje domin na tareta karta shigo, na manta da hawayen da ke fuskata har sai da Jidda ta min magana. “Nawwara kuka kike yi?” Nasa hannu na share hawayen yayinda wasu suke ƙara zubo min, kuka ya zama biyu a yanzu. Hannu ta kama ta danka min dubu uku. “Ga dubu uku ku ƙara” “Ke kuma ina kika samu wannan kuɗin?” Na tambaya muryata na rawa. “Wayata na siyar vivo” A maimakon na yi mata godiya sai kawai na fashe da kuka, hakan ya karantar da ita ba wannan ne kawai damuwata ba, lallai da akwai wani abun a ƙasa. “Nawwara ko dai wani abun ya faru ne?” Ɗurƙushewa na yi a gurin na fashe da wani sabon kuka, har su Sakina suka yo kaina. Hakan yasa na katse kukan na miƙe tsaye na kama hannun Jidda muka shiga ɗaki. “Jidda Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin” Na faɗa ina nuna mata kuɗin. Ita kuma ta ɗora hannu saman kai tana faɗin “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Inna ta ji? ” “Bata sani ba, amman yanzu dole zata sani idan ta ga wannan kuɗin” “Habiba miyasa kika yi haka?” Jidda ta tambaya hawaye na bin fuskarta. Habiba kan aikin kuka kawai take, ta ma kasa ɗaga ido ta kalli Jidda. “Ina zaku ce kun samo wannan kuɗin Nawwara?” “Nima ban sani ba” “Karki faɗawa Inna, bari na je da kuɗin ni nasan yadda zan yi” Duƙawa ta yi ƙasa ta tsince kuɗin ta fita. Har na cira ƙafa zan bita sai Habiba ta kirani cikin muryar kuka. “Nawwara” Juyowa na yi na dawo. Sai ta tashi zaune “Dan Allah karki faɗawa Inna” “Ba zan faɗa ba” “Idan na yi tafiya ba zata ga ne ba?” “Ba zaki ita tafiya ba ne ba?” “Gurin zafi ya ke min sosai, bana iya haɗe ƙafafuna da kyau” Wani ƙololon bakin ciƙi na ji ya ratsa zuciyata. Cikin rashin ƙwarin jiki na fita waje na kunna wuta na ɗora mata ruwan zafi, Sakina kuma na ce su je su siye wani abu su ci da kuɗin da Baba Sulaiman ya basu. Sai da na cika mata roba da ruwan zafi sannan na zuba mata wasu a bota, da kaina na kai mata banɗaki, naje na riƙo ta kaita banɗakin. Tana gurin wankan Inna na ta dawo, fuskarta da alamun damuwa tun daga yanayin sallamarta na lura da hakan balle ma lokacin da ta zauna kusa da ni. “Kin dawo” Na tambaya ina ƙoƙarin ɓoye hawayena. “Eh mun kai musu kuɗin amman sun ce sai an cika sauran, ba su bar mu mun ganshi ba” “Allah yayi mana mafita” Na faɗa ina sauƙe ajiyar zuciya. Yayinda idona ke kallon Habiba ta tsaya tana leƙon. Na san tsoronta ɗaya kar Inna ta gane halin da take ciki, ina baƙin cikin halin da Habiba ta faɗa da ƙananan shekarunta ni kaina mai shekara ashirin da huɗu mutane kan kirani da ƙaramar yarinya balle ita mai sheƙaru goma sha bakwai. Tunanin dabarar da zan yi ma Inna ya ɗaukr hankalinta har Habiba ta samu ta wuce na ke, sai ga Jidda ta shigo kamar ta san ina nemanta. Saman tabarma ta zauna tana gaishe da Inna, ko da wasa Jidda bata kalli inda na ke ba, sai kawai ta fara jerawa Inna irin ƙaryar da data tsara. “Inna ga dubu ashirin na kawo, na siyar da kayan Kitchen ɗina ne, Maman Nura ma bata sani ba kuma idan ta ji zata min faɗa, dan Allah karku faɗa mata, inyaso idan Allah ya kawo sai ku biyani” Ya ƙarasa tana danƙawa Inna dubu ashirin ɗin, Inna ta saki baki. “Haba Jidda ayi haka?” “Zan iya muku komai Inna ni dai ki rufa min asiri karki faɗawa Maman Nura” “Ba zan faɗa ba, Allah ya saka miki da alheri ya biyaki da aljanna, ya baki miji na ƙwarai” Da ido na yi ma Habiba magana akan ta zo ta wuce saboda hankalin Inna ya ɗauko kan kuɗin, sannan na amsa da “Amin Jidda mun gode Allah ya bar zaman tare” “Ba komai ai yi ma kaine” Inna ta kalleni. “Ai ban ga ta zama ba ni kan, bari na je na samu Sulaiman mu kai musu cikon kuɗin ko?” “Inna ana kiran magariba kuma? Da dai kin haƙura har a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119