Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 111

Chapter 111

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma abokin Babansu da Kannen mahaifinsa airport suka hau Jirgin Abuja, shi kuma ya dawo gida. Tun daga ranar Jibril ya fara shirye shirye, a bokansa na baya da baya ja a jikin saboda abotarsa da Siraj yanzu kan ya zubar da wannan halin yaja kowa a jikinsa, sai dai be yarda ya yi amini a cikinsu ba domin a yanzu ya wayance da duniya. NAWWARA POV. Tun da aka saka lokacin Inna ta cigaba da shirye shiryenta kamar yadda ta fara, babu yadda Jidda ba tayi ba akan na je gurin gyaran jiki amman na ki, duk wani shirye shiryen da amarya take idan an kusa aurenta ni ban yi ba, ban da rama da baki ma babu abunda na yi, ranar da step mother dinsa da yayanta da wasu familyn Jibril suka kawo lefe ma na sha kuka sosai, basu karbi komai ba, ni ban ma san za a kawo lefen ba dan tun lokacin da aka saka mana rana ban taba daga waya na kira Jibril ba, shi ma kuma be kirani ba ko gaisawar da yake da Noor sai ya daina. Idan har zai yi wata magana da ta shafi auren sai dai ya kira Baba Sulaiman, idan kuma ya bukaci ganin Noor sai ya aiko da direbansa ya daukeshi a akai masa shi. Bilal kuma ban sake saka shi a idona ba, duk da ba fita na ke ba tun lokacin da aka saka min rana, Mama Turai ce take zuwa tana bani shike-shike na itatuwa da wasu abubuwa wasu na kan sha saboda fadan da take min, wasu kuma da na kafaici idonta sai na zubar. Ni dai bana shirin komai duk wani shiri daya danganci auren Inna ce take yi tare da Sakina da Jidda sai kuma yan uwnata da kuma yan Babban gida. Ina jin yadda suke shirya za su yi walima ni dai Uffan ban ce musu ba, a nan naji cewar Jibril ya ce ranar da aka daura auren zan tare, ji na yi kamar na rabe biyu saboda bakinciki. Kallo daya zaka min ka fahimci cewar bana son auren. Ana sauran kwana uku a daura auren familyn Jibril suka kawo danyin abinci kama daga shinkafa da duk wani abu da za a sarrafa a ranar bikin, sannan suka bada kudi mai yawa na hidima. Cikin kudin ne Inna ta diba ta gyara gidan aka cike inda duk da fashe aka shafe gidan sam kai bama ka ce gidan mu ba ne. Yau ta kama Assabar ranar da aka saka dauren aurena da Bilal, yau na tashi cikin damuwa da tunani, tun bakwai da rabi na safe Bilal ya turo min sakon da ya hanani sukuni. _I love you so much Nawwara, na yi abunda na yi ne saboda ki samu farinciki, ni san Mama ba zata taba bari ki samu farinciki a gidana ba ina miki fatar alheri_ Ina gama karanta sakon hawaye suka wanke min fuska, wani abu marar dadi ya zo ya tsaya min a zuciya. Karfe Goma dai dai na safe aka daura aurena da Jibril, a lokacin ne na fara kuka kamar an min mutuwa a ranar sai da na fita ran kowa daga Inna har yan uwan babana da yan'uwanta duk suka kasa fahimtata, Mama turai ce ta yi min fada sosai hakan yasa na daina kukan na koma yin na zuci. Da hudu na yamma aka yi walima a a Women development center, walimar da ta bawa kowa da mamaki saboda kayan da aka rana, ko da yake wasu sun riga sun ji cewar mai kudi zan aura, daman na san wasu gulma ce ta kaisu domin ni bana shiga mutane balle kuma biki amman aka taro sosai ga yan uwan Su Jibril suka yi nasu takeaway daban suka rabawa mutane. Malama Aisha ta yi nasiha sosai akan zamankewar aure da kuma hakuri da tsabta nidai duk abunda take fadi jinta kawai na ke dan ban shirya yi ma Jibril ko daya ba. Misali takwas na dare ya aiko da motoci daukar amarya motocin har sun yi yawa, Jidda ce ta cilasta ni ta yi min kwalliya ba dan na so ba, ta dauko min wata farar farar atamfa na saka, bayan na saka Inners farare sannan na saka fararen takalmi da farin gyale, Inna na min nasiha tana kuka kamar yadda nima na ke yi, sai aka wuce da ni babban gida su Baba Sulaiman da Yakunbo suka min tasu nasihar sai aka saka ni a mota ina ji ina gani aka dauki hanyar Sama road da ni. Na yi zaton gidan kai tsaye za a wuce da ni ganin ni bazarawa ce amman sai da aka biya wani babban gida inda yan uwan Jibril suka sauka aka kaini gurin Step mother dinsa da wasu kanen mahaifiyarsa da gwaggonsa suka min nasiha sannan aka sake sani a mota. Ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa wani katon gida mai farin fentin da gate golden color, ko ina na gidan haskene kamar da rana. Ana fitowa da ni daga mota na done kaina kasa ban sake dagawa ba har aka shiga da ni bedroom din gidan, da kafar dama na shiga kuma tare da bismillah. A tsayar gadon na zauna fuskata a bude hawaye kawai na ke ganin hakan yasa Jidda ta ja min mayafina ta rufe min fuska, yan uwansa suna ta daukata hoto wasu kuma na ta kokarin ganin fuskata sai Jidda ta hana. Bayan kamar minti arba'in Jibril ya shigo tare da abokansa sai zolayarsa suke, a gafe gado ya zauna, sannan wasu daga cikin abokansa suka shiga yi mana nasiha daga karshe suka rufe da addu'a. Ina jin lokacin da suka fita tare da nawa yan uwan da kuma Jidda, suka bar mu mu kadai a cikin dakin. Mun kusa minti talatin daga ni har shi babu wanda ya ce da wani uffan, baka jin komai sai shesshekar kukana. A hankali na ji ya kai hannunsa ya yaye mayafina ya dago fuskata, hawaye yake kamar yadda nima na ke yi. “Ki yi hakuri Nawwara na san ba ni kike so ba, na san na yi miki kutsu a rayuwarki, amman ina da tabbaci zaki auri Bilal nan da wani dan lokaci kadan, da shi zaki yi rayuwa dawwamamma irin wacce kike so” Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba. “Ada na yi tunanin idan an aureki zan kasance a cikin farinciki, amman wannan hawayen da na gani a idonki ya sani jin babu dadi kuma ya sani jin nadamar cilasta miki aurena” “Ba zan taba son ka ba Jibril, ka rabani da komai nawa, idan har kana da kunya a idonka ba zaka taba kai hannunka ka taba jikina ba, jikin macen da ka hada hotonta da wani ka ce karuwa ce mai neman maza da aurenta, ka rabani da mutumen da yake so tsakani da Allah saboda kawai ka samu farinciki, to bari na fada maka, ka kara matsowa da mutuwarka da bakinciki da damuwa da nadama a kusa da kai” Na fada ciki kuka. Sai ya yi saurin dauke kansa ya sauke wani numfashi da alama maganata bata masa dadi ba. Tashi ya yi tsaye ya cire Babbar rigarsa ya aje. “Taso mu yi sallah”

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});