Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 50

Chapter 50

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

marin shi kuma ya wuni yana ta mitar fitar da na yi, hakan yasa ya kulle kitchen kuma ya karɓe wayar da ke hannuna, wai naje gurin matar da nake zuwa ta bani abinci. Daga lokacin kullum da yunwa na ke wuni na kwana sai ya ga dama zai dauko wani abun ya bani jiki na rawa na karɓa na cinye, sai na koma abar tausayi, da na masa laifi kaɗan sai ya dakeni kamar wata ƴarsa, yana yawan shigowa da Aisha ta kwana a gidan ko ta wuni yasa na dafa musu abinci na kai musu ruwan wanka idan sun gama sai naje na ɗauke kwanukan, sai dai duk da haka ko da wasa be taɓa sakewa Aisha fuskar da zata rainani ba baya bari ta sakani aiki ko ta faɗa min wata maganar marar kyau idan ma an wulaƙanta a gidan to shi ne kawai yake da wannan damar. Wata rana ina zaune falo cikina na kukan yunwa, shi kuma yana ɗaki sai gashi ya fito ya jefo min wayata wai zan yi waya da Mama, sannan ya juya ya fice daga falon. “Babanki ba lafiya Nawwara, kuma bamu da komai, shine na ce idan da wani abu a hannunki ki aiko mana dan Allah, ko abinci sai mu siya” Shine abunda Mama ta roƙa ni kuma na ce mata zan aiko mata, bayan na kashe wayar na soma raira kukan da ban san ta inda yake fito min ba, ina haka abokinsa ya shigo hakan ba ƙaramin ɓata ran Jibril ya yi ba saboda ƙananan kayana ne jikina kuma abokin nasa ya ganni, ya yi min masifa sosai har da dukana ya yi akan haka. Muna cikin wannan halin Daddy ya yi rashin lafiya ya rasu, sai komai ya koma min sabo domin ganin Babu Daddy ya bawa Jibril damar azantar da ni da kalar azabar da yake so, sai dai bayan rasuwar Daddy sai Mahaifinsa ya kira ta wayarsa ya riƙa tambayata ko da wani abun ni dai ban taɓa faɗa masa ba. lokacin da Ya Jamal zai koma Jos sai ya biyo inda na ke dan mu gaisa, kamar ƙaddara sai ga Jibril ya dawo a ranar na sha duka wai akan me zan shigo masa gida, ya yi faɗa da Ya Jamal sosai har Ya Jamal yake masa faɗa akan yadda ya maidani kamar wata tsohuwa saboda wahala. Na sha fama a gidan Jibril ga shi baya son Sallah akan lokaci idan kuma na tasheshi sai ya yi ta masifa da ni, wata rana sai kamo tashar musulunci dake cikin receiver wa'azi wani babban malami yake akan irin azabar da ake ma masu wasa da sallah da kuma halin da suke shiga tun nan duniya, da gangan na cika murya dan yaji ashe kuwa saƙon ya isa dan tun daga wannan lokacin be sake wasa da sallah ba, wani lokacin da asuba har tashi na ke na tarar da ya riga ni tashi. Abun da na lura da shi Jibril yana da rayuwar turawa saboda zama da ya yi a can tun yana da ƙurciya har girma, gaba ɗaya rayuwarsa ta turawace, sai dai a wannan lokacin Jibril ba ya cin goro ma balle taba, rashin ilmin addinin islamiya ne yake ta cutar da shi, idan ina karatun ƙur'ane ya kan natsu yana saurarena musamman da asuba, akwai ranar da ya taɓa tambayata wai waya koya min karatu manyan surori haka na ce makarantar islamiya, daga ranar kuma be ƙara tambaya ba, ni kuma na maida tashar wa'azi ta zamo abar saurarena kullum, sai dai hakan be hana shi zalunta ta ba, be kuma hana shi yin fasiƙanci da Aisha ba, be kuma sanya shi ciyar da ni ba, ni dai iya abunda zan iya shidunsa da shi shine kishi, Jibril yana kishina sosai dan ko abokansa baya bari su gan ni, idan kuma wani ya yi magana da ni ko ya nuna kulawarsa akaina ranar zai wuni yana masifa kamar ya cinye kansa. Haka na bi na lalace ba ƙarfin yau bare na gobe, wata rana mahaifinsa ya aiko da mota aka ɗauko ni aka kaini gidansa, muka gaisa ya ɗauki wayarsa ya kira Jibril yana zuwa ya fara masa akan yadda ya ga na lalace sai Jibril ya yi tunanin ko na faɗa masa wani abun ne, bayan ya sallame ni da kuɗi mai yawa muka fito ni da Jibril na shiga motarsa muka kama hanyar gida. Sai da ya tabbatar na yi nisa da gida sannan ya faka motarsa ya fisgoni da ƙarfi ya jefar a gefen titi ya koma cikin motar ya yi tafiyarsa ya bar ni a gurin. Haka na zauna a gurin har aka kira magariba sai da wani mutun ya zo zai wuce ya tsaya ya tambayeni na nemi ya taimaka min ya taimaka ya ɗauko ni a motarsa ya kawoni gida, a ranar sai da Jibril ya mareni kuma ya yi min duka mai kyau. Washe gari sai ga Momy ta zo gidan ta karɓu kuɗin da Daddynsa ya bani, ni dai na roƙeta akan ta raba biyu ta aikawa Baba rabi duk da nasan ba zata yi ba. Jibril ya kan kirani da ko wane irin suna, idan na yi masa wani abu ba dai'dai ba sai ya ce min annoba ko baƙin maciji, yana yawan faɗar cewar ya fi son mutuwarsa da ni. Tun da ya aureni be taɓa bari naje gida ganin Baba ba, gidan momy kawai na yake kaini shi na kuma da dare yake kaini bayan ƴan mintuna ya ce na taso mu dawo gida. Ranar da zamuje raka daddynsa zuwa airport ya mareni a bainar jama'a saboda kawai na zubar da ice cream ba da gangan ba, aiko ranar ya sha faɗa a gurin mahaifinsa har sai da ya raina kansa. Bayan mun dawo gida ya wuce ɗakina na yi kuka har na gode Allah, daga nan bachi ya yi gaba da ni ina cikin bachin na soma jin ana shafani, hakan yasa na farka a firgice ina ihu, sai ya ji haushin ihun da na yi ya mare ni ya riƙa ya jefar ƙasa har sai da kaina ya bugu da madubin gadon, sai kuma ya taso ya doso inda na ke gadan-gadan ya dake fiskgata ya jefa saman gadon. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣2⃣ A ranar Jibril ya maidani cikankiyar mace, da safe ni na taimakawa kaina na shiga banɗaki da kaina na haɗa ruwa na yi wanka sannan na ɗora da alwala na fito a wahalce na yi sallah. Da safe be shigo ya tambayi ya na tashi ba duk da yasan halin da ya barni, ban fito daga ɗakin ba sai tara da rabi na safe kai tsaye na nufi kitchen sai na samu ya aje min makaroni da mai da tumatir da sauran kayan da zan sanrafa na dafa makaroni ɗin, cike da tausayin kaina na dafa makaronin ɗin ne na dawo ɗaki ina ta aikin kuka. Haka nake wuni na kwana babu ruwan Jibril da ni a gidan, tun daga ranar kuma be saki kuni da sunan zamantakewar aure ba, idan baya nan gidan Ummu Faisak na ke zuwa na zauna musha fira ta haka nake samu na cika cikina

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});