Chapter 58
Chapter 58
yi min magana ba tare da ya kalleni ba. “Congratulations Miss Nawwara, kin samu baban promotion zuwa office ɗin Oga Jibril you're now his new PA, Rabi zata zo ta miki bayanin komai” Mamaki ne na cikani new pa haka kawai bayan bana da dogon karatu? “Amman ban yi wani zurfin karatun da za a bani wannan matsayin ba” Kamar daga sama na ji muryar da nafi tsana a duniyar nan wato muryar Jibril ashe yana bayana ta gurin kujerar da ke farkon shigowa, ni ban ma san da shi ba kasancewar ban kalli gurinba tun da na shigo idona yana kan abokin nasa. “Shi kuma ga damar baki idan kuma ba zaki yi ba you can leave” Ba yabo ba fallasa ya faɗi haka ya kana ya miƙe tsaye suka fice tare da abokin nasa suka barni nan tsaye ina mamaki. __________________________________________ Kalamaina sun yi ƙaranci su gode muku fans akan irin soyayyar da kuke nunawa littafin nan. #Team RB #Team Nawwara #Team Jibril #Team Mustapha #Team bilal Na gode na gode sosai Nawwara ta ce a gaishe da masoyanta.😜 Soyayyar da kuke nunawa littafin nan a yanzu Allah yasa ku nuna min irinta a littafi na gaba mai suna HAFSATU MANGA labarin ƙauye. Ina muku son so Fisabilillah a duk inda masoyin littafin nan yajke. 😍 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣6⃣ Wata kyakkyawar mace ce ta shigo mai far'ar fuska da kuma ta ruhi domin kuwa muna haɗa ido da ita sai naji kamar na santa, hannu ta miƙa min. “Sannu sunana Rabi Ismail” “Nawwara” Na faɗa ina miƙa mata nawa hannun. “Zo muje zan nuna yadda aikin naki yake” Tana gaba ina biye har muka isa office ɗin Jibril, a gaban computer ta fara isa ta nuna min yadda zan danna na buɗe ƙofar farko ta shigowa, sannan muka ƙarasa ciki ta nuna abubuwan da zan yi da zarar na iso da safe, sai kuma abubuwan da Jibril yake buƙata da kuma tsarin yadda zan jera masa komai. “Aikinki ne ki sanar da shi idan zai yi meeting kamin lokacin ya cika, da zarar ya shigo da wuri saki sanar shi duka abubuwan da zai yi, wayarsa da ke nan office ke zaki riƙa amsa ta, idan wani na buƙatar ganawa da shi ke zaki tabbatar da tsaro kuma ke saki saka time, yanzu kan ba zaki tashi aiki ba sai 4:00pm, kuma dole ne ki shigo 8:00am, masu kowa ƙorafi ko wani bayani na cikin kamfanin nan ke zaki kula da su shi kuma sai kije ki masa bayani a tsanake, aikinki ne gogewa da kuma gyara ɗakin nan, idan na shigo dole ne zaki tashi ki gaishe kuma ki tambayeshi abunda yake buƙata” Ya juya ta ɗauko wata leda dake saman teburinsa ta miƙa min. “Wannan kuɗi ne naira dubu ɗari biyar zaki siye tufafin da zaki saka masu kyau saboda Oga baya son ana saka tufafi marar rsada musamman yanzu da kike new PA ɗinsa, wannan kuma makullin gida ne dake Abdullahi Fodio Road a gidan zaki zauna komai akwai a ciki” Na sauke ajiyar zuciya ina kallon makullin data fiddo daga aljihunta tana miƙa min. “Daman idan mutun ya fara aiki haka kuke masa a wannan kamfanin?” “A'a Karamci ne kawai irin ya Oga Jibril ina tunanin kina da muhimmanci a gareshi sosai shiyasa” “Ki bar kuɗin ki aje makullin kuma ki faɗa masa ba zan yi aikin ba” “Amman miyasa?” Ban bata amsa ba na juyo na yi tafowata zuciyata na ta raya min abubuwa da dama, idan har na yarda na yi aikin nan tau Jibril ya ƙwareni kuma duk wulaƙancin da ya yi ya tashi a banza kenan, taya mutun zai wulaƙanta ni sai kuma na dawo na fara aiki a tare da shi? Ya samu danar wulaƙanta ni saboda kuɗin da yake da su, yanzu kuma sai na yarda ya yi amfani da kuɗin ya maye gurbin abunda ya aikata? Lallai ni wawuya ce. Haka na ke ta tunanina har na iso reception na ɗauki wata a inda na aje tare da Hijabi na saka na nufi ƙofar fita ba tare da na saka lokacin da na tashi ba. “Nawancy” Da sauri na juyo jin muryar Bilal, sai na sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake min. “Ashe kin shigo?” “Ee amman yanzu zan koma” “Har kin gama aikin ne?” “Ee yau baka kirani ba, duk na damu” Ɗan murmushi ya yi muna fara takawa tare yana faɗa min akwai abunda ya ɗauke masa hankali. “Amman ko minene ai ya kamata ka min ko da massage ne” “Haka ne am sorry my dear ba zan sake ba” Hango Jibril da na yi a tsaye a gate ɗin garden yasa na washe haƙura ina kallon Bilal. “Ma yafe maka ammam karka yarda ka ƙara” “Allah ya Huci ran sarauniya ba zan ma sake ba” Haka mike tafiya tare muna firarmu sai dai yadda na ke dariya sai ka ɗauka wani labarin ban dariya ne yake ba ni. Muna dosar gate Jibril kuma ya doso cikin kamfanin tare da mutumen da suke magana tare. “Good Morning Sir” Bilal ya faɗa cikin girmamawa a lokacin da Jibrilya kawo kusa da mu, ni kan ko kallonsa ban yi ba har sai da na ji maganar da ke fitowa daga bakinsa. “Miye tsakaninka da wannan yarinyar?” Ƙasa Bilal ya yi da kansa ya kasa amsawa kamar mai tsoro sannan ya buɗe baki xai yi magana sai na yi karaf na karɓe duk da ba ni ya tambaya ba. “Wanda zan aura ne” Sai ya juyo kaina ya kalli fuska a ɗaure ya ce “Bamu gina wannan kamfanin domin masoyaba, idan zaku yi soyayyarku sai ku yi ta a can waje nan kam domin aiki muka ɗaukeku dan haka bama buƙatar ganin wani abu daya alaƙancin soyayya a nan. Ku wuce gurin aikinku” Kallona Bilal ya yi ya sakar min murmushi. “Sorry Nawancy zan kira ki” “Okay Dear I love you” “I love you too” ya mayarmin da martani sannan ya juya ya koma ciki. Ina kallon yadda Jibril ya ɗauke kai ya haɗe yawu da ƙarfi, ya saka hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma ya jimƙeshi sosai. “Wuce kije office” “Ba zanyi aikin ba” Na bashi amsa kai tsaye, sai ya ɗaga kafaɗunaa alamar ko a ajikinsa. Ni kuma na kama hanyar fita daga harabar kamfanin. Ina cikin Napep kira ya shigo wayata da fari na ɗaukar Jibril duk kasancewar baƙuwar number ce, hakan yasa na ƙi ɗauka, sai dai har na isa gida ba a daina kiran ba da zarar ta tsinke sai a sake kira ni kuma na ƙi na ɗaga. Ko da na shigo Inna na wankin tufafinta na sakawa, da sauri na cire Hijabina na aje na tsuma hannayena cikin wanki ina faɗin ta cire nata. “Amman dai yau ma kin yi saurin dawowa” “Na gama aikin ne da wuri” “Bayan fitarki Ɗansandan nan ya zo be tararda ke ba ya ce zai sake dawowa” “Ya yi wata magana ne?” “Cewa Ya yi suna nan suna cigaba da bincike amman yana son ganawa da ke, ya kuma tambayeni akan yadda muka tararda Babanku lokacin da muka je duba shi” “Uhmm su dai suka sani” “Wayarki tana ƙara” “Barta a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119