Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rawa yake naje gida na labartawa Inna wannan labarin. A hankali wata mota da ta fito ɗaga gidansu Manjo ta doso inda na ke, mai maotar na kawowa daidai ni sai ya sauke baƙin gilashin motarsa. Ashe Mustapha ne, cikin shigar manyan kaya wato farar shadda da kuma barar hula sajensa na kwanta sai sheƙi yake, da alama jumma'a zai je tun da yau friday, fuskarsa cike da annuri, sai dai bana mutanen kirki ba, na kuɗi da kuma kyawun hallita da suka nuna isa a fuskarsa. Kallona yake ba ko ƙyafta ido, ni kuma na bawa banza ajiyarsa sam babu tsoro a tare da ni saboda na shirya tarbar ko minene daga gareshi. Haka nasa kai na wuce na barshi a gurin zuciyata har wani zafi take min saboda da tsanarsa. Da sallama na shiga gida, Inna da dpo suka haɗa baki gurin amsa min, hakan yasa naji kamar na janyo sallamar na mayar da ita a bakina, yau ma ya taki sa'a na sauke idona cikin nasa hakan yasa ni jin kamar na ƙarasa a inda yake zaune gaban Inna na shaƙe wuyansa. THE GAME IS ABOUT TO START .*RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣4⃣ Na ɗauke kaina kamar ban san da zaman mutun a gurin da Inna take ba. “Har kin dawo?” Inna ta tambaya, ni kuma na nufi ƙofar ɗakin mu ina amsa mata domin bana son na juyo idona ya haɗu da na azzalumin mutunen nan. “Eh Inna” Na ɗaga labulen ɗakin mu na shige zuciya cike da abubuwa guda biyu farincikin abunda Bilal ya yi mana da kuma baƙincikin ganin dpo a gidanmu. Kayan da ke hannuna ma saman katifa na jefasu, na zauna ƙasa raina a jagule. Jidda ce ta faɗo min a rai, ya kamata ace na tabarta masa samun aikin nan da na yi, har na unƙura zan tashi na fita sai na tuna dpo yana tsakar gida, hakan yasa na koma na zauna, sai tunanin Bilal ya dawo min rai. Lokaci zuwa lokaci na kan samu kaina da murmushi tuna irin abubuwan alherin da Bilal yake mana, wanda na san har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa saka masa da abunda ya yi min, ya sadaukarda abubuwa da dama saboda farincikina. Kiran da Noor yake min a tsakar gida ne ya katse min tunani, ina unƙurin tashi na fita sai ya shigo ɗakin da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa. “Momy duba aka raɓa mana sabon littafi a makaranta” Na faɗaɗa fuskata da murmushi ina karɓar littafi tare da buɗewa ina dubawa, littafi rubutu ne mai hoton ciyaman, da alama ya kai musu ziyara ne, daman naji a rediyo ana cewar zai ziyarci makarantu. “Momy da idona na ga Ciyaman yana jawabi har da godiya ya yi mana, sai aka raba mana littafai” Na kai hannu na shafa fuskarsa ina dariya “Amman Ciyaman ya kyauta da ya bari Noor ya ganshi” Sai ya ƙyalƙyale da dariya ya rumgume ni. Haka ɗa na yake, masu kuɗi da ƴan siyasa suna burgeshi ko a mota ya ga mutun sai ya tsaya kallonsa har sai ya daina hangoshi sannan hankalinsa ya kwanta, a ranar kan labari sai abunda ya manta. Zaunar da shi na yi saman jikina, na soma cire masa talkamin makaranta tare da safa, shi kuma yana duba littafin tare da karantawa. Habiba ce ta shigo ɗakin babu ko sallama, kana ganinta kasan a gajiye take jikar littafanta ma a bakin ƙofa ta sakesu ta kwanta kusa da ni tana ƙoƙarin cire hijabinta. “Lafiya kike kuwa?” Na tambaya ina kallonta, Noor kuma ya tashi da sauri ya fita waje. Ɗan guntun tsaki taja irin na wanda baya son magana kana ta ce “Wallahi bana jindaɗi, amai na biyu makaranta kuma kaina ciwo yake sosai” Dukan shida-shida gabana ya yi tsaɓanin uku-uku da na kowa keyi, a take nima na ji ciwon kan ya kamani, dafe kaina na yi na lumshe ido yana sauraren yadda zuciyata take bugawa. Ƙoƙarin kawarda abunda ke zuciyata nake, yes cikin zai iya nunawa a sati biyu amman ba ko wanne ba, cikin Noor ma a sati biyu aka gano ina da ciki balle kuma Habiba da ke da wata ɗaya har da sati ɗaya, tunda ranar litanin Inna zata cika wata ɗaya da sati biyu cikin taƙaba. ‘No ba ciki ba ne, maleriya ce inshallah ba ciki ba ne’ Zancen da nake a zuci shi Habiba take a zahiri. “Nawwara na ce ƙila maleriya ce, saboda idona har nauyi yake” Na buɗe ido na kalleta tare da ɗaga mata kai alamar ‘Eh’ “Ita ce, bari na aika Sakina ta siyo miki Anti-Malaria shago” “Tau” Ta juyo min baya tana dafe da kai, hakan ya bawa hawayen da ke maƙƙale a idona saukowa zuwa kumatuna, ban taɓa tabbatar da hawaye na da zafi ba sai a wannan lokacin, gumi ne ya soma keto min ta ko ina kamar wacce ta yi rashin gaskiya. Cikin hanzari na kai hannu na share hawayena saboda motsin Sakina da na ji zata shigo ɗakin, sai na miƙe tsaye na nufi ƙofar fita. Ashe magana take min ban ji ba har sai da ta riƙoni. “Anty Nawwara, wai ɗan sanda nan yana kiranki a waje” Da kai na iya amsa mata, daman Hijabin da na shigo da shi yana jikina sai kawai na zarce ƙofar gida, har ga Allah ba dan ina cikin ruɗu ba babu abunda zai sa dpo nan ya kirani kuma har na tafi. Tsaye na yi masa idona a ƙasa ina ta tunanin makomarmu, idan har ta tabbata Habiba na da ciki mun shiga uku, lallai mutane zasu gasgata cewar Mahaifinmu ya yi sata, tun da ga ƴar'uwata da cikin shege, duk wani yabo da ganin mutuncinmu da ake a unguwarnan zai zube, ya Inna zata yi idan ta ji Habiba na da ciki? Ita kanta kanta Habiba ya zata kasance? Ni kaina da suka san na yi aure lokacin da na haifi Noor sai da suka kira shi shege balle kuma Habiba. “Nawwara” Kiran sunana da dpo ya yi na yasa na dawo hayyacina har na kalleshi, ashe tun da na zo gurin magana yake min amman ban fahimtaba saboda tashin hankalin da ke zuciyata. “Ki yi haƙuri dan Allah, ki share hawayenki, duk abunda na faɗa miki zanyi ki yarda da ni” Sai a lokacin na kula da hawayen da ke ta zuba a idona, cikin sauri na sa Hijabina na gogesu ina jan magina. Sai ya ɗora da zancen da ban gane masa ba, ba dan kuma yana min wani yaren ba sai dan hankalina baya gurin, babu komai a zuciyata sai fargaba tunani da kuma zullumin abunda zai je ya dawo, na tabbatar da za'a auna jinina a lokacin za a tarar ya haura ɗari uku da wani abu bama ɗari biyu ba. A gurin na barshi tsaye na shige gida ba tare da hawayen sun tsaya min ba, haɗa ido da muka yi da Inna yasa idona ƙara cika da ƙwalla, tausayinsa ne ya kamani tabbas Mahaifiyata ba zata iya ɗaukar wannan ba, duka-duka yaushe ta rasa mahaifina kuma yanzu ta ji Habiba na da ciki. “Lafiya?” Tambayar da ta yi min ne yasa na share hawayena ina ƙoƙarin ƙirƙiro ƙaryar da zan mata. “Ba

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});