Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da abincin gidanta, ban taɓa labarta mata irin yadda Jibril yake azabtar da ni ba, sai dai tasan irin zaman da nake a gidan ko da yaushe tana ƙoƙarin koya min abubuwan da zan yi na burge Jibril ko kuma na janyo hankalinsa akaina. Ranar wata lahadi yana zaune gida na same shi a garden inda yake zaune yana hutuwa na risina har ƙasa na roƙoshi akan ya taimaka ya sake ni, amman ya ƙi har ma ya soma iƙirarin shi yanzu ya fara zama da ni, sai dai ya taimaka min ya ba ni makullin kitchen, daga ranar kullum abinci kala uku na ke girkawa wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ko kallonsa ba ya yi. Yana zaune falo shi da abokinsa ni kuma na nufi kitchen saboda miyar da na ɗora karta ƙone, ina nufar kitchen ina jin yadda yake faɗawa abokinsa wai Aisha tana da ciki and he's so happy and excited akan cikin da aka samu babu aure, ina kitchen ɗin na tarar da ni ya shaƙe ni yana tambayar ina Hijabina taya zan fito haka babu mayafi a gaban abokinsa, da kansa yaje ɗakina ya ɗauko min Hijab na saka sannan na wuce ta gaban abokinsa, har abokin yana zolayarsa wai shi yana ganin matan wasu amman shi ba a ganin nasa. Ma samu sasauci sosai daga lokacin da ya bani makullin kitchen ɗin saboda kullum zan girka na ci, sai dai wata rana sai na gama girkin na ji bana so ko kuma na ji wannan na ke so bana son wannan abu a kaɗan sai amai, nan da nan zazzaɓi ya rufeni haka na kwashe kwana uku ina fama da rashin lafiya kamar zan mutu amman ko da rana ɗaya Jibril be taɓa shigowa ya duba lafiya na ke ba. Ranar da na samu sa'ida na ɗaure na fito falo saboda na gaji da zaman ɗaki, ranar sai ya shigo ya sameni falo yadda ya ga na rame shi kansa ya bashi tsoro, da kanshi yana zo yana tambayar me ke damuna cikin nuna halin ko in kula saboda kawai na ce be damu ba. Bayan na faɗa masa ya ɗauko min roba ya ce na yi fitsari sai kuma ya ɗibi jinina, ya bani wasu magunguna. Washe gari sai gashi ya dawo cikin gidan a rikice kai tsaye ɗaki na ya nufa. “Ina kika samu ciki?” Shine abunda ya fara tambayata fuskarsa na nuna tsantsar ɓacin rai da ke tare da shi, ni kuma na ɗago kai a hankali na kalleshi na maida kaina domin bana iya amsa masa. “Ni ban shirya haihuwa yanzu ba, saboda haka ki san yadda zaki yi da cikin nan, daga yin abu sau ɗaya sai ace ciki ya shiga, zubar da shi zan yi ko kuma ya zama ƙarshen auren mu” Ni dai uffan ban ce da shi ba ina ta aikin kuka, ban san miya aikata ba bayan kwana biyu ya shigo ɗakina ya bani lemu ina sha hankalina ya ɓace ban farko ba sai da aka kira assalati. A week later ya ɗauki ni zuwa gidan Daddynsa ashe ya kira Baba ni ban ma sani ba sai da muka isa, a falon ya yi min tozarci da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ya tozarta ya yi min ƙazafi a gaban Mahaifina da mahaifinsa ya fiddo wasu hotuna na tsiraici tare da wani ya nuna musu kuma ya yi min ƙazafin cewar na aikata zina da wani a waje kuma da aurensa. Ban iya cewa komai ba sai aikin kuka, har ga Allah ban san inda ya samo wannan hoton ba amman ni dai nasan babu wani namiji da wata mu'amala ta taɓa shiga tsakaninmu sai shi amman ya juya baya ya murje ido ya ce ba nashi ba ne, a ranar na riƙa hannunsa na riƙe shi akan ya karɓi cikin nan sai ya tureni yana faɗin taya zai karɓi cikin da ba nasa ba. “Ni kan ban haifi ƴar iskaba kuma na san irin tarbiyar da na bawa ƴata” Shine abunda Baba ya faɗa, Shi kuma ya sakeni saki uku mahaifinsa ya ce idan an saki mace a lokaci ɗaya kamar saki ɗaya ne dan haka ya maida aurensa ya yi haƙuri, sai kawai ya ce ya sani saki ɗaya ya sake ni saki biyu ya sake ni saki uku saboda kawai kar na koma gidansa sai Baba ya kama ni muka fito daga gidan, gidan aurana na koma na ɗauke duk abu na wa mai muhimmanci daga nan kai tsaye muka nufi tashar mota, sai dai ba mu kawo sokoto ba sai washe gari saboda ko da muka taso yamma ta yi sosai a zaria muna kwana, dawowata ta bawa kowa mamaki musamman da aka fahimcin ina da ciki sai aka fara zancen cewar ba aure na je yi ba iskaci naje yi wasu kuma su ce daman haka sai ya faru tun da Baba ya nuna kwaɗayinsa a kan abun duniya, har ma da masu cewa babu makarantar da na tafi. Baba ne yake ta dawainiya da ni shine ci na shana har na haihu da ƙarma ƙarama ya samo aka yanka rago ranar suna, yaro ya ci suna Muhammad Noor. Bayan na haihu Inna ta ce ya faɗa masa sai azo a auna jininsa da na yaron amman Baba ya ce ba zai yi ba, ai namiji idan ya girma shi zai nemi ubansa, kuma yasan komai daren daɗewa sai Jibril ya dawo gurin ɗansa. Da wannan na zauna a gida ina rainon ɗana har ya cika shekara biyu da wasu watanni, a lokacin ne muka fara sabo da Bilal saboda gaisuwar arziki da take haɗa ni da shi, abotarmu da Jidda kuma ta ƙullu sosai, a gunta na ke jin labarin ai mahaifin Zinatu yana ɗaukar aikin local government har da masu ssce, haka na ɗauki takarduna naje gidansu Zinatu neman ta yi ma Babanta magana akan aikin amman sai ta tsaya tana kallona har ma da zolayata wai ina karatun da aka ce ina yi a waje har tana dariya, daga baya take faɗa min cewar mahaifinta ya ce sai masu degree yake ɗauka. A hanyata ta dawowa daga gidansu na haɗu da da Faruk, tun daga unguwar yake bina har sai da na iso gida sannan ya yi min magana, ya kuma gabatar min da kansa ni kuma na faɗa masa ko wacece ni ban ɓoye masa komai. Daga nan sai alaƙa mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninmu har ta kai ga neman aure duk da ban so haka ba Baba da Inna suka buƙaci na aureshi tun da har ya nuna yana son aurena. Faruk mutum ne mai hallaci da kawaici yana so na tsakani da Allah, da kansa ya ce na daina cewa Noor babansa ya mutu saboda na yi masa ƙarya tun farƙo na faɗa masa cewar Baban Noor ya rasu ne, wasu mazan basa yarda mace ta yi aure da ƴaƴan wasu a gidansu amman shi kan ba zaka taɓa gane cewar ba shine ya haifi Noor ba, duk abunda ya kamata uba ya yi ma ɗansa shi yake ma Noor ba dan kuma baya da ƴaƴanba, domin yana da aure har da yara biyar, sai dai yana aiki ne a

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});