Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 104

Chapter 104

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

babu wanda ya zauna, Jibril ya matsowa kusa da shi sai Dsp din ya shiga tsakani. “Ba sai ka taba shi, ai hukunci za a yanke masa dai dai da abunda ya aikata, abun jindadi ma ya amsa laifinsa da kansa, kuma mutane da muka kama a gidan da aka aje Noor sun fadi cewar shi ya saka su kuma be karyata ba” “Ba komai zan masa ba tambayarsa kawai zan yi” Jibril ya fada yana jin kamar ya kama wuyan Siraj ya shake. “Mina hana maka Siraj? Mina maka ka aikata min haka? Me ka nema na hanaka? Mi Rabi ta maka? Me Noor ya maka?” Ya dago kansa da idanuwansa da suka kumbure saboda duka, har baya iya gani da idon sosai gaba daya an canja masa kamani kamar ba shi ba. “Baka min komai ba Jibril sai alheri, ni kaina ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sai dai babu yadda zan yi saboda zuciya ta dibeni tun farko, abun da na ke ta kokarinyi da gani na fika Jibril, saboda ina bakincikin ace ni ne a karkashinka ba kai ne a karkashina ba, irin rufin asirin da Allah ya baka na so na samu da karfi sai ya gagara, na sa an kashe Rabi ne saboda ta tona min asiri ta ci amanata kuma na san nima kasheni za ayi, a a yayinda ita kuma za a yafe mata kuma za a yaba mata, Noor ya ganni lokacin da na yi kokarin kasheshi shiyasa na sace shi nasa a kashe shi saboda kar wata rana ya fadi sai gashi Rabi ta lalata komai” “Hassadace ta cuce ka Siraj ka ci amanar kanka kuma daman hassada ga mai rabo taki ce, mun dauki amana mun baka sai ka cuce mu Allah ya waddaranka Siraj” Cewar Abbah cike da bacin rai. Jibril ya matso kusa da shi ya chakumi wuyansa ya matse game yana kokarin aikashi lahira, daker aka kwaci Siraj a hannun Jibril har aka wuce da shi Nawwara kawai yake harara idonshi na kanta. “Ka kwantar da hankalinka Jibril kotu za ta yi komai, litanin din nan muke son fara zaman kotu alkali zai yanke masa hukuncin ai” Cewar Dsp yana rike da Jibril ta dake ta faman huci. Daga gidan maza station suka wuce saboda wasu statement din Nawwara da za a dauka. Sun yi awa daya a gurin sannan suka baro gurin tare da tawagar yan sanda zuwa rinjin sambo gidan wani dan'uwan Rabi da take zaune a gidansa. Ko da suka je sun tararda jama'a anyi dandazo a gurin duk kuwa da kasancewar an rufe gidan gaba daya kuma sun bar police uku da zasu yi gadin gurin. Suna isa police din suka bude musu gidan, Nawwara ce a baya tare da Jibril, ya yinda Dsp yake can gaba tare da su Abbah da kuma wasu police din. “Are you sure zaki iya kallon gawar Rabi? Ance fa dadsatsata suka yi” Tsayawa ta yi cak sai ya kalleshi. “Idan kin san zai daga miki karki kalla” Sai kawai ta fashe da kuka. “Duk laifina ne” “Ba laifinki ba ne, haka Allah ya tsara” Kamin ta kara cewa wani abu sai ga wayarta tana ringing, Baba Sulaiman ya kira ya ji inda suke ya zo, da kanta ta tsaya tana masa kwatanci sai Jibril ya shiga ciki ya bar nan waje tsaye. Shi kansa da yaga gawar Rabi sai da hankalinsa ya tashi domin datsata aka yi aka mata guntu-guntu ko ina ya bace da jini, suna cikin gurin su Baba Sulaiman da wasu kanenn mahaifin Nawwara suka iso, isowarsu ta yi daidai da isowar yan uwan Rabi kana kallonsu zaka gane ba hausawa ba ne dukansu yanayin shigarsu da kuma tsagen da ke fuskarsu, da kuka suka shiga cikin gidan maza uku mata biyu a nan suka yi ta ihu har da mai faduwa tana tashi tana buga kasa. Daker suka tsagaita kuka har aka dauko gawarta aka fito da ita zuwa motar police. NAWWARA POV. Ana fitowa da gawarta hankalina ya tashi sosai lallai mai rai ba komai ba ne, duk kyau rabi da far'arta sun tafi kenan, a gurin na raina kaina saboda ina ganin kamar sakacina ne yasa hakan ta faru, amman Jibril ya yi kokarin dorawa kansa laifin ko kuma ya ce min haka Allah ya tsara zai faru, mahaifin Jibril ne yaso a tsaya a yi mata jina'iza a nan amman yan uwanta suka ki, a dole tasa ya hakura ya bawa police kudin mai dan su rakasu har can kogi inda iyayenta suke, a ranar yan uwanta suka juya suka koma a mota tare da gawarta da kuma rakiyar yan sanda. Mahaifin Jibril kuma muka dawo asibiti tare da shi ya duba Noor ya yi masa addu'a tare da step mother dinsa, sannan ya yi mana bankwana akan cewar zai koma abuja a yau gobe tun da safe zai hau wani jirgin yaje kogi saboda ayi jana'iza a tare da shi, sosai ya so Jibril ya bishi amman Jibril ya ki wai sai yaga idon dansa, Abbah ya sashi gaba yana ta masa nasiha sosai akan rayuwa da kuma abubuwan da suka faru. Da yamma lis Abbah ya yi mana sallama ya bar asibitin kasancewar an kira an fada masa jirginsa ya kusa tashi. Mutane na ta zuwa ganin Noor makota da kuma yan'uwa da abokan arziki ciki har da wasu familyn Jibril da suke garin nan da kuma abokansa. Gurare takwas da rabi na dare Jibril ya bar asibitin saboda kiranshi da aka yi, ko minti goma ba ayi ba sai ga Jidda ta shigo tare da Mustapha i was very surprised dana gansu tare saboda ni na ma dauka Mustapha baya kasar nan dan tun lokacin da nayi magana da shi ban sake hada hanya da shi ba, hankalin Jidda ya tashi sosai har da kukanta Mustapha kan yana tsaye kan Noor yana masa kallon da ban san na minene ba. “Ya aka yi aka barku kuka shigo?” Na tambaya bayan Jidda ta zauna har yana kokarin bude abincin da ta zo da shi. Sai Mustapha ya kanne min ido daya yana murmushi “Cin hanci na bayar” Na sauke kaina kasa, sai ya yi yar dariya kadan ya ce. “Allah ya kara sauki ya tsare gaba, kai gaskiya an yi arziki da mun rasa yaro mai kyau, ni da nake son na hada surukuta da ke, dan gaskiya idan na haifi ya mace sai ta auri Noor ko kuma da na ya auri yarki” Ya fada yana dariya kamar babu abunda ya dame shi, ni dai bance masa komai ba, Jidda kuma ta kasa daga kai ta kalleni duk tabi ta tsargu. “Ba ganin danki kawai na zo ba Nawwara, na zo na fada miki cewar na samu matar da na ke so” Sai Jidda ta yi saurin kallonshi. “Haba Mustapha wannan wane irin magana ne, baka ga halin da take ciki ba? Ko ma minene ai ni ya kamata na fada mata” “Na ga kamar ba zaka iya fada mata ba ne, shiyasa ni na zabi fada mata da kaina” “Amman dai ba a yanzu ya dace ka yi wannan maganar ba” “Fine ba zan kara ba” Ya fada yana daga hannunsa sama

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});