Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 96

Chapter 96

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rayuwar, ni ce na yi ruwa na yi tsaki a rayuwar mutumen da na fi tsana a duniya, bana da matsala a yanzu sai ta mutum biyu Bilal da kuma Siraj, na rasa yadda zan yi na fito kai tsaye na nunawa Jibril irin kudirin da Siraj yake da shi akansa, ina son nayi masa yadda zai fahimta ne kuma ya kamashi dumudumu amman na rasa yadda zan fahimtar da shi. Sai Bilal da ya kasa fahimta ya kasai daina zargina duk kuwa da kasancesar an saka ranar aurenmu a yanzu, zuciyarsa ba raya masa kamar ina son Jibril ne, ga kuma ta bangaren Familynsa har yanzu mahaifiyarsa fushi take dashi ta kasa sakewa da ni saboda bata son auren, gashi tana ganin kamar saboda ni aka kore shi aiki daman mahaifinsa ne ya tsaya kai da fata akan maganar har aka saka ranar auren. Ko ranar da aka kawo tufafin sakawata sai sa yan'uwansa mata suka yi ta Maganganun kamar na habaici, ni dai ko kadan hakan be dame ni domin iya abunda na sani Bilal yana so na ni ma kuma ina son shi so kiyayyar yan'uwansa ba zata dame ni ba, domin ina jin a jikina zan iya canja musu rayuwa su soni ta hanyar kyautata musu da kuma yi musu biyayya. Ban tsammaci Bilal zai zuba min lefe kamar haka ba, domin kala talatin da biyu ya yi min kamar wata budurwa babu abunda be saka ba a cikin lefen, da na masa magana sai ya ce wai daman ya dade da siye ya aje ba a yanzu ya siya ba, baya aikin komai a yanzu sai tsaron wani shagon computers suna biyanshi kullum, amman ya yi applying a cbn da kuma aikin kaki har guda biyu, sai dai aikin naija sai a hankali za ka yi applying dauka sai na manta ma, baya son komawa kamfanin Jibril aiki kamar yadda nima bana so saboda kar Jibril ya dauka cewar Bilal da kamfaninsa kawai ya dogara. Ban taba sanin cewar Bilal yana da zafin kishi ba sai a yanzu, domin ko kallona ya yi sunan Jibril yake kira wai ai daman yasan ina son shi ni kuma wani lokacin har dariya yake bani domin idan ya bata rai abun baya masa kyau. Yau ta kama Friday ina dawowa aiki na zauna na shiryawa Bilal Snack saboda yana ciki favorite dinsa musamman ma idan ni nasa yana ci sosai, sai da magariba na gama sai na yi wanka na shirya cikin wata jar kamfala, ta karbeni sosai saboda jan abu yana fitar da farin mutum, sai na bi jikina na fashe da turare sai na dauki blue mayafi na saka, na dauki wayata na kirashi bugu biyu ya daga. “Hubby ina nemanka yanzu” “Me za ki ban?” “Sai zan baka wani abu kawai na ke da ikon ganinka?” Na fada kamar zan fasa masa kuka. “Gani nan zuwa” Yana fada ya kashe wayar, haka yake mina yanzu zuwa fira ma sai yaga dama saboda kawai yana fushi da ni wai ala dole ni soyayya na ke da Jibril, ko kadan bana ganin laifinsa domin na san ko a littafi ba za a samu namijin da zai yarda ya kyale matar da zai aura tayi aiki karkashin wani ba a Wai dan kawai da taimaki rayuwar danta. Ta bangaren yan uwansa ma nasan ba a rasa masu masa magana domin abokansa da yake zuwa da su wani lokacin sukan zolayeni da Maganganun marar dadi ko kuma na bugun ciki domin kawai su ji abunda zan ce, amman ya toshe kunnuwansa domin kawai ya bani damar cin ma kudirina har shi yake kokarin kare ni wani lokacin. Bayan kamar mintuna talatin sai gashi ya aiko min sako wai na fito yana kofar gida, ni kuma na yi murmushi na dauki snack din na kira Noor ya rika min lemun kwakwa hadin gida da na yi masa muka fito tare fito Noor na aje jug din yaje da gudu suka rumgume juna. “Uncle Bilal i miss you” “I miss you too Noor” “Wannan Saturday data wuce ka ce zaka zo kaje da ni yawo kuma baka zo ba” “Mantawa na yi but dis weekend zamu je” “Gobe ko? Gobe weekend fa” Bilal ya dafe kansa. “Oh na manta tau gobe za muje” “Thank you” Ya fada har da tsalle, sai kuma ya tsaya yana kallon bakina da shi yadda muke gaisawa, ganin hakan yasa na umarce shi da ya wuce cikin gida. “Ga snack din da na maka” Sai ya kawarda kai baya ma son kallon snack din. “Bana jin cin komai a yau” Hakan yasa ni jin babu dadi amman sai na daure na dauki daya na mika masa a hannu. “Dan Allah ka ci da kaina na hada maka” “No na koshi yanzu na gama cin indomie” “To ga lemun kwakwa nan da kaina shi ma na hada” “Ai ko baki fahimtar hausa ne?” “Na fahimta dan Allah Bilal ka daina fushi da ni, na san ka yi hakuri ni kaina ba dan raina yana so nake aikin nan ba, kuma na yanke shawarar aje aikin a wannan week” Ya kalleni “Saboda mai?” “Saboda ya kamata na aje, na yi iya kokarin da zan yi na taimakon Jibril, sai dai na bishi da addu'a kawai, kuma kaga aurenmu sauran wata uku a wannan lokacin ne ya kamata na aje aikin ai” Murmushi ya yi ya soma wasa da yatsun hannunsa. “Har yanzu kina son Jibril ko Nawwara?” Kallonshi na yi jin tambayar banbaragwai da kuma yanayin yadda ya kira sunana kai tsaye ba kamar yadda ya saba kira ba. “Wannan kuma wace irin tambaya ce Bilal?” “Tambaya ce dai kamar ko wace tambaya amsarki kawai na ke so” “Idan har baka so ba aikin nan Bilal ba zan yi ba” “Na isa na hanaki? Ban riga na aureki ba Nawwara balle na gindaya miki wasu sharadodi, so ban isa na hanani aiki tare da Jibril ba, idan ma na yi kokarin hanaki sai Inna da ke sun ga laifina” “Babu wanda zai ga kaifinka saboda kana da cikakken iko a kaina, be kamata ka zargeni ba Bilal” “Mi zan yi bayan zarginki Nawwara? Jibril first love dinki kuma karya kike yanzu ki ce min babu son shi a cikin zuciyarki, na san yana son ki sosai kuma zai yi komai dan ya ga ya same ki, ya fini kudi na sani kuma ya kyautata musu da abunda ni ba zan iya ba” Idanuwa sun cika da kwalla kalamansa sun ratsa zuciyata cikin rashin jindadi na hadeye yawun da ke bakina na ce “Jibril ya fika kudi amman be fika karbuwa a zuciyata ba, Jibril ya wukanta ne Bilal irin wulakancin da wani da namiji be taba ma mace ba, kuma a yanzu kake zargin zan iya aurensa? Bayan an saka mana rana da kai mika dauki iyayena ne zasu canja magana ta da kai saboda kawai Jibril ya fika kudi?” “Idan har baki son shi dan me za ki taimaki rayuwarsa? Har ku kuma kuna zama kamar wasu masoya, dan Allah Nawwara baki ji kunyar kanki ba?” “Da ka nuna min baka so tun farko da ban yi ba, dukan abunda na ke ma Jibril ko kuma na

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});