Chapter 22
Chapter 22
sha wahala a nan idan har na aikata aiki na ƙwarai ina zuwa ƙiyama kai tsaye aljannah zan wuce, kuma kin ga can ba a mutuwa ba a baƙinciki balle tsufa. Ki rumgume ƙaddarar nan Inna, karki yi Habiba abunda zai ƙara mata baƙinciki, ta ce min zata gudu ta bar gidan nan saboda kar ta zama silar ajalinki” Da sauri Inna ta miƙe tsaye da sauri hankalinta a tashe. “Ina take?” “Tana ɗakinmu” Da gudu ta nufi ɗakin, ni kuma na rufa mata baya. Ko da muka shiga ɗakin sai muka samu babu kowa a cikinsa, daga ni har Inna sai da gabanmu ya faɗi, Inna ta juyo ta kalleni nima na kalleta. “Habiba” Na kira sunanta da ƙarfi, sai ta amsa min daga bayan gambu da take ɓoye, a zatonta Inna zata faɗa mata wata maganar marar daɗi ne ko kuma ta daketa hakan yasa ta ɓuya a nan. Da sauri Inna ta duba gurin domin ta fini kusa da shi sai ga Habiba a tsaye tana hawaye jikinta na rawa tana jiran sakamakon Inna. “Zo nan ƴata na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yi miki albarka, ya isar miki” Inna ta faɗa tana miƙa hannu taja Habiba jikinta ta rumgume, sai suka fashe da kuka, sai nima na fara nawa kukan da daga inda na ke tsaye, a raina kuma ina ta godiyar Allah. *** *** *** Haka muka wuni a cikin gidan kamar waɗanda akayi wa mutuwa, Sakina da Jamila ma sun lura da haka su kansu basa wani sakewa saboda ganin kamar muna cikin damuwa, Noor ne kawai yake ta sha'aninsa shi kan be ma damuba. Washe gari kasa zuwa aiki na yi saboda na tashi jikina da kuma zuciyata babu daɗi, duk yadda Inna ta so naje sai na ƙi, su Sakina kawai suka je makaranta, mu kuma muna gida shiru-shiru babu wani motsin kirki da ɗayanmu ke yi, misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bilal ya kirani ina ɗauka sai ya fara tambaya miyasa ban je aiki ba, ni kuma na amsa masa da cewar babu komai, sai dai ban yarda ba yana ganin kamar ɗan ya ganni babu hijabi jiya ne yasa na yi fushi. Jikin Habiba ya ƙara tsanani da yamma, har na ke bada shawarar mu kaita asibiti sai Inna ta ƙi saboda aganin asiri mu zai tonu. “Idan mukaje asibiti zasu faɗa mana ciki ne, wanda nasan nan da nan za a ji a unguwar nan, ya kike so acewa Yakumbo da kuma mutane babban gida? Da wane ido zamu kallesu, yanzu zasu ce dan margayi ba shi da rai ne na ƙyale Habiba ta aikata wannan abun ni zasu ɗorawa laifi” “Da ido da muke kallonsu Inna, tun bayan da aka gama amsar gaisuwa kin saki ganin ƙafar wani a gidan nan? Ba mu da nisa da su amman basu taɓa ɗauko ƙafa suce bari su leƙo mu suga ya muke ba, kowa harkar gabansa yake” Ta yi shiru kamar ba komai kamar mai tunani can kuma ta kalleni “Ni da wai na ce ko zubar da cikin zamu yi?” Gabana ya faɗi, naji maganar kamar saukar aradu. “A'a Inna idan muka je zubar da cikin ai dole za'aji” “Ba asibiti ba wai gida” “Taya zamu zubar da ciki gida?” “Ƴan kayan ɗacin nan da ake badawa mana, tun da kin ga yanzu be yi ƙwari ba kuma a iya busa masa rai ba, idan har be zube ba sai mu ƙyaleta” Na kasa cewa komai saboda na lura ranta ya kwaɗaitu da a zubar da cikin, duk da ina ganin zubar da cikin yana daga cikin alamomin rashin yarda da ƙaddara. Tausayin Habiba ne ya kamani sai na ji ina ma nice ba ita ba, hawaye suka zubo min sai na yi saurin tashi tsaye ina faɗin. “Bari naje na siyo mata maganin zazzaɓi” Inna ta amsa min da tau cikin yanayin damuwa, ɗaki na nufa na ɗauko Hijabina ina kallon Habiba take kwance malala kamar lakka. Kamar na fasa kuka haka na fito ɗaga ɗakinmu bayan na ɗauko ƴan canjina na fita zuwa siyo mata magani, har na isa tunanin maganar Inna nake, ta yadda zan yi na hanata kawai na ke nema. Bayan mum gaisa da mai shagon maganin sai na miƙa masa ɗari biyu na ce ya haɗa min maganin zazzafi kala-kala. Ya haɗa min kusa kala takwas cikin har da na malaria da na ciwon kai da na zafin jiki, ya ɗora min a saman gilashin da suke ɗora magani ni kuma na karbi leda na saka ina jiran canji. Sai kawai na ga Mustapha cikin shagon kamar an jefoshi, matsawa yayi kusa da ni sosai yana min magana ta yadda babu wanda zai ji “Ki yi haƙuri da abunda ya faru ranar nan, Wallahi ba da ke nake ba da mai Napep ɗin daya ɗauko ki na ke” Ji na yi kamar ace akwai wuƙa kusa da ni na daɓa masa a ƙirji, wani ɗogon tsaki naja wanda ya jawo hankalin duk wanda ke shagon zuwa garemu, na ɗauki canjina na fice zuciyata na bugawa kamar zata fito saboda ɓacin rai. NOT EDITED ⚠️ SHARE, COMMENT, VOTE. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣6⃣ Haƙiƙa akwai ƙurciya a rayuwar Habiba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta aikata abunda ta aikata, wanda take tunanin kamar mafitane, sai gashi ya zame mana matsala, yanzu kuma tana ganin kamar guduwa ta bar gida shi ma mafita ne, ni ko nasan duk yarinyar da ta gudu ta bar iyayenta lallai tana tare da na sani da kaico a rayuwarta. Ba zan bari ƴar'uwata ta aiwatar da wannan ƙudirin nata ba, ko da kuwa haka yana nufi salwantar rayuwar mahaifiyata ne, ba zan bari ta sake aikata wani kuskuren ba. Ƙoƙari nake na tsayarda kuka ta yadda zan ƙarfafa mata guiwa da rarrashi amman hawayen da ke min zuba sun ƙi bani haɗin kai. Idan har ban yi ƙarfin halin shiga tsakaninta da wannan kuɗirin nata ba, lallai zamu iya rasata wanda na san hakan zai iya sama sadiyar rasa Inna. Hannayenta na saki na share hawayena ina kallonta, cike da ƙarfin hali na ce “Babu inda zaki je Habiba, irin wannan tunanin na ki ne yaja miki kika jefa mu cikin wannan halin, yanzu kuma zaki sake aikata irinsa? Kina tunanin aikata wannan abun shine mafita? Ba zai canja komai ba, sai dai ma ya ƙara ɓata ran Inna har ta kasa yafe miki, mu kuma ki ja mana ɓacin suna, haka kike so?” Ta girgiza kai alamar a'a, muryarta a shake ta ce. “Ta ce ta yi nadamar haihuwata ni ce ajalinta, ba zata yafe min ba” Hannu na kai na sake riƙe hannayenta. “Zata yafe miki Habiba, ni ma uwace na san halin da Inna take ciki, akwai zafi idan wani abu ya samu ɗanka musamman mace, idan wani abu ya sami Noor bana iya yafewa kaina, bana iya controlling kaina bana iya juriya, kin san saboda me? Saboda Ina ƙaunar Noor, a duk faɗin duniya babu wacce zata gwadawa ɗa so kamar uwarsa, duk abunda Inna ta yi miki saboda tana ƙaunarki ne ke kanki kin san Inna tana son ki, karki yarda ki gudu idan har kika gudu babu ni babu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119