Chapter 46
Chapter 46
matsalar sa ɗaya baya son zaman da yake a waje kuma baya son yarinyar da yake tare da ita” Sosai na ji babu daɗi duk da bani da wanda zan iya fitar a lokacin na ce gashi shi nake so, amman hakan yasa ni jin babu daɗi, sai dai ban yarda na nuna masa ba domin na san ba zai min abunda zai cutar da ni ba. “Ai kin san Alhaji Bashir ko? Ɗan sa da yake waje yana aiki, ta hanyarsa ma Daddy mu ya samo muku gurbin karatun, ba zaki rasa sanin Jibril ba dan ance makarantar ku yake koyarwa, kuma a can zamu zauna sai kin gama karatun sannan ku dawo gida gaba ɗaya” Wannan karon Momy ce take maganar da ta kwantar min da hankali kuma ta saka ni farinciki, cikin nuna tsantsar ladabi na ɗago na kalli Daddy na ce “Ba zaka taɓa yi min abunda zai cutar da ni ba, ni kuma ba zan taɓa butulce maka ba, ko wuta ka kunna kace naje na shiga zan iya shiga na ƙone kaina balle aure, fatana Allaj yasa haka shine alheri” Ya ji daɗin farucina har ma yasa min albarka shi da Momy sannan na taso zuciyata cike da farinciki fal na dawo sashenmu, jikin har rawa yake na labartawa Salima abunda ake ciki, ita ma tayi farinciki sosai sai da nayi mata alƙawari karta faɗawa kowa kuma karta nunawa Daddy ina sonsa, ita kuma ta yi min alƙwarin haka. Bayan kwana ɗaya muka yi shirin zuwa sokoto ni da Salima wannan karon ma jirgi muka bi, Inna ta yi farinciki ganin sosai ni kaina ban san na canja ba sai a wannan lokacin na yi mamaki da Inna ta ƙara haihuwa ba tare da ƙara wasu shekaru biyar ba, kuma ace har anyi sunan Jamila ba a faɗa min ba. Dare muke rayawa ni da Salima muna labarta Inna da Baba rayuwar waje, Habiba kan ta shige cikina tare muke kwana a shinfiɗa ɗaya, a wannan lokacin ne na samu damar ziyarar abokaina da muka taso tare ciki wasu kuma da muka yi makarantar islamiya da boko a tare kamin tafiyata Abuja, cikin har da Zinatu da Baraka da kuma Jidda a lokacin duka muna unguwa ɗaya kamin su Zinatu su koma kware road gawon nama. Wasu basa yarda ina karatu a waje saboda suna ganin mahaifina ba kowa bane, kuma ba kowa ne mai arziki ba ne zai iya yi mana yadda Daddy ya yi mana. Inna ta labarta min yadda ake ta tsigumi a unguwarmu wai saboda kwaɗayin abun duniya zai siyar da mutuncin ƴarsa ya yarda naje na yi karatu bayan na secondry da aka ce na yi, a cewarsu wai yaƙi ya yi min aure jira yaƙe sai na gama karatun sai mai kuɗi ya zo ya aureni. Ni kaina maganar bata min daɗi ba kuma daman nasan za a samu haka, mutane ba zasu taimakeka idan kuma wani ya tallafawa rayuwarka sai koma gefe suna zagi da ganin hakan be dace ba. Sai da muka yi sati biyu a sokoto ana sauran kwana uku mu koma Abuja, Baba ya shigo ya same ni a ɗaki a lokacin ina ni kaɗai ya soma labarta min maganar da Daddy ya yi masa, ganin na ƙi cewa komai yasa ya kira Inna suka sakani a gaba akan ina son haka ko bana so domin shi ba zai yarda ayi min auren dole ba. Ni kuma na yi shiru ban amsa ba, hakan ne ya tabbatar masa da ina so ɗin kamar yadda Annabi ya faɗa shirun budurwa shine amsarta. “Amman yasan ke ba ƴar Alhaji ba ce ko? Saboda bana son ayi abu daga baya ya dawo na rashin daɗi” “Wallahi Baba ban sani ba, amman na san ba zai rasa faɗa masa ba” “Idan ma be faɗa masa ba ni zan buƙaci.ya faɗa masa, ƙara yasan ko wacece gudun kar sai anyi abu wani abu ya biyo daga baya, kuma ina son yasan mu talakawa ne iyayenki ba masu kuɗi ba, idan ya ji zai iya aurenki a haka walillahil hamdu idan kuma ya ce ƴar mai kuɗi yaƙe so sai mu jira Allah ya kawo miki na gari” “Hakan shi yafi Allah ya zaɓa miki alheri” Cewar Inna, ni dai ban ce komai ba, Allah kawai na ke roƙo ya zaɓa min abunda ya fi alheri. Bayan mun koma Abuja Momy take faɗa min wai cikin satin nan Jibril ɗin zai dawo dan haka na shirya tarbonsa a kowane lokaci, a lokacin hutunmu sauran sati uku ya ƙare. Shiru-shiru Jibril be zo ba, da sunan ganin matar da zai aura, hakan ya tabbatar min da cewar shi ma baya son auren wata ƙila shi ma an masa yadda aka min ne, wato haɗi. A week later Momi ta ce na shirya ni da Salima zamu je area 1 gurin abokin Daddy mu ƙarɓo saƙo, duk kalar tufafin da na saka sai Momy tace ba su yi ba naje na canja, kuma ni kawai take cewa ba da Salima ba, daga ƙarshe sai ta shigo ɗakinmu da kanta ta zaɓa min tufafin da zan saka kuma tasa na canja kwaliyar fuskata na feshe jikina da turare sannan ta kira direba ta ce ya kaimu. Na samu kaina da faɗuwar gaba sanin gidansu Jibril ne zamu je, sai dai ko da wasa ban kawowa raina cewar zan je mu gaisa ba ne, iya abunda na zata zamuje karɓo saƙo ne wata ƙila yana nan shiyasa take son na yi kwalliya ta yadda ko da ya ganni ba zai raina ni ba, amman abun mamaki bayan mun isa gidan mun gaisa da Hajiya Zainab Step mother ɗinsa sai aka nuna min wani falo wai na shiga zamu gaisa da Jibril. Na ji babu daɗi duk da kasancewar ina sonshi amman sai nake ganin kamar hakan be dace ba, shi da yake namiji ya kasa zuwa ya ganni sai ni da nake mace za a ce naje mu gaisaz, ba zan iya mata musu ba tunda ita a tunaninta Momy ta faɗa min haka tun gida. Da sallama na shiga muryata can ƙasa-ƙasa, amman be amsa min ba kuma be ɗago ya kalleni yana ta aikin dannar wayarsa fuskarsa a haɗe kamar baƙin hadari, his perfume make me feel comfortable har na zauna duk da be min izinin zaman ba. From head to toe ya kalleni sannan ya jinginar da kansa yana taɓe baki ya ce “Ke kuma haka tarbiyar gidanku take? Mata su suke zuwa fira da kansu? What kind of woman are you, kin cika arha da yawa gaskiya abun har cikin gida” “Ni ma ba a faɗa min da kai zan gana ba, saƙo aka ce min zan karɓa shiyasa yazo da ko mayafina baka isa ka gani a gidan nan ba” Ba bashi amsa kai tsaye, sai ya tashi zaune yana taɓe baki tare da cigaba da kallona. “Really? Kuma kika ci kwalliya haka? Kina tunanin zan ga kyauki ne ko? Mutumen da yake son ki zai yaba kyauki, amman ba ni ba dan ni kamar baƙin maciji nake ganin ki, ki taimaki rayuwata baiwar Allah ki ce baki so na, Wallahi zan biyaki ko nawa kike so” “Kai miyasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119