Chapter 48
Chapter 48
zai fara sonki har ya kyautata miki, ke ko be so ki dole zai kyautata miki domin su masu kuɗi matuƙar suna auren mace dole ne su kyautata mata domin dukiya bata musu zafi. Nawwara karki yarda ki faɗa ko ki nunawa Alhaji cewar baki son zaɓin da ya yi miki domin hakan zai iyasa zuciyarsa ta buga ya mutu gaba ɗaya, dan Allah ki yi min alƙawari zaki auri Jibril albashi idan daga baya kika ga zaki fito sai ki ce ya sakeki, kuma kin ga waje ma zaku zauna kina karatunki shi yana sha'aninsa” Ta ƙarasa tana riƙe hannuna cike da magiya. Kai kawai na iya ɗaga mata alamar na amince ba dan raina ya so ba, har ga Allah ni kaɗaina ina ganin kamar idan ban auri zaɓin Daddy ba ban masa halacci ba. Bayan fitarta Salima ta shigo tana zolayana, yadda ta ga ina kuka ya tsorata ta har ta soma tambayar ko wani abun ne ni kuma na amsa mata da ba komai. A haka na jure na kauda kaina daga duk wani abu da zai nuna bana son auren saboda kar ran Daddy ya ɓace, su kuma sai hidimar ɗaurin auren suke har ana daf da ɗaura aure Baba be daina min magana akan idan bana sonsa na faɗa ba, amman na ƙi na faɗa, ni dai kawai na ɗaukarwa kaina alƙawarin zan jure ko ma minene saboda na zama ƴar halak a gurin Daddy da Momy. Ana cikin haka ne Ya Jamil ya samu transfer gurin aiki zuwa Jos, ni kaina na jidaɗin haka nasan idan ya yi nisa da ni zan fi samun sakewa. Sai da ana sauran kwana biyu ɗauren auren Jibril be taɓa kirana ko a waya ba, kuma be je ya gaishe da Baba ba, sai dai Mahaifinsa ya tafi tare da muƙƙarabbansa suka gaishe da Baba, komai a ɗaurin auren a nan Abuja aka yi saboda haka sai ranar da aka ɗaura min aure sannan mahaifina ya ga fuskar mijin ƴarsa kasancewar ya samu halarta tare da wasu ƴan'uwansa. Na ji ni daban a cikin wani yanayi marar misaltuwa a wannan ranar, bana farinciki kuma bana baƙinciki ni dai kuka kawai na ke kukan da ban san dalilinsa ba, ganin haka yasa Momy ta kaini ɗaki ta ja min kunne akan na daina kukan kar mutane su zargi wani abu, haka na wanke fuskata na keɓe kaina a ɗaki har sai da ka ce na fito ga Baba can zamu gaisa. Babu wata gaisuwa da na yi da dashi sai ta kuka kuka na yi sosai har sai da shi ma na saka shi kuka, ya yi min nasiha sosai akan rayuwa da kuma zamantakewar aure, ya faɗa min yanzu na tashi daga ikonsa na koma ikon wani, hakan yasa na ji ni cikin wani babban ɗaki mai nauyi. Washe gari ma da zai koma sai da ya kirani shi da ƴan uwansa suka zagaye ni suna min huɗuba mai ratsa jiki. Kwana biyu da ɗaura min aure aka kwantar da ni a babbar asibitin Abuja saboda rashin lafiyar da ya taso min, a wannan ranar ce Jibril ya hau jirgi ya bar ƙasar nan, har na yi jinyar na gama be taɓa kirana ba sai dai mahaifinsa da wasu Sisters na sa sun zo duba ni da kuma step mother ɗinsa, Mahaifinsa ne ya fi nuna min kulawa da damuwa, su kan kamar daman sun zo ne by force. Bayan an sallameni da kwana biyu Salima ta fara shirin zuwa makaranta, ni kuma Daddy ya hana ni da sunan wai ba zan koma ba sai na ƙara jin sauƙi, ni kuma ban musa musu ba na amince, ina ji ina gani Salima ta koma makaranta ni ina nan. Yana lura da yanayi na sosai, har ta kai wata rana ya kirani a ɗakinsa ya tambayeni ko dai bana son auren ne, sai an kasa amsa masa, ya yi min nasiha akan haƙuri da halin Jibril wai daman yasan za a samu haka saboda baya son auren kwata-kwata babu zancen aure a gabansa, wannan yarinyar ce kawai yake kulawa ita kuma ba ƴar mutunci ba ce zaman kanta take wannan dalilin ya saka mahaifinsa ya ƙi yarda ya aureta, a ranar yake labarta min cewar Jibril ne ya hana na koma makaranta wai ya ce be bada izinin na koma makaranta ba. Ranar na yi kuka sosai har sai dai na raina kaina, mutumen da ba zai iya kirana ya tambayi tafiyata ba shi ne zai ce bada umarnin kar a barni na koma karanta kuma a ƙyaleshi saboda kawai yana taƙama da kuɗi. A haka na kwashe wata shida a ban koma makaranta ba, idan kuma nunawa Momy ina son anje gida gurinsu Inna sai ta ce min ba haka ba, wai ba zata bari na tafi bada izinin mijina ba. Tun daga ranar da aka ɗaura min aure da Jibril duk wata sai Alhaji Bashir Makama ya aikowa da Momy kuɗi ya ce a bani amman bata taɓa bani ko naira ba, bata ma taɓa faɗa min ko nawa ba ne tana dai faɗan min ya aiko saboda kawai na yi masa godiya. Tun da Jibril yasa ƙafarsa ya bar ƙasar nan be sake waigo Nigeria ba, kuma be taɓa ɗaukar waya ya kirani ba, wani daga familynsa be taɓa zuwa da sunan ganina ko duba lafiyata ba. Da wannan baƙinciki na ke kwana na ke tashi ban taɓa nunawa kowa ba, sai dai hakan be hana Daddy damuwa ba, wata rana bayan na gama haɗa abun karyawa mun sai ya aiko yana kirana, ko da na shiga sai na samu Momy tare da shi, guri na samu na zauna na natsu ina ta sauraren abunda yake faɗa min. “Na gaji da wannan halin na Jibril, ba zai yiyu ya ce ba zaki koma makaranta ba, kuma baki tare ɗakinki ba, tun da ya tafi be ma kira ya tambayi lafiyarki ba, dan haka na faɗawa mahaifinsa idan ba zasu iya tanƙwara ɗan su akan abunda suke so ba, ni ba zan cutar da ƴata ba, na faɗawa mahaifinsa idan har yana ganin rabuwa da ke shine maslaha tam mu muna maraba, kuma ina fatar wannan hukuncin ya yi miki” Kamin na ce wani abu sai Momy ta yi karaf ta ce. “Haba Alhaji yaran zamani ai sai an yi haƙuri, karka yi maganar raba auren su ko shekaran jiya na tambayeta ta faɗa min ita tana son mijinta, kawai ka yi ta musu addu'ah” Kallo ɗaya na yi mata na ɗauke, wata ƙila tana min haka ne saboda ni ba ƴar ta ba ce, Daddy kan tuni ya gama gamsuwa da bayaninta, jiki a sanyaye na taso na fito daga part ɗin Daddy. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣1⃣ A nawa tunani Momy tayi min haka ne tun farko saboda kar na auri ɗanta, yanzu kuma bata son a kashe auren ne saboda dukiyar gidansu Jibril tasan duk wulaƙancin da zai min ni ba ƴarta ba ce saboda haka wannan ba zai taɓa damunta ba, babu wanda zai fi jin zafi jin zafin ɗa kamar uwar da ta haifeshi, ni kaina da Mahaifana ne ce zan iya fahimtar da su kuma su fahimta, amman wannan duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119