Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 85

Chapter 85

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kullum ba ya zo ko da sau hudu ne a sati. Ranar da Noor ya kwana takwas a asibitin na bukaci a sallamemu amman sai ya ki, ni kuma ba dan komai na ke son komawa gida ba sai dan Bilal saboda kwana biyu nan na rasa gane kansa ya kasa fahimtata yawan zuwa da nake asibiti jinyar Noor yana ganin kamar wata sabuwar soyayyace ke kulluwa tsakanin da Jibril. A ranar da muka fara zuwa kotu zama na farko na sha kuka a ranar saboda ya tuna min da mahaifina da kuma Habiba, na yabawa Dpo sosai domin ya nuna kulawa akan case din ga kuma police din da alkali ya bada ikon tsarewa har zama na gaba, wani abun da ya bani mamakin matar da ta ce Mahaifinmu ya yi mata sata tana da yanayi da Siraj sosai kuma ita ba ce a tsareta ba saboda tana da kudi ko kuma tana da daurin gindi ko kuma dan tana da kokarin kare kanta cewar ba ita ta saka su ba oho. Ni dai har muka fito daga cikin kotun ban daina harararta ba ita kuma bata daina kallona ba. Tare muka fito da Inna da Sakina, sai Jidda da Bilal da kuma yan uwan Baba da na Inna, kowa da abunda yake fada ni dai ban ce komai ba, har muka shiga Napep muka dawo gida. Muna shigowa gida Jidda take labarta min cewar Mustapha ba shi da lafiya jiya aka kai shi asibitinsu Jibril. “Miya ke damunsa?” “Ke kika damunsa Nawwara” “Kamar ya? Ai na ce na yafe masa” Ta yi shiru bata sake cewa komai ba. “Kinje kin duba shi?” “Ina tsoron mahaifansa” “Mai tsoro baya zama gwanin Jidda matukar kika saka tsoro a zuciyarki Mustapha ba zai taba fahimtar cewar kina son shi ba” Ta kalleni da sauri. “Waya ce ina son sa? Mustapha da yake son ki sai kuma ace ni ina son sa?” “Ba fada min aka yi ba, a idanuwanki na karanta” “Baki min adalci ba Nawwara baki san komai a kaina ba” Ya mike tsaye a fusace ta fice, ni kuma na bita da kallon mamaki domin ban ga abun daga hankali a cikin wannan maganar ba. Tashi na yi soma dora girki muna ta firar yadda zaman kotun ya wakana ni da Inna, da dare sai ga Bilal ya kirani a waya wai na fito yana kofar gida. Na yi mamakin jin hakan saboda kwana biyu ya dauke min kafa daga zuwa fira ko da kuwa ni na bukaci hakan sai dai mu gaisa a waya, na dauri aniyar sakashi farinciki a yau ko da kuwa ba da niyar hakan ya taho ba, dan haka na dauki kayan kwaliyata na dandasa kwaliya mai kyau na feshe jikina da turaren da Jibril ya aiko min cikin kayan da ya siyo min kwanaki, na dauki gown din atamfa da take cikin kayan da Jibril ya aiko min na saka, ni kaina na san na yi kyau a wannan dare, Inna ma kallona kawai ta yi tayi murmushi, nima na fice ina murmushi. A yanayin yadda na tararda shi yasa ni jin babu dadi, domin kuwa fuskarsa babu annuri jikinsa kamar a sanyaye, bayan na masa sallama sai ya amsa min idonsa akaina kamar zai cinyeni. “Nawancy kin yi kyau” “Dan kai kadai na yi ta na gode da ka yaba” Sai dan yi murmushi. “Aiko ya kamata na bada tukuici ko?” “Ka adana tukuicinka da daddadan kalamanka har sai na fada maka dalilin wannan kwaliyar tawa” “Akwai wani daliline bayan wanda na gani?” “Sosai ma, a wancan gani ka yi, wannan kuma ji zaka yi” Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi. “Nawancy kina yaudarar zuciyata da yawa, da fushi na zo nan gurin, amman kin shiga kin yi nikaya kin tarwatsa duk wani damuwa da fada da na zo da su” “Ai daman haka ya kamata ko wace amarya ta kasance gurin angonta, mai wanke danuwarsa ta shimfida farinciki a zuciyarsa” “Ina ma da gaske Nawancy amaryar Bilal ce da yafi kowa farinciki a duniyar nan” “Akwai wanda ya isa ya hana abunda Allah ya zo kasanewarsa tun farkon hallitar Nawwara?” “Babu” “Ashe ko Nawwara sai ta fi Bilal kasancewa a cikin farinciki daga ranar da aka daura aurenta da angon da ya fi ko wane ango tsada a duniyar nan” Ya yi murmushi yana kallona tare da lumshe ido. “Ina son ki sosai Nawancy” “Kai so na kawai ka ke ni ko kaunar ka na ke” Ya sauke ajiyar zuciya. “Kamin ki kaini duniyar da ba zan iya dawowa ba, fadan min dalilinki na yi wannan kwaliyar” “Kamin na maka albishir mai tsada ya kamata ace ka fada min abunda ya kawo ka nan” “Yo tun yaushe kika duniyar kwakwalwa kika mantar da ni wanene ni ma, balle abunda ya kawo ni nan kuma” “Yanzu dai rumtse idonka sai na fada maka albishir din” “Ai kunnene yake ji ba idanuwa ba” “Ina gudun kyawawan idanuwan nan naka su ba ni kunya ne” Sai ya yi dariya ya lumshe idanuwasa. “Inna ta ce na fada maka, idan ka shirya ka turo magabatanka suje can Baban gida su gana da nawa magabatan” Da sauri ya bude idanuwansa ya kallini “Da gaske Nawancy?” “Na saba maka irin wannan wasan ne?” Wani ihu ya yi ya daka tsalle ya dire, ni kuma na yo cikin gida da gudu ina dariya. Da na shigo sai na ce da Inna Bilal ya ce zai turo magabatansa amman be saka rana ba. “Mashallah Allah ina fatar kina sonshi dan karki yi wa kanki zabi irin na baya, kuma ina son ki bawa Allah zabi a cikin lamurranki nima zan taya ki da addua idan aurenki da Bilal alheri Allah yasa ayi, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya kawo maslaha” “Amin Inna, inshallah Alheri ne” Daga wannan sai fira ta biyo baya Inna na ta nanata min burinta na ganin na yi aure domin shine kwanciyar hankalinta, a daren Bilal ya yi min kira ya fi a kirga ni kuma na ki dagawa, misalin uku da rabi na dare na tashi na yi nafila na Mikawa Allah zabina akan ya zaba min dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata. Washe gari bayan na gama komai na shirya na nufi asibiti zuciyata cike da tunanin yanayin Jidda gabana kuma nata faduwar da ban san daliliba. Jirbil kawai na tarar a dakin Noor baya nan, na gaisheshi cikin ladabi kamar yadda na saba masa a yanzu. Be amsa min ba sai ya matso kusa da ni yana ta kallona kamin ya risina kasa wanda hakan yasa ni ja da baya. “Nawwara dan Allah ki yafe min abunda na yi miki na san na yi kuskure amman ki dubi girman Allah ki yafe min” “A kwanakin nan da muka dauka be isa yasa ka fahimci cewar na yafe maka ba?” Ya mike tsaye yana kallona. “Ki kalli cikin kwayar idanuwana ki ce kin yafe min” Ya fadi hakan ne saboda ya tabbatar da yafiyar tawa, domin yasan babu abunda zan gani a cikin idanuwansa sai tsanarsa da kiyayyarsa, ras na sauke idanuwa cikina nasa zuciya a natse bakina ya furta cewar. “Na yafe maka Jibril Allah ma ya shaida

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});