Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hankalinki ba zan cuceki ba, ba kuma za a haɗa baki da ni a cuceki ba” “Idan har ni be cuceni ke zai cuce ki” “Mustaphan da kika sani a baya ba shi ne a yanzu ba, Wallahi ya canja Nawwara kuma saboda ke ina ganin wannan kaɗai abun farincikine ace ta dalilinka wani ya shiryu” Na gyara zamana ina kallonta da kyau. “Bakin san waye Mustapha ba shiyasa kika wannan maganar, baki san iya ta'asar da ya yi ba shiyasa kike ganin kamar ya canja” “Ya canja Nawwara ko ki yarda ko karki yarda Mustapha ya canja, ganin da kika mana tare yazo gurina ne saboda yana neman yafiyarki, yana son na taimaka masa na nema masa yafiyarki” “Kin san abunda ya aikata min kuwa?” “Shine mutumen da ya yi fyaɗe ya bata dubu ashirin ko? Ko ba wannan ba ne?” Kallon mamaki na yi mata. “Ya faɗa miki kenan?” “Ya faɗa min komai saboda kawai yana neman yafiyarki, ki dubi girman Allah Nawwara ki yafe masa ko ya samu sassaucin rayuwa” “Taya kika san tuban gaskiya ya yi? Maza suna yaudararmu Jidda saboda sun san mu mata muna raunin zuciya, sukan yi amfani da wannan damar su sake cutar da mu” “Ba zai taɓa cutar da kr ba Nawwara, tun daga lokacin da kika taɓa marinsa ya ƙyaleki zuciyata ta raya min Mustapha son kin yake ko kuma son wani na ki, ya isa shaidar kirki cewar Mustapha tuban kirki ya yi tun da ya biyo ki har ƙofar gidanku ya nemi yafiyarki, idan har yana son cutar da ke ba zai taɓa neman yafiyarki ba, zai iya sakawa a ɗauko masa ke ya yi miki yadda ya ke so, zan iya dafa miki ƙur'ane cewar Mustapha tuban ƙwarai ya yi kuma ya yi nadama” “Ba zan yafe masa ba da gangan mutun zai aikata abu sai kuma ya dawo neman yafiya, da ace be mata fyaɗe ba da bata samu ciki ba da duk be kaita ga halaka ba, da yanzu ƴar'uwata tana nan raye” Na faɗa zuciyata na mugun ƙuna. Sai dai abunda ya fito daga bakin Jidda ya kusa ya ruɗar da ni ko kuma ma na ce haukatarda ni gaba ɗaya. “Ashe jahila ce ke Nawwara, karatun addininki be amfaneki da komai ba, baki da imani ko kaɗan saboda baki yarda da ƙaddara ba, kuma bari na gyara miki kalamanki da ace yar'uwarki bata je ta kai kanta gunsa ba da be samu damar yi mata fyaɗen ba, kuma ko da Mustapha ko babu Mustapha dole Habiba zata mutu kuma dole sai wani ya yi mata fyaɗe kuma dole sai ta yi ciki saboda yana rubuce cikin kundin ƙaddararta, tirr da halinki Nawwara tirr zuciyar da bata yarda da ƙaddara marar kyau ba sai mai kyau, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle ke da Allah zai cewa faɗi ki mutun kuma ki faɗin ki mutu dan dolenki, zuciyarki bata da kyau Nawwara saboda babu imani babu tausayi a cikinta, bawan Allah nan ko shi da hannunsa ya kashe Habiba ya kamata ki yafe masa tun da har yace miki ya tuba, balle fyaɗen da idan aka bincika daga shi har ita suna da laifi-!” Tun da ya fara maganar na ke kallon yadda take dantsar baki tana faɗa min duk maganar da tazo daga bakinta idonta na hawaye kamar yadda nima nawa idanuwan suke hawaye, cikin muryar kuka na ce. “Faɗa min nawa Mustapha ya biyaki Jidda? Dala dubu nawa ya biyaki da har tasa kika goya masa baya tsaɓanin aminiyarki? Da me ya siye zuciyarki har kika ƙoƙarin ɓata abotarmu?” “Da imani da tausayi ya siye zuciyata, ni na yarda da ƙaddara a yayinda ke baki yarda da ita ba” “Saboda baki dan yadda na ke ji ba Jidda, a gaban idona yar'uwata ra rasa ranta saboda wannan azzalumin” “Na san yadda kike ji, amman na fi jin yadda Mustapha ya ke ji saboda ƙaddara ta faɗa kansa wacce bata wuce faɗawa kowa ba” Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye ta fice ta barni a gurin ina ta hawaye da mamakin kalamanta. Jin ana kiran sallah isha'i yasa na tashi na wanke fuskata na yi alwala a waje na yi sallah isha'i kamar yadda na yi ta magariba. Bayan na gama addu'o'ina na tashi na nufi ɗakin Inna, ko da na shiga na tarar tana sha'u da wutiri Noor da Jamila kuma na saman gado suna mugun wasa, ƙasa na zauna kusa da ita ina jiran ta ƙare idona suna kan ɗana da ke ta sukuwa saman gadon. “Noor bari mana gadon Inna zaka yi sukuwa” Da sauri ya sauko sai ya nufo inda na ke yana faɗin. “Momy zaki ara min wayarki na yi game ko?” Sai a lokacin na tuna da na bar wayar a wajen da na zauna har na yi a zamar tashi na fita na ɗauko wayar cike da fargaba na kunnata ina shigowa ɗaki, zan miƙawa Noor naji ƙarar shigowar saƙo, hakan yasa na tsaya dubawa. _Matiƙar baki dawo aiki gobe ba, wannan shegen saurayin na ki zamu sallameshi kuma try me_ Ba shiri na zaro ido gabana ya shiga faɗuwa na furta shiga uku da kirama kaina hallaka. “Na shiga uku na lalace” Da sauri duk suka kalleni har Inna dake jan carbi. “Miya faru?” Kallonta na yi sai kuma na rasa ta yadda zan mata bayanin ga Noor da Jamila har Sakina duka idonsu a kaina, saurin goge saƙon na yi na miƙa masa wayar. “Ungo je kayi game ɗin” “Momy miya faru?” “Ba komai kuje waje da Mama Jamila sai ku yi” Yana karɓa sai suka yi waje ni kuma na zauna kusa da Inna idona cike da ƙwalla na kama hannunta na riƙe sai na kasa yin magana hawaye suka fara yin aikinsu. “Nawwara mi yake damunki?” Hannuna ɗaya na kai na share hawayena yayinda wasu ke ƙara zubo min. “Inna ko na faɗa miki ba zaki fahimce ni ba, kuma fushi zaki yi da ni” Nan take hankalinta ya tashi ta damƙe hannayena biyu tana kallon cikin idona. “Me kika aikata har haka ne Nawwara? Abunda ƴar'uwarki ta aikata shi kika aikata kema?” “A'a Inna Jibril ne” Na faɗa ina sosa kaina hawaye na sauka a fuskata. “Wane Jibril?” “Baban Noor” Da sauri Sakina ta tashi zaune daga kwancen da take tana kallona, Inna kuma ta saki baki. Ni kuma na rasa ta inda zan fara mata bayani. “Kamfanin da na samu aiki ashe na Jibril ne, ni ma ban sani ba sai daga baya....” Haka na bi na zana mata komai tun daga farko har ƙarshe ban ɓoye mata komai ba, har maganar siye gidan da kuma wannan saƙon da ya aiko min yanzu. Lunshe ido ta yi ta jingina da gado tana sauke ajiyar zuciya. “Miyasa kika ɓoye min wannan tun farko? Da ace kin shawarce ni da duk abun be kai haka ba, har yanzu baki san ƙima da matarba uwa ba ko? Wani na waje ya ji sirrinki mahaifiyarki bata sani ba? Akwai wanda ya cancanci ki yi sirrin da shi fiye da ni?” “Ba haka ba ne Inna, kawai ina tunanin irin halin da zaki shiga ne idan na faɗa miki, wata ƙila ma

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});